Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

The following day suka tashi da Shirin mother’s Eve.

Yau wani hadadden lace Layla ta sanya Red..head dinta da komai na jikinta ma is red..i think I don’t have to tell you guys yanda kayan sukai suiting dinta..just imagine a very fair lady wearing deep Red clothe..kunsan ba karamin haskawa zatayi ba…
Shi Kuma angon nata milk din shadda yasa yau..yayi kyau shima sosae kmr ba tsoho ba????????

5pm sharp suka fara event din…qawayen ummi da yawa sunzo wurin..haka friends din umma ma sunzo all the way from kano..

Event din was very lovely..kowa ka gani zaka ga alaman yana enjoying abun…yau ma kememe Taheer ya hana Layla cashewa..duk yadda taso yin rawar hanata yayi..wai mutane zasu kalleta…sai daga karshe ummi da kanta ta jata sukai rawar tare..wnn Kam ba yanda ya iya dole yaja bakinshi ya tsuke yana binsu da kallo…baa tashi da wuri ba..don sai around 8 na dare suka tashi..

Daga yau kuma biki ya kare..waleema kadai zaayi gobe a nn cikin gidan nasu..zuwa dare kuma ango ya dauki amaryarshi su wuce don ba mutane ne zasu rakata ba.

Saturday…

Tun karfe 3 malama Aisha Ahmad wadda itace zata fadakar a wurin waleeman ta iso gidan…baa fara ba Kuma sai da akai sallhn asr.

Nan compound din gidan aka zuba kujeru..kowa ya zauna Kai..ita Kuma Malama Aysha tana daga dan wani wuri da akai matata danyi sama..yanda kowa dake wurin zai ganta zai kuma ji abun da zata fada.

Amarya Layla na sanye cikin lace fari qal..dinkin riga da skirt daya amshi jikinta sosae…sai aka kawo lafaya shima white mai zanen black flowers a jiki..aka nannadeta cikin lafayan..ko fuskanta baa iya gani…tana zaune inda aka tanadar domin ita da kuma maids dinta.

Bayan an bude taro da addu’a malama Aysha ta ta dauki microphone dake kusa da ita snn ta fara kmr haka…..”Rabbushrah lissadhri…wayasrili amri…wahlil uqlatan min lisani…yafqahu qauli..wa ba’ad Assalamu alaykum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu”…gaba daya mutane wurin suka hada baki wajen fadin”wa’alaikumusalam warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu”…snn malama Aysha taci gaba…”Muna godia ga Allah SWA daya hadamu a wnn wuri mai albarka…wadan nn ma’aurata da Muka taru dominsu muna fatan Ubangiji Allah ka Sanya Albarka a cikin aurensu…ubangiji ka kade dukkanin fitina dake cikin wnn aure…Ya Allah ka basu zaman lfy mai dorewa…ubangiji kasa abokan arxikin juna ne snn Allah ya basu zuri’a dayyiba Allah Kuma yasa zamansu zai dore har gidan aljannah”…nan ma mutane suka sake amsawa da Ameen…

Malama Aysha tace”to da farko dai amarya Maryam…inaso ki Sanya a ranki cewa shi aure bauta ne…snn ibada ne…idan kika Sanya a ranki cewa bauta zakije kiyi…da izinin Allah Zaki yaqi duk wata fitina da zata bullo cikin gidan aurenki…don kinsama ranki dama bauta kikazoyi….

Sannan da akwai wasu shika shikai guda biyar zan fadesu yanxu…Wanda duk wani aure da kika gani a duniya…wadann nan shika shikai da zan zayyano su yanxu…sune suke rikeda wnn auren..alal haqiqa Maryam in har kika dauki wadan nn abubuwa da zan fada Kuma kikayi amfani dasu a gidan aurenki…to tabbas baki ba matsala na zamantakewar aure da izinin Allah…bama ke kadai ba dukkanin yan uwa Mata ku saurareni da kyau…akwai shika shikai ko Kuma ince ginshikai da suke rike ragamar aure matukar mace ta daukesu snn take amfani dasu a gidan mijinta..Da Farko Akwai

1-Hakuri….yes Hakuri nada matukar muhimmanci a zamantakewar ma’aurata…Kuma idan akace hakuri ana nufin hakuri kan abubuwa da dama da zaki iya cin karo dasu a gidan aurenki…hakurin nn ya hada da…hakuri kan source of income na mijinki…maana ya zama dole mace tayi hakuri da yanayin yanda samun mijinta yake…walau me kudi ne walau Kuma akasin haka…duk abinda mijinki ya kawo..ki karba kiyi godia…snn ki nuna masa cewa wnn abun da yayi ba karamin faranta maki yai ba…hakan zaisa ko da yaushe mijinki ya ya ringa kokarin ya faranta miki shima…duk abunda ya samu zai ringa kokarin ya kawo maki don yasan you’ll appreciate….snn hakuri na biyu shine…hakuri kan yanda yanayin halittar mijinki yake… Ma’ana ya zama tilas mace tayi hakuri kan yanda mijinta yake… kyakyawa ne ko akasin haka…Haram ne matar aure ta kalli wata siffa ta mijinta ta kusheta…ko Kuma tace bashida kyau or something like that…da yawa daga cikin matanmu na hausawa sunayin haka…wata Kuma wani zata gani a waje ta yabeshi… which is very bad…sbd haka don Allah Mata mu kiyaye….sai hakuri na uku…shi kuma Yana nufin kiyi hakuri da halayyan mijinki…kunsan ance Dan Adam Tara yake bai cika goma ba…so dole mace zata samu mijinta nada wani hali Wanda ita ba haka takeso ba…to a nan ma sai kinyi hakuri dashi…matukar wnn halin ba sabon Allah bane…yakamata kiyi accepting mijinki a yanda yake…snn ki koyi zama dashi…forinstance wani namijin yanada fada…wani saurin fushi ne dashi…wani Kuma yanada hakuri…to ya zama dole mace ta fara sanin yanda halayyan mijinta yake..snn tayi hakurin zama dashi da wnn halin nashi…don kema bazaki rasa naki fault dinba….idan mijinki nada fada…kar ki kuskura ki daga murya lokacinda yake fadan… instead kiyi shiru sai kin bari ya gama sai ki tausasa murya ki bashi hakuri…ko Kuma kiyi masa bayanin abunda kika aikata yanda zai fahimceki…ta hakan ne kadai zaku samu dorewar zaman lfy a tsakaninku…idan Kuma namiji mai hakuri ne baa ce kije kiyita dirka rashin mutunchi ba…wai don kinsan mai hakurine…to kiyi a hankali don mai hakuri bai iya fushi ba…snn ki gujewa kanki daukan alhakinsa….sai hakuri na gaba shine…hakuri da dangin miji…idan akace dangin miji ya hada da mahaifi…mahaifiya…yayye…qanne…kowa da kowa daya danganci mijinki….ya zama dole suma kiyi hakuri dasu…ki kumayi kokari kowa ki koyi yanda Zaki zauna dashi…ki daukesu tamkar yan uwanki…iyayenshi ki daukesu tamkar naki…ba kyashi…ba rowa…Banda baqin ciki…kar kiga mijinki zaima mamanshi ko qannenshi wani abu ki hanashi…babu ruwanki instead kiyi encouraging dinshi…Banda daure fuska idan sunxo gidanki….ko kiyita bacin rai…snn banda gulma da munafurci…don nasan halinmu Mata akwai mu da gutsuri tsoma…don haka ayi kokari a kiyaye domin Allah.
Abu na biyu shine

2-Gaskia…gaskia nada matukar muhimmanci a zaman aure…kar ki kasance mai yima mijinki karya instead anaso ya kasance tsakaninki da mijinki kalamu Waheed…ya zamana duk mgnr da Zaki fada mai ki tabbatar gaskiyarki kika fada…idan kika saba da fadawa miji gsky wlh ko hadaki dashi akesonyi bai zama lallai yayi tasiri ba don kin riga kinyi winning trust dinshi…ko wani abu akace kinyi bazai yanke hukunci ba tareda yaji ta bakinki ba…duk mgnr da kika fada mai Kuma zai amince sbd ya yadda dake ????Amma idan kika sake mijinki yayi miki shkedan karya…na farko bazakiyi qima a idonshi ba snn bazaki taba fadan mgn ya yadda dakeba koda gsky kika fada…amma idan kika saba fadan gsky kinci riba biyu…na farko kin kauce daga sabon Allah don kowa yasan karya sabon ubangiji ne…na biyu Kuma kinyi winning trust din mijinki wanda ba Wanda ya isa ya canxa hakan..
Abu na uku shine

3-Biyayya…itama tana taka muhimmiyar rawa a rayuwar ma’aurata…anaso mace ta kasance mai biyayya da duk wani umarni na mijinta…idan yace wance yi kaza…ki tabbatar da cewa kinyi wnn abun ko bakiso…haka idan yace wance banason abu kaza a denayi…kiyi iya bakin kokarinki kiga kin daina din koda shima bakyaso…hakan ba karamin kima da daraja zai Kara miki a wurin me gidaba…kuma ba wai kicema miji kin dena abu kaza snn kicigaba dayi a bayan idonshi ba…no..duk abinda kikace mai kin bari ya zama kin baryi knn for good…if not duk rananda ya gane baki bari dinba bayan Kuma kince kin Bari..mutunchinki kaff zai zube a idonshi and kinsan shi mitunci kmr Madara ne idan ya zube kasa bai kwasuwa…so don Allah ayi hattara Mata.
Sai Abu na gaba shine

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button