Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A bangaren ango kuwa tun yamma dama ya gudu daga gidan Yusuf bayan ya sallami some of abokanshi da suka koma…Sam baison wani rakiya da abokai sukema ango wurin amaryarshi..shi Sam hakan baiyi mai ba..haka nn kawai ka kwashi katti suje suyita kallema mata suna mgn da ita…ba dashi zaayi wnn kwadon ba Kam…a masallacin kusa da gidansu yai sallahn magrib snn yaci gaba da zama a ciki har akai Isha..bayan idar da sallahn yayi add’u’o’i sosae kan aurenshi da Layla saida ya idar snn ya nufi gidan don ganin wainar da ake toyawa.

Kai tsaye part dinshi ya wuce bayan ya hadu da some of family members dinsu dake nn compound sunata tsokanarshi…ya bude daki ya shiga snn ya maida kofan ya rufe..ya karasa tareda kwanciya kan three seater dake parlon..sai ya fada duniyar tunani…yana tunanin yanda zamanshi zai kasance da Layla ba tareda wani abu na aure ya shiga tsakaninsu ba..yanaso yai keeping distance dinshi as he promised amma Kuma yana tunanin how…Allah ya gani shi din ba wai ma’asumi bane snn Shiba karfe bane da zai iya rayuwa cikin gida daya da wadda yakema matsanancin So irin haka Kuma ba tareda ya aikata komai a game da ita ba…yana tunanin ta Ya zai iya coping if suna rayuwa da Layla under thesame roof ba tareda yayi messing plan dinshi ba…yasan for sure zai iya kasa jurewa wani lokacin..amma Kuma baiso ya aikata abinda zai zama baiyi fulfilling promise dinshi ba..yanaso ne ya bata kulawanda bata taba tunani ba…yanaso ta tabbatar da ita din yake so bawai wani abu na jikinta ba..but how…a wani bangaren Kuma Yana tunanin rabuwa da ummi…yasan definitely zata shiga damuwa na rashinsu sosae..ta riga tayi sabo dasu na tsawon shekaru..gashi ita ba wasu yaran ke gareta ba..shi kadai Allah ya bata sai Layla…yanxu gashi aure zai nisantasu da juna..wnn shine dalilinda yasa ya dage kan umma ta dawo Abuja gaba daya…yasan idan tana nn ummi zata samu saukin kewansu da zatai…and shima zai riga kokari kullum yazo ya gaishesu as hakan zai rage Mata damuwa sosae..itama Layla sai Yana kawota tana ganinsu time to time…yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda wayarshi tai ringing ba..bai kumaji lokacinda umma ta shigo har ta zauna kusa dashi ba…Saida tasa hannu tadan jijjigashi snn ya mike zaune da sauri Yana rarraba ido…umma na mai kallon mamaki tace”tunanin me kake haka Taheer har nai maka 2 missed calls baka ganiba snn na shigo har na zauna bakayi noticing ba..are you alright”…Saida ya sauke numfashi snn yace”lfy Lou nake umma..kawai Ina tunani ne”…umma tace”ai dama ba bacci kaji nace kanayi ba…so nake inji tunanin me kakeyi haka”…ya saki dan smile snn yace”come on ba wani abu bane fa umma”…Yana rufe baki umma tace”tunanin Yaya kakeyi koh”…a hankali Taheer ya daga Mata Kai alaman eh…ita Kuma ta kamo hanunshi tace”kar ka damu kanka kan wnn.. InshaAllah zanyi iya bakin kokarina inga bata shiga wani hali sbd missing dinku ba..dukda nasan ban isa in hana taji kewan naku ba..but i promise bazan bari damuwa ya rabeta ba..she’s my sister afterall..so Nima tana Sona sosae baku kadai takeso ba”…umma ta karasa mgnr da murmushi a fuskarta..tanaso taga ya saki ranshi shima…saida yai Mata murmushi snn yace”na sani umma..nasan bazaki taba barin ta shiga damuwa ba…Allah ya saka maki da alkhairi umma for making everything here possible …thank you for getting me married to baby…without you this couldn’t have happened..so nagode nagode sosae umma…Allah ya saka maki da aljannah”…umma dake murmushi ta janyoshi jikinta ta shiga shafa bayanshi kawai…ita kanta tasan zatai kewansu.. especially shi da kusan duk problem dinshi itake solving…a hankali Taheer yace”am going to miss all of you umma”…still umma na shafa bayan nashi tace”and we are going to miss you both..Allah ya Baku zaman lfy da zuria dayyiba”… Taheer ya amsa da Ameen…cikin hikima umma ta shiga mai nasiha sosae kan zamantakewar aure…dukda tasan ya sani amma Yana dakyau a Kara tunatar dashi..nasihan nata ko na shiganshi sosae har ba karamin kashe mai jiki yayi ba.

A can wurin amarya kuwa..ummi da Nafisa nata Mata nasiha itama..Banda kuka ba abinda takeyi..sun dauki tsowon lokaci kafin su gama..Ummi ta dauki lafaya dinta yellow..wanda aka turara da turare shima snn ta nadeta a ciki…tana kallon Nafisa tace”ki kula da ita Nafee..bari inje in samu in Kira Taheer din..ban taho da wayn nawa ba”…Nafisa ta mike tareda karasawa inda Layla take ta zauna..ita Kuma ummi ta fita…Layla ta fada jikinta tana Kara sakin wani kukan…Nafisa ta rungumeta a jikinta cikin sigan lallashi tace”kukan ya isa haka Layla ko kinaso kanki ya fara ciwo ne..kiyi hakuri kinji duk wata mace da haka ta fara…ki nustu sosae Layla domin aure gareki yanxu…mijinki yana bukatar kulawarki sosae don haka kiyi kokari don Allah kiga kin biya mai duk wata bukatarshi…kiyi kokarin sauke duk hakkinshi dake kanki nasan shima bazai taba tauye maki hakkinki ba…sai ki dena wnn shashashancin don ke zaki kula da kanki snn ki kula da mijinki ma..ki zama jaruma Layla banda raki Banda gudun miji duk abunda yace kiyi kiyi mai Layla..duk abunda yace baiso ki bari kinji… InshaAllah zamuzo har gidan naku kafin mu koma..Allah ya Baku zaman lfy”…Layla najin duk abinda ta fada amma bata dena kukanta ba.

Ummi kuwa na fita ta wuce part dinta..Saida ta dauko wayanta snn ta shiga dialing number din Taheer…lokacin ya fito daga wanka..yana shiryawa Kiran ya shigo..yai picking tareda sallama a hankali…ummi tace”ka sameni part din abbanka yanxun nn”…tun kafin yai mgn ma ta yanke wayar…Yana kallon umma ya fada Mata abunda ummin tace…ita ta fara mikewa tace”kayi sauri ka gama ka fito..nasan an gama shiryatane”..Taheer Kai kawai ya iya daga mata..umma ta fita zuwa part din dad din nashi..shi Kuma ya karasa shiryawa snn ya fita.

Umma bata dade da shiga ba shima ya shigo..kanshi a kasa ya nemi wuri ya zauna…ummi na dubanshi tace”to ga Layla nan dai Taheer…ka dauketa ku tafi…I don’t have to remind you kan duk wasu hakkokinta dake kanka cox kai ba yaro bane…inaso ka riketa tsakaninka da Allah Taheer..karka cuceta Kuma kada ka bari wani ya cutar da ita… remember Amana ce yanxu a hanunka..sai kayi kokari kar Amana ya cika..Allah ya Baku zaman lfy ya kawo zuri’a dayyiba”…Taheer kanshi a kasa ya amsa da ameen a hankali…ummi ta mike tareda kamo Layla da har yanxu ke kuka jikin Nafisa…ta kama hanun Taheer din shima ya mike tsaye…kawai saita rungume su gaba dayansu tana hawaye… tasan tafi kowa farin ciki da wnn hadin nasu..da Layla da Taheer duk nata ne..ta Kuma San irin son da Taheer din ke mata bazai cutar da itaba…kawai she’s going to miss them…ta riga tayi sabo dasu gashi yanxu zasu tafi…a hankali Taheer yaji wasu hawayen tausayin mahaifiyar tashi sun zubo kan face dinshi…yasan su kadai gareta…Layla kuwa dama kukanta yafi na kowa…sundauki kusan 6 mins a haka kafin ummi ta sakesu a hankali snn ta juya tareda shigewa bedroom..Nafisa ta mike tabi bayanta da sauri…ita Kuma umma ta karaso inda suke ta rike hannayensu cikin nata snn suka fita daga part din…har bakin mota umma ta rakasu..bayan ansa akwatin kayan Layla a motan…Saida ya bude mota ta shiga snn shima ya shiga…Yana ganin umma na musu waving har suka fice daga gidan…shi kanshi gaba daya jikinshi a sanyaye yake…tausayin ummin yakeji sosae…yasan dole zataji ba dadi..dama shi kadai ta Haifa kwal..sai Laylan da aka basu…yanxu gashi duk sun tafi sun barta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button