Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Wannan kenan

Bayan shekaru Sha daya,abubuwan da dama sun faru ciki hadda auren Ramla ‘yar autan umma tana nn zaune a abuja da Kuma sadiq shi Kuma Yana kano,sai kuma rasuwan mahaifinsu Nafeesa,da kammala secondary school din Layla lokacin she’s 17 years old.Sai kammala first and second degree din Taheer duk fannin medicine ynxu haka yanada clinc nashi na kanshi nan cikin Abuja snn akwai different hospitals da yake visiting Har zuwa wnn lokacin kuma baiyi aure ba bai Kuma San lokacinda soyayyan da yakema Layla ya rikide ya koma so irin na aure ba bayan bashida hope at all.

Follow n vote on Wattpad@ummuashraf22

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

06

Back to labari…

Ranan kusan raba dare sukai hira a parlor gaba dayansu har yaran,sai can dare snn kowa ya tafi daki ya kwanta.

Washe garima still hakan ne ya fari,sai bayan sun gama lunch Taheer yacema yaran su shirya zasuje unguwa,hakan kuwa akai duk suka shirya, Al’ameen, Ramadhan da Kuma Layla,sukayima su ummi sallama snn suka tafi.
Gidan Ramla suka fara biyawa wnn karon dai anyi saa Taheer ya shiga ciki Amma basu dadeba yace su tafi,yawo suka shigayi sosae,sunje parks iri iri sunje shopping,su Al’ameen sukace akwai park din da suke son zuwa don haka ya nufi can dasu.
Bayan sun fito a mota ya samu wuri ya zauna su Kuma suka shiga wasanninsu Yana gefe Yana kallonsu,yana Kuma lurada wata yarinya dake gefenshi sai kallonshi takeyi kmr ta samu tv,Yana Shirin barin wurin sai ga Layla ta zauna gefenshi tana mai murmushinta me kyau tace daddy wayana zan dauko cikin mota zamuyi pictures ne”ba tareda yace komai ba ya Mika Mata key din ta tashi ta tafi,tana Shirin bude motan taji sallama a bayanta,ta fasa budewan ta juya tana kallon mai sallaman,budurwa ce kyakyawa tanata murmushi,itama Layla murmushin tayi Mata snn tace sannu”yawwa”ta amsa Mata kafin taci gaba”don Allah sis taimako nakeso kimin idan ba damuwa”Layla ta gyara tsaiwanta tace umhum inajinki”yarinyan ta juya ta kalli Taheer snn tace don Allah wancan mutumin uncle dinki ne ko brother dinki? Layla ta juya ta kalleshi itama face dinta da murmushi snn tace”daddy na ne”yarinyan ta danyi shiru tana kallonta ta sake juyawa ta kalli Taheer din kmr dai bata yadda da abinda ta fada ba sai ta sake sakin smile tace to don Allah alfarma nake so kimin,tun da kukazo wurin nn nake kallonshi naji ya kwanta min a rai na Kuma kasa tunkaran inda yake,shine nakeso idan ba damuwa dn Allah kiyimin iso wurinshi inason yin mgn dashi,Layla daketa faman doka murmushi kmr an Mata albishir da aljanna tace”u don’t have to beg me plss,idan kika shawo kanshi ni kaina ba karamin farin ciki zanyi ba,so don’t worry bari inyi mgn dashi”tana gama fada ta juya zuwa inda yake zaune dama tun dazu Yana kallonsu Yana Kuma tunanin me suke tattaunawa daya sa Layla farin ciki haka.Ta karaso ta zauna dab dashi snn tasa hanu ta kamo nashi ta wani langabe irin yanda tasan idan tayi mai hakan yana saurin yi mata duk abinda takeso idanunta cikin nashi tace”daddy plss I want a favour from you”ya kauda kanshi gefe ganin yanda har yanayinshi ya fara sauyawa cikeda karfin hali yace”what”ta sake marairaicewa tace daddy waccan matan ne takeson mgn dakai Amma ta kasa zuwa shine tace i should talk to you Dan Allah daddy kar kace aah plsss,at least listen listen to her bakasan me Allah zaiyi ba”ya lumshe ido ya bude Yana sake jin wani baqon al’amari na ziyartanshi,da tasan yanda shagwaban nn nata keda effect a kanshi da bata ringa yimai Shiba,ya daure dai yace alright kice tazo”cikeda murna ta dago hanunshi dake cikin nata ta manna mai peck snn ta mike zuwa inda yarinyan ke tsaye,shiko Taheer mutuwan zaune tayi,gabaki daya ta hargitsa mai lissafi,yai kokarin daidaita kanshi ganin yarinyan ta kusa karasowa inda yake,idanunshi har sun canza launi”Assalamu alaykum”yarinyan ta fada bayan qarasowanta,ya amsa mata ciki ciki snn ya matsa Mata ta zauna,ba tareda ta kalleshi ba tace am sorry idan zuwana ya bata maka rai I just can’t let go of you ne,Amma Dan Allah ko digits dinka ka bani inyaso sai muyi mgn ltr,ya juyo yana kallonta ba yabo ba fallasa yace don’t worry Fadi abinda Zaki fada kawai”ta Dan gyara zama snn tace first inaso in tambayeka yarinyan can tacemin Kai dad dinta ne,da gaske ne?bai san sanda wani murmushi yai escaping lips dinsa ba,Yana kallon cikin idonta yace”ba gaskiya bane,she is my wife”ta zaro ido tace u mean wannan din matarka ce?ya girgiza Kai still smiling yace ya naga kinyi mamaki,baa riga anyi auren ba ai,yarinyan ta Dan kauda Kai snn ta qaqalo murmushi tace shknn Ni zan tafi,am sorry for disturbing u”bata jira cewarshi ba tayi gaba da sauri,shi Kuma ya bita da kallo Yana murmushi ya shafa beared dinshi yace”good girl”Layla na ganin ta tafi ta qaraso inda yake da sauri tana Dan turo baki tace dady me kace mata?ya danyi murmushi snn yace bance Mata komaiba”Amma naga ta tafi ranta a bace nidai am sure ka fada mata wani mgn”ya kamo hannayenta yace of course na fada Mata wani mgn,I have told her ni inada wadda nakeso”ta zaro ido da sauri tace Dan Allah da gske dady,Amma meyasa baka taba fadamin ba,I want to know her plss”murmushi kawai yakeyi Yana shafa gemu yace je kirawo su Al’ameen mu tafi”but dad…bata karasa ba ya katseta”just go and call them baby don’t waste my time”bata sake cewa komai ba ta kirasu,suna zuwa Kuma suka shishiga mota suka tafi.
Saida ya sai musu kayan makwalashe snn suka nufi gida,Layla ce kadai ta shiga ciki su Kuma suka wuce masjid don time din sallah yayi.
Itama Layla bayan tayi sallah bata fito parlor ba Saida tayi isha’i,ba kowa parlon sai nafeesa data fito itama ynxu,ta kalli hibba dake bacci kan kujera tana kokarin daukanta saiga Layla,ta fasa zaukan nata ta zauna tareda daukan remote tace da Layla”dauki hibba ki kaimin ita daki”Layla ta zaro idanu tana kallon nafeesa tace”mami banji me kikace ba”cewa nai ki dauki hibba ki kaita daki,ta sake maimaita Mata,Layla ta Dan marairaice tace”Mami Allah bazan iya daukanta ba”nafeesa ta juyo da mamaki tana kallon Layla tace ban gane bazaki iya daukanta ba,,ta sake langabar da kai tace Allah Mami bazan iyaba kinga tanada nauyi fa Kuma dady yace in dena daukan abu me nauy…bata karasa ba nafeesa ta cillo Mata pillow dake gefenta,tana Mata mugun kallo tace”kin dauketa kin wuce ko sai na gaura maki Mari,sa’arki ce ni da zan saki abu kicemin bazaki iyaba?Layla da har ya fara hawaye ta shiga kokarin daukan hibba dake kan kujera,ta dago hannayenta nafeesa ta daka mata tsawa”karyamin ‘yar zakiyi?Layla bakida hankali koh…daidai nan Taheer suka shigo parlon su Al’ameen na biye dashi,ya kalli Layla dake ta faman share hawaye snn ya kalli nafeesa yace”what’s wrong?yaya wai yarinyan nan ince ta dauki hibba ta kaimin daki take cemin wani wai bazata iyaba…ba tareda yace komaiba ya nufi inda Layla ke tsaye tana sharan hawaye,ya janyota zuwa jikinshi ya shiga share mata hawayen yace”it’s okay stop crying”nafeesa baki da hanci ta bude tana kallon ikon Allah,,ita data kawo mai kara instead of ya mata fada shine yake lallashinta…”yanxu yaya goya mata baya zakayi?kiri kiri nasata abu takiyi Amma har wani lallashinta kake..har ynxu Layla na jikinshi yace”ai ba cewa tayi bazayi ba koh?cewa tai bazata iyaba and mgnr data fada gsky ne bata iya daukan abu mai nauyi infact nine ma na hanata yin hakan,,still nafeesa da mamaki tace yanxu hibba har wani nauyi gareta da zatace bazata iya daukanta ba,..Saida ya zaunar da Layla kan kujera snn yace”wnn katuwar ‘yar taki koni da kyar idan zan iya daukanta”yanzu dai kana nufin bazata dauketa ba,,yace kiyi hakuri gsky ni Bari in dauketa,ya dagata ya kaita har daki snn ya dawo yace to an Kai maki ita sai hankalinki ya kwanta me ‘ya…ta danyi mai hararan gefe tace Kaine dai zaace me ‘ya,,,dariya kawai yayi daidai lokacin su ummi suka shigo parlon,,umma na kallonshi tace akwai fa mgnr da nakeson yi dakai son”ya danyi shiru kmr Yana nazari sai Kuma a hankali yace toh,ta mike zuwa daki ya mara mata baya yayinda ummi Kuma ta zauna nan parlon nafeesa ta shiga bata lbrin yadda sukai da Taheer din,ita kam Layla samu tai ta sulale zuwa dakinta tun kafin ummi ta Ankara da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button