Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Saida suka hau kan titi yace”umma amma dai baby bata San da mgnr bako”… murmushi umma ta saki tana kallonshi tace”hope dai ba tsoron ‘yar taka kakeji ba Kuma”…da sauri yace”I must be scared umma.. infact kunyarta ma nakeji wlh…ban San ya zata dauki wnn mgnr ba…umma do you think zata amince Dani despite ta daukeni a matsayin uba?…still umma na murmushi tace”InshaAllah bazataki amincewa ba son..ai she loves you”…Taheer na girgiza kai yace”ba irin wnn son take yimin ba umma…idont think she will accept me as hubby…I know she won’t”…ya karasa mgnr Yana hargitsa gashin kanshi…umma dake mai murmushi har yanxu tace”Taheer you are very funny wlh…yanxu babyn kakejin tsoro Kuma…well stop being afraid and think positive okay?…na fada maka I’ll always support you so worry not…ya juyo yana kallonta da murmushi shima yace”InshaAllah na dena ummata…I love you”…Saida ta kama free hand dinshi tayi pecking snn tace”I love you more my Son…angon baby”…wani murmushi ya subuce mai jin sunan da ta kirashi…ya sake kallonta yace”I love you”…ita kuma ta daga masa Kai tana murmushi.

Suna isa gida Taheer yaji zuciyarshi na wani tsalle kmr zata faso kirjinshi ta fito…a hankali ya bude motan ya fita bayan yayi parking…umma na lura da yanda yayi wani tsuru tsuru…ta kamo hanunshi ta rike cikin nata..har suka shiga bedroom din ummi…idanun Taheer a kasa a nemi wuri ya zauna nn kasa…ita Kuma umma ta zaune gefen gado…tunda suka shigo dama ummi ke binshi da wani matsiyacin kallo…ji take kmr ta kwada mai Mari don takaici…murya can kasa yace”umma barka da…..tun bai karasa ba ta daga mai hannu tace”rike gaisuwarka malam…bana bukata”…Taheer yai shiru kmr ruwa ya cinyeshi…cikin daga murya ummi ta fara mgn”ashe dama baka da mutunchi ban saniba…ashe mugu ne Kai Taheer baka da kirki ban saniba…yanxu ba kunya ba tsoron Allah Taheer…duk matan dake duniyar nn ka rasa wadda zakace kanaso sai Layla…Layla Taheer… yarinyar daka haifeta ka girmi uwarta Taheer… yarinyar dake maka kallon mahaifinta tana kiranka daddy…Taheer duk duniya ka rasa wa zakace kanaso sai ita sbd rashin Imani…ita Kuma uwarka ta goya maka baya sbd tsabar son kai…to wlh Bari kaji in fada maka…tun wuri ma idan zaka cire wnn tunanin daga ranka ka cire don muddin Ina raye bazan bari a cuci rayuwar yarinyar nn a aura mata tuzuru kmr ka ba…bazan taba bari a aura mata tsoho ba haka kawai kaje ka kashe mana ita…ashe dama duk soyayya da kulawar da kake bata ba don Allah kakeyi ba koh..kanayi ne sbd kanada mugun nufinka a zuci kana ganin zaka yaudaremu da wnn koh…to ko ka yaudari kowa Taheer Ni baka isa ka yaudareni ba…kuma muddin Ina raye wnn auren ba mai yiwuwa bane…Taheer da tunda ummin ta fara mgn yake hawaye..duk abinda ummin ta fada yasani gsky ne…gsky ne yayi ma Layla tsufa amma baisan ya zaiyi da soyayyar da yake Mata ba…a hankali yace”ummi kar kimin haka don Allah…wlh nima bansan ya akai sonda nake mata ya koma son aureba…amma wlh ummi duk abinda nayi mata banyi da wata manufa ba…ki taimakeni ummi wlh idan ban auri baby ba mutuwa zanyi”…ummi ta shiga salati tana tafa hannaye tace”Kai dai bakada kunya wlh Taheer…yanxu Laylan kake cewa idan baka aure taba mutuwa zakayi…ko kunyar mgnr nn bakaji ba dn Allah…to wlh ko kukan jini zakayi kayi ni bazai dameni ba…shiyasa knn kaketa min zaune a gida kaki maida hankali Kai auren..Ashe Kai kanada mugun nufi cikin ranka…to ta Allah ba taku ba…Kuma aurenka da Sameera ba fashi”…Taheer zai sake yin mgn cikin tsawa ummi ta katseshi da fadin”karka cemin komai malan..ka tashi ka bani wuri”…bai sake yunkurin mgn ba ya mike da kyar…yana hada hanya ya fice daga dakin…umma dake gefe tana kallonsu tun dazu…a hankali itama ta mike tabi bayan Taheer…ta karasa da sauri inda yake ta rikoshi da kyau…ganin yanda yake tafiya kmr Dan maye…a hankali ta shiga janshi har zuwa dakinta…ta zaunar dashi bakin gado itama ta zauna…tayi cupping fuskarshi da hannayenta..with so much concern tace”Taheer calm down plss..ka dena wnn kukan..duk maganganun da yaya ta fada ranta ne a 6ace..na tabbata ba har cikin zuciyarta ta fada ba..kayi hakuri yanxu ka dena wnn kukan… InshaAllah sai inda karfi na ya kare kan wnn mgnr…I won’t let you suffer son..so ka dena damun kanka don Allah”…a hankali Taheer ya shiga girgiza kai yace”ummah…zuciyata umma…umma ki taimakamin don Allah…kiyima ummi bayani..indai ban auri baby ba wlh mutuwa zanyi…ki taimakamin plss”…wnn karon saida umma tayi hawaye sbd tausayinshi…wane irin so ne Taheer kema Layla haka…tasa hannu ta janyoshi jikinta…ta shiga patting bayanshi a hankali tace”I promise sai inda karfi na ya kare Taheer..don Allah ka sassautama kanka wnn damuwan..kar wani ciwon ya kamaka”…Taheer dake rungume jikinta bai iya cewa komai ba…wani irin zafi yakeji cikin zuciyarshi…ya tabbata duk dauriyar shi wnn karon indai ummi ta dage kan mgnr nn zai iya kwanciya asibiti…all this while yana daurewa ne baison kwanciya amma a yanda yakeji yanxu…if care is not taken zai iya loosing rayuwarshi gaba daya…da sauri ya mike daga jikin umma…yana kokarin tashi tsaye umma ta rikoshi”Ina Kuma zakaje”…ta tambayeshi with concern…cikeda karfin hali Taheer yace”magani zanje in dauko umma.. I want to sleep..banason zuciyata tana tunanin nn..indai ba maganin nasha ba bazan iya bacci ba na sani..and I want to stop thinking of all that has happened umma…I want to get rid of my worries plss”…Saida umma ta goge hawayen da suka zubo mata..snn a hankali tace”you should relax..Bari inje in dauko maka”…yace”umma I don’t want to sleep here plss..nasan kona fara baccin baby na shigowa zan tashi and I don’t want that”…hannu umma tasa ta kwantar dashi kan gadon..ta mike tsaye snn tace”I can’t leave you all alone Taheer..kayi baccinka a nan..I promise bazan Bari Layla ta shigo ba..so tell me inda maganin yake in dauko maka”…idanunshi a lumshe yace”cikin first aid box”…umma najin haka ta dauka key din part din nashi..snn ta fita…da saurinta ta shiga ciki…ta rarumo gaba daya first aid box din ta taho dashi…don batasan takamaiman maganinda yake so ba…tana zuwa ta bashi..ya mike zaune da kyar ya dauko drug din ya balla…umma ta Mika mai ruwa..yasha snn ya sake komawa ya kwanta..ita Kuma tai zaune kawai tana kallonshi…Saida ya jima snn baccin da yake bukata yayi gaba dashi.

A Daren ranar…ummi ta shigo dakin Layla tana dubanta tace”yanxu Zaki Kwanta ne”…Layla tace”eh ummi..daddy kawai nake jira yazo yamin addu’a sai in kwanta”…ummi da daure fuska snn tace”to dauki abinda zaki bukata ki wuce muje dakina”…ba tareda Layla ta kawo komai a ranta ba..ta shiga gaba ummi na binta a baya suka fita..don ba abinda zata dauka a dakin…suna shiga dakin ummi..ummin tace”to hau gado ki kwanta..Allah ya bamu alkhairi”…da mamaki Layla ta dan dubeta snn tace”anan zan kwana ne ummi”…ummi tace”eh”…da sauri Layla tace”ummi to Bari in dauko wayana in Kira daddy ince mai zan kwana a dakinki…kar yazo yimin addu’a bana nn”…a fusace ummi tace”kina fita daga dakin nn sai na gaura maki Mari wlh…kanin ubanki ne Taheer din da sai kin wani cemai Zaki kwana a nn dakin”…a hankali Layla tace”ummi addu’a fa zaiyimin”…ummi tace”idan kika sakemin mgn saina cicci miki wlh..addu’an ne baki iyaba da sai wani yazo yayi miki snn zakiyi bacci”…mamaki sosae ya kama Layla jin abubuwanda ummi ke fada”..tadan turo baki snn tace”ummi daddy na fa nake nufi ba wani ba”…wnn karon ummi Saida ta jefo Mata carbin dake hanunta tace”bakazi shiga taitayinki daniba ko Layla..na sakeji kin ce daddynki sai na babbalaki a gidan nn”…Layla tayi shiru tana ganin latest attitude din ummi…to meya faru…kodai daddy yayi Mata laifi ne…why take cewa kar ta sake kiranshi daddy…da sauri ta hau gado ta kwanta tareda kudundune kanta cikin bargo ganin ummi tayo kanta gadan gadan…still tana turo baki ta shiga kunkuni..”naga dai babana ne..to meye idan nacemai a dakinki zan kwana”…iyaka tunanin Layla ta kasa gane dalilinda yasa ummi ke behaving haka…har bacci ya dauketa tana addu’an Allah yasa idan daddy yaje dakinta bai ganta a can..yazo dakin ummi..ta riga ta saba duk dare sai ya Mata addu’an nn takejin dadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button