Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A hankali yake tafiya don baiso sugane yana binsu…gaba daya he’s worried about her..meyasa ummi zata hanashi dubata…snn meyasa zaa barta ta fita da mayafi kadai..ko hula fa babu a kanta..almost rabin gashinta duk a waje.

Tafiyan almost 13 mins sukayi yaga sun shiga wani private hospital…yai kasake kawai Yana kallon motarsu daya shiga ciki…yanzu ummi ta gwammace ta kawota wani katon banza ya dubata a kan shi ya dubata…laifi ne don yace yanson Layla ko laifinshi ne don an daura musu aure bata saniba…gaba daya he’s becoming more angry than before…bai shiga da motan ciki ba yai parking nan waje snn ya fita ya shiga cikin clinic din…ya sauke ajiyar zuciya daya tuna mai clinic din is his colleague..so at least zai nemi alfarmar a barshi ya dubata and zai samu.

Suna shiga reception ummi ta nemi wuri ta zauna tareda rike Layla a jikinta…umma da Nafisa Kuma suka tafi don bude Mata file…Taheer kam cikin wasu mutane da yaga zasu shiga ciki ya shiga..Yana tsakiyarsu suka shiga wurin…Allah ya taimaka dai ba Wanda ya ganshi a cikinsu… Kai tsaye ya wuce office din abokin nashi…yana kokarin yin knocking sai ga abokin nashi ya fito daga office din…ya wara ido yana kallon Taheer din yace”what a suprise..yau Dr.Taheer ne a clinic dina”… Taheer yai murmushi yace”wlh nine Dr.Umar…wani alfarma nake nema wurinka plss”…Dr.Umar yace”ok mu shiga daga ciki”..
Saida suka shiga suka zauna snn Taheer yace”you know..matata ce aka kawota clinic din nn yanzu..batada lfy and ummi na fushi dani..taki bari in dubata..shine nakeso plss ka Bari in dubata da kaina”…Dr.umar ya daga Kai snn yace”bakada problem Dr…yanzu dama fita zanyi so In na fita zan turo maka ita..saika dubata a nan”…da sauri Taheer yace”yawwa friend…na gode sosae”…Dr.Umar na murmushi ya fita daga office din….ya samu su ummi a reception ko file din ma basu bude ba yace”ummi kece a clinic Dina yau”…ummi na kallonshi tace”wlh nice Dan nn..kaga yarinyace ba lfy wlh”…Dr.umar yace”ba matsala ummi taje office dina ta jirani..yanxu zan dawo sai in dubata…abokin Taheer ne ni ai”…ummi na murmushi tace”Allah sarki..bari muje office din toh”..da sauri dr.umar yace”No ummi ita kadai zataje ai…kinsan yanda yanayin aikin namu yake..in ana bukatar wani abu sai a kiraki”…ummi ba don taso ba ta koma ta zauna snn tace”to shknn”..dr.umar na murmushi ya kalli Layla yace”yawwa baby muje koh”…ba musu Layla ta shiga gaba yana binta a baya..da kyar take tafiya..saida sukaje har kofar office dinshi snn yace”ki shiga ciki ki jirani..ynxu zan dawo”…ba tareda ta kawo komai a ranta ba bude kofar ta shiga…tana cin karo da Taheer ta juya a rikice ta shiga kokarin bude kofar zata fita…ya karaso inda take da sauri yasama kofar key…sai ta durkushe a wurin tareda sakin kuka…Taheer ya risina ya kamota da sauri…yasa hanu ya toshe Mata bakin…ganin zata tara mai jama’a…ta runtse idanunta gam..kirjinta sai sama da kasa yakeyi…Taheer yai tsai yana kallon yanda ta zabura daga ganinshi…duk sai yaji he hates himself daya furta cewar yana sonta…da bai fadaba duk da bazaayi hakan ba…ya kama hanunta a hankali ya zaunar da ita kan kujera…shima ya zauna Yana kallonta da kyau yace”baby am very sorry plss…ki yafemin dn Allah..nasan I was too selfish but wlh sonda nake maki ne duk ya janyo haka…kiyi hakuri ki dena kukan nn..I promise zan sawwake maki tunda baki Sona…i don’t want to be seeing you like this…don Allah stop crying and tell me abunda ke damunki”…Layla dai bata bar kukan da takeyi ba..Kuma bata bude idanunta ba…yana kallon gashinta da rabinshi ke waje yace”why did you come out like this…Ina hijab dinki”…Layla kukanta kawai take batace komai ba…a hankali ya durkusa nan gabanta..ya kamo hannayenta ya rike cikin nashi…murya a raunane yace”zaki fasamin zuciya baby…don Allah ki dena kuka…you are making me feel guilty”…ta tsaida kukan nata tareda zare hanunta dake cikin nashi…ta goge tears din dake idonta Kuma har yanxu bata bude idon ba…Taheer ya mike tareda komawa inda yake ya zauna idonshi a kanta yace”yanxu Ina ke maki ciwo”…”Kai na”ta fada a takaice…yace”bayanshi Kuma sai me”…ta sake cewa”zazzabi”…Taheer yai shiru kawai…Yana kallon yanda take mgn without looking at him…bai taba tunanin akwai rana da zatazo..wai baby taji batason ganinshi ba…lokaci daya zuciyarshi ta sake karyewa…sai yaji kmr ya rushe da kuka…itama da yake so kmr zai mutu ba sonshi takeyi ba..inaga su ummi Kuma..shi dama yasan wnn abune mai kmr wuya…he thinks he’s going to divorce her kawai if that will make he r happy…he always wants to see her happy…ya daure ya kakalo murmushi snn yace”shknn inda ke maki ciwo”…ta daga mai Kai kawai…yace”alright don Allah ki jirani a nan..zanje in siyo drugs in kawo maki”…ta sake daga kai…shi Kuma ya juya ya fita..Saida yai locking dinta ta waje snn ya tafi..don bai yadda da itaba…Yana zuwa pharmacy ya siya drugs din da yakeso snn ya koma office din a gaggauce…ya bude kofar ya shiga…tana nn zaune inda ya barta..ko idanun bata bude ba..da gaske ko ganinshi bata sonyi…jiki a sanyaye ya karasa tareda daukan pen kan table…ya zana Mata prescription na drugs din a jiki snn a hankali ya Mika Mata ledan yace”take”…ta miko hannu ya Dora Mata ledan a Kai snn ta mike tsaye…har takai bakin kofa taji yace”don Allah kar ki cema ummi ni na dubaki…and kar ki kara fita without wearing hijab pls “…ta daga Kai kawai alaman toh snn ta fice daga office din…Taheer ya koma ya zauna tareda dafa kanshi da hannayenshi…wnn shi ake Kira tsaka mai wuya…gaba daya duniyar yaji ta fice mai a rai…komai ya denajin dadinshi.

Ummi na ganin Layla ta dawo..ta mike da sauri tareda rikota..ta amsa ledan hanunta tace”wnn meye Kuma”…da kyar Layla tace”magunguna ne”…ummi ta kama hanunta suka nufi hanyar fita snn tace”inace rubutawa zaiyi sai ya bamu katin mu siya..shine zai siya da kanshi Kuma”…itadai Layla batace koma ba…suna isa bakin mota Nafisa ta bude ta shiga..umma ma ta shiga front seat..Layla da ummi Kuma suka shiga back seat.

Dr.Umar ya shigo office din ya samu Taheer zaune…yana dariyar shakiyanci yace”Dr.ashe baby ta zama Matarka Kuma…ka tuna me kake fada Mana a school idan mukace son yarinyar nn kake”…Taheer yai shiru ya rasa abun cewa…shaf ya mance dr.umar din ya San lbrin Layla a wurinshi…bazai manta ba lokacin suna school daidaikun mutane ne basu sanshi da baby ba…wani lokacin kafin a gama lectures zai gudu..idan aka tambayeshi sai yace”baby naje na gani”…ya sauke ajiyar zuciya wato tun tana tsumma yake sonta ganewa ne kawai baiyi ba sai yanxu.

Bayan kwana biyu…

Nafisa da yaranta nata shirye shiryen komawa gobe…ummi tace tunda an fasa bikin ya kamata su koma gida haka nn…ta hadama Layla kayanta.. don tace tareda ita zasu tafi…Nafisa dai kmr tace bai kamata su tafi da Layla ba tunda yanzu she’s married..sai Kuma tayi shiru…tasan tana fadar mgnr nn to ummi ta inda ta shiga ba ta nan zata fita ba..sai taja bakinta ta tsuke tareda zubama sarautar Allah ido.

A bangaren Taheer kuwa..duk Wanda ya sanshi a baya..idan ya kalleshi yanxu zaiyi tunanin yayi wata da watanni a kwance ba lfy sbd tsabar ramewan da yayi…tako Ina bugashi kawai akeyi…ya zamana ba inda zaije yaji sanyi…yayi regretting fadama umma yanason baby tunda gashi fadan baiyi amfani ba…gaba daya yanzu ko shiga part dinsu baiyi…da safe dai kafin ya fita zaije ya gaishesu Wanda umma ce kadai ke amsawa…idan ya fita Kuma bai dawowa gidan sai dare…umma ce kadai ke aiko da abinci a kawo mai..dukda baci yakeba..ita Kuma bata tambayeshi meyasa baici ba..yasan she’s very mad at him..and ya zama dole ya bata hakuri don hakurinshi na gab da karewa…tunanin yanda Layla ta mai dashi tamkar dodo ma kadai ya isheshi kafin ma azo kan mgnr ummi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button