Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Sai kannen amarya..su Ramadhan shadda sukasa brown..dinkinsu suma iri daya..sai Hibba da akai ma dogon riga da nata..sunyi kyau suma sosae..sun kuma fito a qannen amarya sakk.

Kasancewar taron ba maza..so iya Mata ne kadai a wurin..sai su Al’ameen din da suka kasance yara…kafin karfe 5 wuri ya cika sosae taro Kuma ya fara daukar harami..decor din wurin ba karamin kyau yayi ba..komai na gargajiya akayi..babu abinda ke tashi wurin sai kidan kwarya..????

Amarya Layla na zaune inda aka tanadar Mata..daga kasa Kuma..inda aka tanadar ma friends dinta ne..Wanda most of them daga cikin family dinta suke..sai Kuma family friends don ba wasu kawaye gareta ba…Hanna na zaune a wurin itama..ta shiga cikinsu sai ka rantse ba yau suka fara haduwa ba.

Bayan an gama ciye ciye..su ummi suka fita domin yin kamun…aka sakar musu kida suka shiga..akaita fesheta da turaruka kala kala ana sakin guda..Saida suka gama snn aka bada filin rawa..nan fa mutane sukaita shiga suna cashewa..abun dai sai Wanda ya gani…nima daga baya maida wayata nai cikin jaka na shiga fili na dan taka snn nafito.
Can na hango mutanena..members na Dr.TAHEER Fans Group sunata tikan rawa a tsakiyar fili????

A takaice dai baa tashi daga wurin ba sai after magrib..kowa ya watse..Wanda zasu gidajensu suka tafi..Wanda zasu kwana a nn Kuma kowa ya nemi masaukinshi..amarya Layla ma da brides maids dinta suka nufi inda aka tanadar musu.

Wanda suke son zuwa biki suyi mgn don a tanadar musu cards dinsu????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

29

Bayan Layla ta raka Hanna kofar gida sun tafi..ta koma ciki..tana kokarin kwanciya wayanta dake kasan pillow ya shiga vibrating…ta zauna gefen gado tareda janyo wayan daga inda take..gabanta ya yanke ya fadi ganin Taheer ne me Kiran..bata san me zaice ba yanxu Kuma..Saida ya kusa katsewa tai picking tareda Kara wayan a kunnenta…a daya bangaren Taheer yace”badai har kin fara bacci ba baby”.. Layla ta wani kwantar da murya..ita a lallai mai jin bacci tace”yanxu dai zan kwanta”…ajiyan zuciya Taheer ya sauke snn yace”thank God tunda baki fara baccin ba..baby ki fito waje in ganki plss”…ta wani zare ido sosae tace”kasan dai ba barina zaayi in fito ba daddy”…Taheer yace”ai ba Wanda zai san kin fito..ta kofan kitchen zaki biyo..Ina jiranki back yard”…Layla ta turo baki snn tace”Allah daddy idan aka kamamu nidai ba ruwana”…Saida ya saki murmushi snn yace”Kai baby..wai idan aka kamamu sai kace wasu marasa gsky.. InshaAllah ma babu Wanda zai ganmu..kiyi sauri kizo kinji”…yana gama mgn yai hanging call din…Layla daketa faman turo baki ta mike tareda daukan katon mayafi ta yafa kan long rigan baccin dake jikinta..snn a hankali ta fito daga dakin..Sadaf Sadaf ta ringa tafiya har ta isa kitchen..Kai tsaye ta bude kofan da yace mata Yana ta nan din snn ta fita…ta shiga duba wurin amma bata ganshi ba..tana Shirin juyawa bayanta ta duba nan ma..kawai tajita a jikinshi..yai hugging dinta ta baya..ya sunkuyo da kanshi daidai kafadanta yana cewa”baby I missed you so much”…itadai bata iya cemai komai ba don ba karamin tsoro ya bata ba…bayan yayi breaking hug din..ya dauko kujeru biyu dake cikin plastic chairs dake ajiye can gefe..da alama Wanda sukai amfani dasu ne yau..ya zauna kan daya snn itama yace mata”sit”…ba musu ta zauna kan kujerar…Taheer ya zuba Mata narkakkun idanunshi Yana kallo..murya kasan makoshi yace mata”kinyi kyau”..ta dago idonta da sauri ta saukesu kanshi..sai Kuma tai murmushi kawai tana girgiza Kai…Taheer ya matso da kujeranshi gab da nata..har gwuiwanshi na gugan nata..still idanunshi kanta yace”Allah baby da gaske kinyi kyau..komai kikasa yana miki kyau baby..shiyasa nakeda kishi sosae a kanki..banso kowa yana kallon kyawunki sai ni kadai”…Layla da magangunshi ke sata murmushi itama ta kada baki tace”ai kaima me kyau ne daddy..duk kayan da kasa suna maka kyau..and you always look 30 not 40″..dariya sosae Taheer yayi kafin yace”baby yanxu dai kema kinaso kice nayi maki tsufa koh”…ta girgiza kai da sauri tana cewa”ni ba haka nake nufi ba..Ina nufin you are the perfect man for me”…Taheer bai san lokacinda ya sake hadata da jikinshi ba tsabar dadi..kalamanta ba karamin faranta mai sukai ba..ya Kai bakinshi saitin kunnenta murya can kasa yace”I love you so very much baby..I love you to the moon and back”…itama yau dai ta bude bakinta tace”l love you more”…Taheer ya dagota da sauri yana kallonta not believing his ears..did she just said she loves him..if he can recall rabonda ta bude baki tace mai I love you tun kafin ya furta yana sonta sai yau…yasa hanunshi yai cupping face dinta yace”what did you just said baby..say it again plss”…Layla na girgiza kai tareda boye face dinta a chest dinshi tace”ni kunya nakeji daddy”…Taheer ya shiga kokarin dago fuskan nata daga jikinshi yace”then lemme kiss you tunda kunyana kikace kinaji”…aiko da sauri ta bar jikinshi tana fadin”sorry ba kunya nakeji ba”…shima yana Mata murmushi yace”kin manta deal dinmu koh..daga yau duk kika sake cewa kinajin kunyana i must kiss you”…tana gyada Kai da sauri tace”na yadda”…Taheer ya mike tsaye tareda zira hannayenshi cikin aljihunshi yace”bari inzo in wuce baby tunda na ganki..yanxu xakiji wancan dan iskan ya fara damuna da waya”..itama ta mike tsaye tana fadin”to Saida safe”..yace”Allah ya kaimu..amma ki fara shiga tukuna sai Nima in tafi”..bata sake mgn ba ta bude kofar ta shiga..ya matso inda take tareda manna mata peck a goshi snn ya juya ya tafi…itama ta rufe kofar snn ta koma cikin gidan..Kai tsaye ta wuce dakinta..inda some of brides maids dinta ke kwance suna bacci..ta tsallakesu itama tareda kwanciya kan gado ta rungume pillow..tanata tunaninshi a haka har bacci yai gaba da ita.

Shiko Taheer dama daga gidan Yusuf yazo..don tun jiya dayaga gidan ya cika taf..ya dauki duk abunda yasan zai bukata ya wuce gidan Yusuf inda some of abokanshi wanda ba cikin Abuja sukeba..suka sauka a boy’s quaters na gidan Yusuf din..shima ya shiga cikinsu..don seriously bayason hayaniya.

Friday…

Yau ya kama zaayi dinner..duka bangarori shirye shiryen tafiya dinner din kawai akeyi.

A can gida kuwa..yauma kmr jiya da wuri make up artist ta iso gidan don yima amarya kwalliya.

Su umma suma kmr dai jiya..yau wani dokakken lace sukasa purple color..dinki da komai nasu iri daya…yayinda Nafisa da Ramla kuwa sukasa irinshi amma nasu pink..daidai da dinkinsu iri dayane..sai hibba itama da akayi mata fitted gown dinta..akayi mata turban style a kanta..sai ta fito dass da ita kmr yammata.

Su Al’ameen kam yau getzner sukasa fara qal..hadda mahaifinsu..dinkinsu Kuma kaf iri daya.

8:pm daidai ango yazo daukan amarya domin tafiya wurin dinner din…da yawa daga cikin jama’ar dake gidan kuwa duk sun tafi wurin..’yan kadan suka rage Wanda basu tafi ba..amarya Layla dake sanye cikin wani dan ubansun gown..na material mai walwali..silver..head dintama silver..haka purse da shoe…wuyanta na sanyeda wata hadaddiyar diamond necklace ita kanta sai walwali takeyi… inshort amarya tayi kyau fiyeda ma jiya..ga gown dinta ya fito da ainihin shape dinta…tana takawa a hankali kmr wata queen yayinda Hanna da wasu mutum biyu daga friends dinta suka sanyata a tsakiya…har main kofan da zata fito daga parlor motan da zata dauketa yazo..Taheer dake cikin motar idanunshi na kan kofa..saida gabanshi ya Fadi da yaganta..don wurin akwai haske sosae…da sauri wani friend din Taheer mai suna Salim wanda shike driving motan nasu..ya fito tareda zagayawa ya bude mata motan…Hannunta rike cikin na Hanna har suka zagaya wurin…a hankali ta shiga cikin motan…Taheer ya lumshe idonshi da sauri jin wani fitinannen qamshi dake fita a jikinta..shima Yana sanye cikin dokakkiyar getzner dinshi ash colour..dinkin babban riga..tun daga kan hula dake kanshi..zuwa su wrist watch da takalmi duk matching clour ne…askin da yai sai ya maidashi kmr dan 35..fuskanshi ya Kara haske ga Kuma siririn sajenshi dayasha gyara suka hadu da gemunshi sai suka sake fito da asalin kyawunshi…bayan ta shiga Hanna ta rufe motan snn ta juya itama tareda sauran friends din suka nufi inda motar mijinta suka shiga..su suka fara fita daga gidan snn motan amarya da ango ma ya fita…Taheer da tunda ya runtse idanunshi bai sake budewa ba har yanzu..ya shiga karanto duk addu’ar dayazo bakinshi…yanajin yanda abubuwa biyu sukazo suka tsaya mai a makoshinsi..na farko dai kyawun da yaga tayi..sai yaji tamkar ya maidata cikinshi tsabar shaukin da yaji yana fizgarshi…na biyu kuma tsananin kishin yanda zata shiga cikin dubban mutane da irin wnn dressing ba tareda ko mayafi ba balle hijab…wnn abun yafi komai tsaya mai a rai…ita kuwa Layla tunda ta dago taga idanunshi rufe bata kawo komai a ranta ba har suka karasa wurin…tun daga waje dama zakasan hall din ba karamin hadadde bane tun ma kafin ka shiga ciki…bayan Salim yayi parking sai ya bude motan ya fita…shi Kuma Taheer ya shiga bude idonshi da yai jajir a hankali har ya saukesu a kanta…cikin karfin hali yace”baby kina nufin a haka Zaki shiga wurin nn wai”…Layla ta dago da kanta itama tana dubanshi tace”eh mana daddy..ko banyi kyau bane”..tun kafin ta rufe baki yace”mgnr kyau ma kikeyi baby..kin ganki kuwa”..sai ya shiga girgiza kai yana fadin”bansan tsaustayin daya kaini amincewa da dinner bama in the first place…da nasan haka zakizo dinnern baby da wlh ko kusa ma bazan taba amincewa ayi dinner ba”…Layla da magangunshi suka bata mamaki tace”wai me ya farune daddy..ban gane me kke nufi ba”…a dan fusace yace”baby babu inda zaki shiga a haka.. infact ko cikin motan nn bazaki fita ba”…ta zaro idanu tana fadin”wai me yake faruwa ne daddy..what’s wrong plss”…da sauri Taheer yace”oh tambayana ma kike..baki san meya faru ba right?..just take a look at yourself..baby you look morethan beautiful..you look very ravishing baby ta ya zan bari ki shiga cikin Alrijalu haka..ko mayafi babu”..da ganin yanda ya karashe mgnr zakasan ba karamin ciwo abun yamai ba…mamaki sosae ya kama Layla tana binshi da kallo a hankali tace”amma daddy haka akeyi fa..Kuma f…bata karasa ba ya katseta da fadin”keep quiet..don haka akeyi ance maki you are thesame da sauran matane..you are different… you are mine don haka babu inda zakije daga cikin motan nn”…kafin tayi mgn taji ana knocking motar ta saitin da yake…a hankali yai winning glass din..sai yaga umma…tana dubansu tace”malamai ku fito mana..ga Wanda zasu shiga daku ciki nn sun shirya”…tana rufe baki Taheer yace”umma baby bazata shiga wurin nn a hakaba..kalleta fa ko mayafi babu”…umma na kallonshi baki bude tace”ban gane me kake nufi bafa Taheer”..ya sake cewa”umma ki kalleta fa kiga yanda tai kyau don Allah..ko mayafi batasa ba ga kayan jikinta sun matseta..ni da na san haka make up din yakema tun farko da bazaai Mata shiba wlh”…umma da mgnr shi ya kular da ita kawai sai ta bude motar tareda kamo hanunshi ta fito dashi…hanunshi na cikin nata ta zagaya inda Laylan take..itama ta fito da ita…ta jerasu wuri daya tareda sa hannun Laylan cikin nashi..tana mai mugun kallo tace”if you dare misbehave a wurin nn Taheer sai na saba maka wlh.. you’ll see the other side of me”…Taheer ya bita da kallo kawai da idanuwanshi da suka sake yin jaa..itadai Layla ko tari batayi ba…saida aka sake arranging yanda zaa shiga da amarya da ango …mace daya namiji daya snn a hankali suka fara tafiya zuwa cikin hall din..amarya da ango na tsakiya..Taheer na rikeda hanun Layla gam cikin nashi..sai mika hanu yake ta bayanta yana faman baza babban rigan jikinshi..wai a dole baiso a ga bayanta in tana tafiya…Saida umma ta sake dawowa ta gargadeshi da babbar murya snn ya dauke hanunshi.
Dj ya sakar musu waqan Bella Shmurda Ft Zlatan(Cash App)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button