Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

After like 15 mins ya dawo daukeda leda a hanunshi…ya karasa kusa da ita yaga har tayi bacci ma..ya dauko rigan daya siyo mata snn ya zauna a hankali ya zira mata rigan a jikinta.. ya rage kayan jikinshi shima snn ya kwanta tareda sanyata sosae a jikinshi feeling extraordinary happy.

Washegari ma Saida suka sake another round snn sukayi wanka suka fara Shirin tafiya can gidan don Taheer zaije daurin aure 11…Layla sai kumbure kumbure take ita a dole ya bata Mata rai…da kanshi ya dauko abayan daya siyo Mata jiya ya zura Mata a jiki..sai Kuma ya rungumeta yana fadin”nace am sorry fa baby..bazaki hakura ba ne..kuma mace maki ban karawa sai da kanki kince mn kinaso”…tana turo bakinta tace”ai nasan ba denawa zakayi ba..kawai kasa duk jikina yanamin ciwo”..sai ta fara hawaye…Taheer yace”come on baby mene abun kuka Kuma..na fada maki as time goes on zaki dena jin zafin..kiyi hakuri kinji”…da kyar ya samu ya lallabata ta karasa shiryawa suka tafi bayan shima ya shirya…dama tun jiya daya fita yaje ya taho da kayanshi ba tareda kowa ya ganshi ba.

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

47

Cikin mintina qalilan suka isa gidan..Taheer ya ba mai taxi daya kawosu kudinshi snn ya kama hanunta suka shiga ciki…kirjinshi sai dukan tara tara yake..bai san wane irin rikici xasuyi da ummi ba..Kai tsaye part din da aka saukesu suka nufa..ita kanta Layla zuwa yanxu gabanta faduwa yakeyi sosae..a haka suka shiga ciki..Ramla ce zaune a parlor tana daurama Hibba dan kwali..su Al’ameen Kuma na zaune a gefenta..suk sunyi shirinsu na tafiya daurin aure suma..abbansu kawai suke jira..Taheer ya karasa cikin parlon hanunshi cikin na Layla snn suka zauna…suna zama din Kuma sai ga umma ta fito cikin shirinta itama…da sauri Taheer ya mike daga inda ya zauna ya karasa inda umma ta zauna..Saida ya zauna kusa da ita snn yayi making pity face yace”umma dn Allah kuyi hakuri wlh ba laifina bane”…umma na girgiza kai tace”wai nace kayi laifi ne Taheer..ai ba laifinda kayi..kawai ka jira hakuduwanku da Yaya”…ta karasa mgnr tana dariya kasa kasa don tasan drama ne zaa Shashi tsakaninshi da ummi…tana rufe baki kuwa abun kmr hadin baki saiga ummin itama ta fito tareda Nafeesa..dama suna niyyan shiga cikin gidan ne tunda time na daurin aure ya kusa…ummi na ganin Taheer a parlon ta daure fuska tamau snn ta karaso ciki tana duban umma tace”Aisha ya kikazo kika zauna Kuma..muda zamu shiga cikin gidan yanxu”..tana gama mgn Taheer da kanshi ke kasa yace”ummi Ina kwana”..ta juyo a fusace tana kallonshi tace mai”rike gaisuwarka banaso..badai ni ka maida mutuniyar banza ba..ka tsalallako Taheer har wajen biki kaje ka sace ‘yar mutane snn ka kama gabanka da ita..sbd tsabar Wulakanci Kuma ko ka kiramu ka sanar Kuna tareda ita..haka kasa mukayita neman yarinya hankalinmu duk a tashe..kuma tsabar rashin kunya sai da kuka kwana a waje snn kake dawo mana da ita..wai yaushe ka zama tantiri ne haka ban saniba”..shidai Taheer shiru yayi yana sauraronta..sai da ta gama snn yace”dn Allah ummi kiyi hakuri..wlh banzo da niyyan in dauketa daga wurin ba kawai gani nayi tayi make up Kuma tanata rawa shine na dauketa..amma dn Allah ummi am sorry kinji wlh baa son raina bane”…yana rufe baki ummi ta sake cewa”to idan batayi kwalliya ba Taheer ya kakeso tayi..haka kakeso ta tafi wajen bikin fuskanta kmr dusa..yarinya da kuruciyanta da kyanta Kuma sai a hana Mata kwalliya kawai sbd kafi uban kowa kishi…kai daka tsinci dami a kala ma ai kamata yayi ka ringa lallaba yarinyar nn tunda dai kasan tafi karfinka..amma shine zaka fara iskanci sbd kana ga ai ka riga ka sameta koh..to baka isaba wlh..kuma idan baka shiga hankalinka daniba ranka zaiyi mummunan baci kaji n gaya maka”…murya a sanyaye Taheer ya sake cewa”to ummi naji Kuma na karba laifina dn Allah kiyi hakuri kinji”..tabe baki ummi tayi tana gyara zaman mayafinta tace”shikena Kuma ai..dama ni rashin kunya ne banso..duk ka sake irin wnn abun Kuma wlh kaji na rantse sai tayi wata hudu bata gidan naka..sai inga karewan iskanci”.. tana rufe baki Taheer yace”InshaAllah ma bazaa Kara ba ummi..thank you”…ita kuma ummi duban Layla tayi tace Mata”je ki sako kayanki sai ki samemu a cikin gidan”..a hankali Layla ta mike tana takawa a hankali ta nufi daki…su Kuma su ummi suka fita daga dakin don don zuwa main hause din…Taheer ya kama hannun su Al’ameen suka tafi wurin daurin auren tare tunda a kofar gidan zaayi daurin auren.

12 daidai suka dawo daga daurin auren…tare suka shigo gidan da Awwal da Kuma su Ramadhan..gaba daya Taheer sai yaji wani nauyinshi yakeji duk ya kasa sakewa dashi kmr da..dukda hiran da yake ta janshi dashi amma ya kasa sakewa har suka shiga part din dasu ummi suke…daidai lokacin suma duk suka dawo ciki…bayan sun zauna a parlor Awwal ya gaishesu with respect…ummi nata tsokanan Hibba da taje jikinshi ta lafe…
Nafeesa da Ramla suka kawo musu abinci kala kala da drinks suka ajiye musu…Taheer dama mikewa yayi don bazai iya cin abinci tare dashi ba…ganin zai fita sai umma tasa aka hada mai nashi daban..tasa aka Kai mai wani dakin…to anan ne ya Dan samu yaci dukda dai ba mai yawa ba yaci ba..

Bayan Sallhn Isha aka tafi Kai amarya…gaba daya su ummi sun tafi raka amaryan Layla ce kadai bata jeba..tana kwance cikin daki tana rama baccinda Taheer bai bari ta samuyi sosae ba jiya wayanta ya shiga ringing…cikin magagain bacci ta dauko wayan tareda picking call din..sai taji voice din Hanna na cewa”mutanen Jigawa”..Layla ta Dan bude idonta tareda mikewa zaune..a hankali tace”mama unborn how far..ya jikin naki”…Hanna tace”ganinan dai kawai Jakada abun baa cewa komai..tun jiya da dare nake Kiran wayan naki switch off”…Layla tace”wlh Hanna daddy ne ya kashemin wayan..ni banma saniba sai da safe na duba naga ashe tun jiya ma a kashe take”…Hanna tasa dariya sosae kafin tace”su love birds kice ana can ana fama..to Allah yasa ku dawo mana da baby”…tsaki Layla ta saki tace mata”ni matsala na dake akwai ki da donkey letter..wane irin mu dawo da baby kuma ana zaune qlou”…Hanna tace”kmr yanda kikaji na fada dai hakan nake nufi..ynxu dai ba wnn ba..kinsan dalilinda yasa na kiraki”…da sauri Layla tace”aah”..Hanna tacigaba”AY Gambo ne yazo yayi test wlh jiya..kuma yace shine C.A dinmu and bazai yima kowa make up ba..shine naketa kiranki tun jiyan in fada maki ko zaki samu kimai mgn idan yaga kece maybe zai hakura yayi miki mk up din”…shiru Layla tayi tana jinjina al’amarin a cikin ranta..bata taba tunanin zaiyi C.A dinshi yanxu ba dukda dama can yace musu shi unannounced C.A yakeyi…a wani bangaren Kuma tana tunanin da kyar idan Taheer zai bari ta sake mgn dashi…Saida ta sauke numfashi snn tace”shknn Hanna nagode..zanyi mgn da daddy duk abinda yace shknn”..Hanna tace”to Allah ya doraki a kanshi..ni zan kwanta Saida safe”…cikeda tsokana Layla tace”as’habul Kahfi iyayen bacci”…itama Hannan tace”eh ba komai..kema naki turn din yana nn zuwa”…da haka sukayi sallama… Layla tayi shiru tana tunanin da kyar Taheer zai bari tayi mgn da AY Gambo..amma abune Wanda ya zama dole don haka babu yanda zaiyi dole haka zatayi mgn dashi din..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button