Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Shi kuwa Taheer Yana fita nearby eatry yaje ya siyo mata breakfast snn ya koma wurin ya bada a kai mata praying Allah yasa taci…

Yana nn zaune cikin mota ya sake dialing number AY Gambo praying Allah yasa yau dai ya shiga… luckily Kuma sai yaji wayan ta shiga…ya sauke ajiyar zuciya mai karfi Yana sauraron ringing din da wayan keyi…Saida ta kusa tsinkewa snn akayi picking…fuska a daure yace”kana mgn da Dr.Taheer Jakada”…AY yace”I know…ni kuma sunana Abubakar Yusuf Gambo”…Taheer ya tuno sunan da ta fada mai dazu AY Gambo…kafin ma yayi mgn AY din yace”dama ko baka kirani ba inada niyyan kiranka..akwai mgnr da nakesonyi dakai”…Taheer cikeda mamaki yace”you have some nerves..wace mgn zakayi dani kuma..anyways nima akwai mgnr da nake sonyi dakai”…a daya bangaren AY yace”yanzu I have classes to attend…amma 4 zan gama..so a Ina ya kamata mu hadu”…a takaice Taheer yace”Cilantro”…AY yace”alright zanzo wurin by 4 InshaAllah”…Taheer bai sake mgn ba yayi hanging call din…cikin ranshi yana zanyi maganinka ne..sai ka fadamin uban daya baka daman Kiran matata kana sending Mata love messages a wayanta..you fool”

Around 1:30 Taheer ya koma saloon don dauko Layla..3 hours din da suka bashi har ya wuce…so yake ya kaita gidan da wuri snn ya samu yaje su hadu da wancan mutumin..he’s eager yaji abunda ya taka da yake kula mai matarshi.

Reception din wurin ya shiga yace ayi mai mgn da ita…ba bata lokaci kuwa sai gata ta fito…tun daga nesa ana iya hango lallen dake hannu da kafanta wanda yayi maroon sosae..abunka da farar fata…sai lallen ya sake haskata sosae…Taheer couldn’t take his eyes off her…kallonta kawai yake yana Kuma kallon lallen da ya matukar tafiya da nutsuwarshi…Saida yai da gaske snn ya ida dauke idanunshi a kanta..cikin ranshi yace”damn she will be the death of me”…sai Kuma ya juya ya fita daga wurin da sauri…ita Kuma tabishi a baya…Yana karasawa inda motarshi take ya bude ya shiga..itama a hankali ta bude ta shiga…Saida suka fara tafiya snn ta mika mai ATM card dinshi dake hanunta tace”gashi”…ba tareda ya kalleta ba yace”drop it”…ta ajiyeshi a hankali nan kusa dashi tana kokarin maida hawayen daya ciko idanunta…tasan da dane tayi kitso da lallen nn tun a mota zaice saita nuna mai ya gani..amma yanxu kmr ma bai San me tazoyi ba..dukda tasan yaga lallen amma yayi kmr bai gani ba..wnn ma kadai ba karamin punishment bane a gareta…wnn chanjawan da yai yana damunta…

Haka suka cigaba da tafiya in silence har suka isa gidan nasu…yana gama parking ya fita..itama ta fito snn suka nufi entrance din gidan tare.

Umma suka samu zaune a parlor..ita Kuma ummi ta mike knn zata shiga dakinta sai gasu…da gudu Layla ta karasa ciki tareda fadawa jikin ummin tana rushewa da kuka…ummi na dubanta da mamaki tace”ke wai lfynki qlou kuwa..tun dazu kike kuka sai kace karamar yarinya”…ganin batace komai ba ummi ta maida dubanta ga Taheer tace”ko wani abun kayi Mata ne”..Saida ya zauna kusada umma snn yace”ni me zanyi mata ummi..ask if itama tayi min wani abu mana”…yana dan turo baki ya karasa mgnr…ummi ta tabe baki tana cewa”kaidai anyi babban kobo wlh..dubi yanda kake wani turo baki sai kace karamin yaro”…Taheer bai sake cewa komai ba..yayima umma side hug yana fadin”umma yunwa nakeji”…umma na shafa kanshi tace”meya hanaka cin abinci har yanxu toh”…baice komai ba sai idanunshi daya lumshe..yanajin idanun Layla a kanshi..ko baa fadaba yasan kallonshi takeyi…Ummi ce ta jata suka nufi dakinta tana cewa”muje ki fadamin idan ma cutar dake yakeyi”..suka bisu da kallo dagashi har umma..Saida suka shiga daki umma ta dawo da kallonta kanshi tace”tell me meyake faruwa ne..ita ta shigo tana kuka kaima kuma you look disturbed..fadamin menene matsalanku?..”Taheer ya danyi shiru kafin ya bata lbrin duk abinda ya faru..har wayan da sukai da AY Gambo dazu…sai daya gama bayanin ya dora da fadin..”umma am really disturbed..sai naga kmr nayi overreacting..i shouldn’t have slapped or shouted at her..am regretting all these umma..i couldn’t even say a happy birthday to her…kwana biyun nn ko abinci bataci..all because of me”…kana kallon fuskanshi zakaga tsantsan regret da Kuma rauni a tareda shi…umma na shafa kanshi tace”come on you worry too much.. bakayi laifin komai ba..and bakayi overreacting ba..abunda ta aikata ya cancanci kayi Mata abunda yafi haka ma..son da kake mata yasa kake ganin kmr baka kyauta ba amma you are not at fault..so ka dena damun kanka dn Allah..tunda anjima zaku hadu nasan zakaji komai daga gareshi”…ya dago kanshi yana murmushi yace”shiyasa nake sonki umma..you always find a solution to my problems..I love you”…ta saki dariya itama tace”I love you more..yanxu bari in zubo ma abincin kaci kafin 4 din tayi”…tana gama mgn ta mike zuwa kitchen..bata jima ba ta kawo mai abincin…ba laifi ya danci amma ba wani da yawa ba…yana kallon dakin ummi yace”umma itama fa bataci abinci ba”…umma tace”idan ta fito sai a zuba mata taci”…ya rausaya Kai yace”umma ko zakiyi mata mgn ta fito taci yanxu”…umma ta galla mai harara tana fadin”Kai meya haka na kirata da kanka”… yace”tsoron ummi nakeji”…umma ta sake yin dariya tace”ka bari su fito sai taci”…

Daga masallaci Taheer ya wuce Cilantro inda sukayi da AY Gambo zaku hadu a wurin…yana isa ya samu wuri ya zauna snn ya zaro waya ya shiga Kiran AY din…baiyi picking ba har ya gama ringing..yana kokarin sake kira Kuma sai ya hango wani na tahowa inda yake..dukda bai taba ganinshi ba..jikinshi ya bashi shine AY Gambon..sai ya fasa Kiran da zaiyi tareda ajiye wayan nashi kan table dake gabanshi…AY Gambo ya karaso ya zauna..face dinshi da murmushi ya bama Taheer hannu sukayi musabiha…
“AY Gambo right?..”cewar Taheer knn yana duban AY din…shi Kuma yace masa”yeah am the one”…Taheer bai sake mgn ba sai daya zaro wayan Layla dake aljihunshi…text message din ya shiga snn ya tura wayan gaban AY din Yana cewa”Kaine ka turama matata wnn text din?..”AY Gambo na kallon text din yace”eh nine”…Taheer ya sake daure fuska snn yace”who gave you the right…how dare you do that..a ina ka taba ganin anyi soyayya da matar aure”…Taheer na rufe baki AY yace”easy plss..nasan she’s not your wife..the fact that kana sonta ba shine zaisa ta zama Matarka ba..nasan komai dake tsakaninka da ita..nasan cewa kana sonta amma family dinku basu son baka ita..shine kake kokarin Koran duk wanda yazo ya nuna yana sonta ta hanyar cewa she’s your wife while she’s not…am sorry to say ni dai bazan koru ba gsky..sbd da gaske nake sonta bada wasa ba..and I want her to become my future wife..the mother of my kids”

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

40

Taheer ya runtse idanunshi gam yanajin yanda zuciyarshi ke tafasa..wai he want her to become his future wife..the mother of his kids…wnn words ba karamin lalata mai zuciya sukayi ba..the thought of someone saying zai aureta har ta haifa mai ‘ya’ya yasa yaji he wants to murder that person..like how dare he zaiyi tunanin auren matarshi har yai mata ciki ta haihu…ya dauki tsawon lokaci idanunshi rufe..sai maimaita innalillahi yakeyi har karshe..he wants to calm himself down don idan yace zaiyi mgn yanxu yana iya dura mai ashar…
shiko AY Gambo relaxing yayi yana kallon yanda bacin rai ya bayyana face din Taheer din karara..ya tabbata ba karamin so yake Mata ba kmr yanda shima din ba karamin son yake Mata ba…
Taheer Saida ya samu wutan dake ci cikin heart dinshi ya dan lafa snn ya bude idonshi da ya koma jajawur sbd bacin rai… yana kallon AY Gambon yace”didn’t she tell you she’s my wife”…AY ya dan daga kafada yace”of course she did..amma ban yadda da ita ba”…yana rufe baki Taheer yace”meyasa baka yadda ba”…Saida ya gyara zamanshi snn yace”sbd an sanar dani dama haka zata fada..sister dinta ta tabbatar min da cewa kaine kake sa tana koran duk saurayin da yazo wurinta ta hanyan cewa she’s married to you..so shiyasa ban yadda ba”…
Taheer goshi ya dafa yana wani irin huci don he’s becoming more angry…ji yake kmr ya shakeshi har sai ya dena numfashi…bai sake cewa komai ba ya dauki wayanshi da har yanxu ke ajiye bisa table..gallery dinshi ya shiga ya lalabo invitation card na bikinsu snn ya Mika mai wayan…Saida ya tabe baki snn ya karba wayan…ya gama karantawa tsaf snn yace”wnn bai isa prove da zaisa in amince she’s your wife ba”…Taheer dake matukar kokari wajen danne anger dinshi yace”alright bani wayan”…ba musu AY ya Mika mai wayan…yana amsa ya shiga folder din da pictures din bikinsu suke snn ya sake Mika mai wayan..karon farko da yaji inama daurin aurensu ba unexpected yazo ba…yasan da dole zaa buga invitation cards yanxu sai ya nuna mai…shikuwa AY shiru yayi yana kallon pics din daya bayan daya…yasan dai tabbas Layla ce jikin pics din haka ma Taheer din…ga Kuma family nn ya gani ga kuma hall nn shedan cewa fa biki ne na gske…ya dauki tsawon lokaci sosae yana nazarin pics din kafin ya maida ma Taheer wayan…cikeda rudu da mamaki yace”but how…knn hakan na nufin Sameera karya tayi min knn”…da sauri Taheer ya zaro idanu waje yana kallonshi yace”Sameera…wace Sameera kake mgn akai”…”Hang on”…cewar AY yayinda ya zaro wayanshi shima daga aljihunshi…ya nemo pic din Sameera ya mikama Taheer wayan yana cewa”here she is”…da sauri Taheer ya amsa wayan tareda kallon pic din daya nuna mai…idanuwa waje sosae yake kallon AY yama kasa mgn..da kyar yace”wait…a ina ka San Sameera…I mean are you two related”…da sauri ya girgiza kai yace”not at all..ban Santa ba..infact banma taba ganinta ba sai sanadin Jakada”…Taheer na gyada kai yace”go on”…
Saida ya sauke numfashi snn yaci gaba”tun ranar dana fara dora idanuna kan Jakada Allah ya jarabceni da sonta…nayi kokarin boyewa amma daga baya sai na kasa…a lokacin ko sunanta ban saniba…ina sane nace zan raba masu assignment dana basu da kaina..sbd ta haka ne kadai zan San sunanta…ta hakan Kuma na gane sunanta Maryam Jakada…the next day da na shiga school sai na tura Class Rep dinsu ya kiramin ita..amma sai yace min bata zoba..the other day ma haka..ganin na shiga damuwa sosae..Class Rep din nasu ke cemin ai ya santa..yace min da akwai sister dinta wai friend din sis dinshi ce…yace zai hadani da ita cox ita kadai zata iya shawo min kanta…ban kawo komai ba nace mai na yadda…washegari sai yazo tareda wnn Sameeran dana nuba maka..ita ta sanar dani alakan dake tsakaninka da ita..ta Kuma snr dani cewa kana sonta amma family dinku basu son baka ita sbd age gap dake tsakaninku…ta Kuma cemin ko Jakada zata shekara tana cemin she’s married kar in yadda sbd haka kake sata ta fadama samarinta sbd ka samu ka aureta…she said all sort of things wasu ma bazan iya tunawa ba…so na yadda da abunda ta fada and nayi amfani dashi…tun ranan dana fara Kiran Jakada office dina banyi wasting time ba nace mata Ina sonta..amma sai tacemin inyi hakuri she’s married..ban yadda da abunda ta fada ba sbd ancemin haka take fada..the following day dana kirata wlh har kuka tayi..she was begging me inyi hakuri in rabu da ita..that tana son mijinta kuma bataso wani abu ya shiga tsakaninta dashi…I still didn’t agree.. washegari na kirata a waya don har number dinta da address dinta Sameera ta bani..samething happens amma dukda haka ban yadda ba..ban Kuma sake kiranta ba sai wnn text dana tura Mata”…ya karasa mgnr cikeda rauni…
Taheer da yai shiru yana sauraron tuggun Sameera mamaki kawai yakeyi…is she this wicked dama har ya taba yunkurin aurenta…wato Allah ya taimakeshi knn da bai sa aureshi da ita ya faru ba..don da bazai taba gane this side of her ba..kawai sbd ta shiga tsakaninsu tayi using poor person da bai san mene alakarsu bama…tayi wasa da emotions dinshi kawai sbd ta cimma wani buri nata… innalillahi wainna ilaihi rajiun..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button