Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

I dedicated this page to all my fans..thank u for loving and reading Dr.TAHEER..Allah ya bar qauna????

28

Yau saura kwana Hudu daidai a fara biki..gida ya fara cika da ‘yan uwa na nesa…Nafisa ma ta dira…da yawa daga cikin family dinsu na kano ma duk sun hallara.

Da dare umma ta Kira Taheer kan yazo yaga kayan lefe..sun gama hada komai..don gobe ma idan wasu zasuje can gidan nashi..zaa tafi mata dasu…yana zaune umma nata aikin daga mai kayan yana kallo daya..ummi ta shigo dakin da sallama..ta dubi yanda umma keta nuna mai kayan sai tayi tsaki tace”yanxu Aisha da nace ba sai kin kirashi kin nuna mai ba Saida kika kirashin dai..idan sunje can karewan kallo ma a jikinta zata sa mai ya gani..to Kuma bai isaba sai an wani nuna mai kawai salon duk an gyara kaya a sake hargitsasu”..umma na ci gaba da nuna mai kayan tace”to Yaya mene laifi yanzu don an nuna mai..ai sai yaji dadi a ransa yaga shima yayi kokari”…a kufule ummi tace”au shine ma yayi kokari zakice..muda mukaita sintirin fita siyo kayan bamuyi kokari ba knn”..umma tace”ba haka nake nufi ba Yaya..kawai dai naga shima yayi kokarin bada kudi a wadace..kuma kayanda akai order wurin Amina Dubai duk ba shi yaje ya karbo su ba”…ummi tace”to ay shknn”..snn ta fice daga dakin…dakin Layla ta shiga tace Mata taje dakin umma itama wai taga kayanta..Layla tace”na riga na gansu ummi..ba sai na Kara ganiba”..ummi tace”ke kika sani dai..kema da baa maki gwaninta”tana gama mgn ta fice a dakin..Layla ta bita da kallo tana dariya..a fili ta furta”Hajia ummi rigima”.

Taheer na gama ganin kayan dama part dinshi ya koma..tun safe yake son ganin Layla amma abu ya gagara..ga gidan ya fara cika da mutane da Kai tsaye dakinta zaije ya sameta wlh…bayan ya gama duk abubuwan da zaiyi..sai ya hau gado ya kwanta tareda daukan wayanshi ya shiga dialing number dinta…Layla na daki tana karatu call dinshi ya shigo..ta ajiye handout dake hanunta snn tayi picking call din…a daya bangaren Taheer ya wani narkan da murya Yana shafa tummy dinshi yace”baby am seriously sterving..ki kawomin abinci part dina dn Allah”.. Layla ta zaro idanu kmr taga abun tsoro tace”daddy ummi bazata barni inzo ba ka sani”..tana rufe baki yace”ai ba cewa nai kije kice mata zaki kawomin abinci ba..kawai zuwa zakiyi kitchen ki dauki abincin sai ki faki idon kowa ki taho..kina zuwa zaki koma Allah ba wani abun zanyi maki ba..I just want to see you..yau duk mutanen nn sun hanani ganinki”…Layla dai tai shiru tana ayyana yanda zaai taje part dinshi ba tareda anyi noticing ba..a wani bangaren kuma tana tsoron abunda zai biyo baya idan taje din..ta fuskanci daddyn nn ba hakuri ne dashi ba..and bashi da kunya ko kadan…Taheer ya katse mata tunani da fadin”it’s okay idan baki son zuwa baby..i won’t force you..bari in fita waje kawai sai in nemi abinda zanc..”..tun kafin ya rufe baki tace”ai ba cewa nai bazan kawo ba daddy..zan kawo maka amma Ina zuwa zan wuce”..yace”na yadda baby..kiyi sauri Ina jira”..Yana gama fadin haka ya kashe wayar tareda ajiyeta nn gefe..sai doka murmushi yakeyi shi kadai.

Ita kuwa Layla suna gama waya ta mike tareda fitowa daga dakin..ta duba parlon Allah ya taimaketa ba kowa..don haka ta wuce kitchen da saurinta..ba bata lokaci ta hada komai kan tray snn ta dauki tray din ta fice daga kitchen din…sauri sauri take tafiya sbd kar a ganta..tana zuwa part dinshi ko knocking batai ba ta tura kofan ta shiga..ta wuce bedroom dinshi da abincin don tasan yana ciki..ko kallonshi batai ba..ta karasa ciki tareda ajiye tray din hanunta kan bedside drawer..ta juya da nufin zata tafi kawai taji ya riko hanunta..ta juyo fuska a kwabe tana kallonshi tace”daddy kace Ina zuwa zan koma fa..tsoron ummi nakeji wlh”..Taheer na murmushi ya janyota ta zauna gefen gadon..ya karyar da wuya yace”to kiyi serving dina mana..idan an kawoma miji abinci..zama akeyi ayi serving dinshi..Kuma sai an tabbatar da yaci snn ake tafiya”..Layla ta turo baki jin abin da ya fada..snn ta mike zuwa inda ta ajiye abincin..ta zuba mai a plate tareda sa spoon a ciki..sai ta juyo ta dora mai a kan cinya..ta sake juyawa zata tafi ya sake rikota ya zaunar gefenshi..ta sake turo baki da gani abu kadan take jira ta fashe da kuka…Taheer couldn’t help it but laugh..yanda tai kicin kicin da fuska ba karamin dariya ya bashi ba wlh..ya dauke abincin data dire mai a cinya tareda ajiyeshi gefe..ya sake kallonta..yana son yin mgn amma dariya ta hanashi..rabon da yayi dariya haka har ya manta..Layla da bakin ciki ya isheta kawai sai tasa mai kuka..ya kunshe dariyan nashi da sauri..ya janyota jikinshi yace”ya Salam..menene abun kuka Kuma baby”…ta shiga kokarin kwace kanta amma ya riketa gam..har yanxu dariyan na cinshi amma ya daure ya sake cewa”ok ok am sorry..sorry for laughing at you..kiyi hakuri bazan Kara ba”..taki cemai komai tana cigaba da kukanta..sai ya dago fuskanta ya shiga share mata hawayen yace”I said am sorry baby..kukan ya isa mana”..sai ta dena kukan itama ta shiga goge tears din..still Taheer na murmushi yace”ur silly daddy is sorry okay?..yanxu ki bari muci abincin sai ki tafi”…ta zaro idanu tana girgiza kai kmr zata fashe da wani kukan tace”Allah idan ummi ta ganni fada zatai min..nidai ka barni in wuce plss”…Taheer ya mike tsaye Yana fadin”to muje in rakaki”..ta zare ido tace”Tabb niba saika rakani ba..ka zauna kaci abincinka”…yai shiru tareda tsura Mata ido kawai…sai Kuma ya bude Mata hannayenshi yace”alright give me a hug indai kinaso in barki ki tafi ke kadai”…bata San lokacinda ta galla mai harara ba..sai ya kwashe da dariya Yana fadin”naga wnn kallon baby thank you..saura hug din”…Saida ta dauke kanta gefe baki a tunzure snn ta taka a hankali tareda fadawa jikinshi…ya maida hannayenshi yai hugging dinta dasu…sun dauki almost 5 mins a haka snn ya saketa a hankali yace”you are free to go now..Saida safe”…ba tareda tace mai komai ba ta juya ta fice daga dakin..Taheer ya bita da kallo har ta fice snn ya koma ya zauna tareda daukan abincin ya faraci..har yanzu bai dena murmushi ba..she really is amazing.

Layla na shiga parlor taci karo da ummi tsaye cikin parlon idanunta a kan kofa kmr dai akwai Wanda take jira..ta sukuyar da kanta da sauri tanajin hawaye na gangarowa face dinta..ummi ta karasa inda take tareda kama hannunta..ta shiga janta har daki..a fusace take kallon Laylan tana cewa”bakida hankali koh..uban me ya kaiki bangarensa”..Layla na hawaye tace”cewa yai in Kai mai abinci”…ummi taja tsaki tace”sbd ke doluwa ce shine kika kwashi jiki kika bishi har bangarenshi..baki san namiji ba kunya ne dashi ba koh…shahsahsa shine zaki dauki kanki ki kai masa”..Layla na kuka wiwi tace”Ummi nifa na wani abun yayi min ba..abinci kawai na kaimai..ai dai bazan barshi ya kwana da yunwa ba”…ummi na salati tace”lallai kin zama abinda kika zama Layla..yanxu nidin kike cema bazaki barshi ya kwana da yunwa ba..ke ‘yar dadi miji koh..to zancicci ubanku wlh daga ke har Taheer din..Allah ya kaimu gobe zaizo ya sameni”..tana gama fadanta ta fice daga dakin..Layla ta fada kan gado tana ci gaba da kukanta..abunda taketa gudu knn gashi nn ya ja Mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button