Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari…

Yauma dai kmr jiya haka Taheer ya tashi kmr mara lfy..gaba daya baida wani energy a jikinshi don ba wani abincin kirki yaci ba..baima da appetite din da zaici abincin kwata kwata..haka ya gama shirinshi sukuku snn ya tafi clinic…zuwa yanxu ji yake bazai iya bari har sai jibi snn ya tafi Dutse ba..ya zama dole yayi wani abun don baijin zai iya tashi lfy gobe idan bai sanyata a idonshi ba..sai ya kira wani yace a bincika mai in da akwai available flight da zaije kano yanaso…luckily Kuma an samu da akwai amma sai gobe Friday zai tashi karfe 8 na dare…dukda Taheer baiso haka ba..amma haka ya siya ticket din don a yanda yake din nn baijin zai iya driving daga Abuja har zuwa Dutse..yau ma Kuma ko kadan bai kirasu ba..Kuma bawai don bayason Kiran bane..ah ah kawai sbd duk yana fushi dasu ne..

Dutse…

Yau sun tashi da shirin yin kauyawa party da zaayi a cikin gidan…kowa sabgan gabanshi yake amma Layla ta kasa samun sukuni at all..yau tunda garin Allah ya waye take zuba idon ganin Kiran daddy amma ko flashing dinshi bata ganiba..gabaki daya she’s disturbed..da yasan yanda fushin nn nashi ke affecting dinta da ya dena yinshi komai girman laifin da zata aikata kuwa…haka suka gama shiri gaba dayansu snn suka fita wurin da zaayi kauyawa din…
Ba laifi ta dan sake daga baya..bayan ta shiga cikin family..taga mutane da dama..wasu ma ta kwashi shekaru bata gansu ba tunda ba kowane yaje bikinta da Taheer ba…amma dukda haka tunaninshi bai bar cikin zuciyarta ba har aka tashi a taron…

Suna komawa masaukinsu dama daki ta shige ta fara rage kayan jikinta snn tayi wanka..tayi sallah snn ta kwanta abunta kmr yanda tayi jiya…tana nn zaune tanata tunane tunane Nafeesa ta shigo dakin…gefen gadon ta zauna snn tace daita”mike Layla mgn nake sonyi dake”…ba musu ta tashi zaune tana fuskantarta… Nafee na kallon yanda jikinta ke a sanyaye tace”inaso ki fadamin mene matsarki..na lura duk a sanyaye kike..bakida lfy ne?..”Layla taji hawaye ya fara zubo mata..a hankali ta girgiza Kai alaman aah… Nafeesa ta sake cewa”to me yake damunki..ko wani abu ya jadaku da dadyn naki ne?..”a hankali Layla ta matso jikinta sosae tareda dora kanta a kafadanta..hawaye na zuba a idonta tace”Mami fushi yakeyi dani tun jiya..ni bansan laifin da nayi ba..duk yau ko kirana baiyi ba”…Nafeesa dan murmushi ta saki..a ranta tace”oh wnn soyayya”…a zahiri Kuma cewa tayi”ke me ya hana ki kirashi tinda kikaga bai kiraba”…Layla tace”Ni banaso in kirashi inji yana hahhade min rai”…wnn karon dariya ta saki sosae kafin ta dago Layla daga jikinta tana share Mata hawaye tace”baa yima namiji haka Layla..da kikaga bai Kira ba ke sai ki dauki waya ki kirashi..idan yace ga laifin da kikayi sai ki bashi hakuri..ba wai kizo ki yita faman kunci kina damun kanki ba..Kuma kema da ummi tace zamu taho dake don me baki ce mata Zaki taho tareda shi ba..nasan hadda wnn dalilin ma yasa yakejin haushin naki tunda baiso ki biyomu ba..dena biyema ummi zakiyi ki tsaya ki kulada mijinki da kyau..tunda kinsan bazata taba dora bukatarshi akan taki ba..bazata taba goyon bayanshi ba koda ace shine mai gsky kuwa..Kuma hakan bawai yana nufin bata son ‘danta bane..no tana sonshi..kawai soyayyan da takemin da Kuma Kara irin nata shiyasa bata taba koyon bayan abinda yakeso..don haka sai ki kiyaye..yanxu ki dauko wayanki ki kirashi..Kuma ki tabbatar kin bashi hakuri kinji na fada maki”…ba musu Layla ta dauko wayanta snn ta fara dialing number dinshi.. ita Kuma Nafee mikewa tayi ta fita…Saida Kiran ya kusa tsinkewa snn yayi picking…maimakon tayi mgn kawai sai ta fashe mai da kuka…Taheer yayi shiru yanajin yanda kukan nata ke ratsawa har cikin heart dinshi…how he wish tana kusa dashi take kukan nn..daya lallasheta yanda ya kamata…ita kuwa kukanta takeyi bilhaqqi don tasan it’s the only thing da zai sauko dashi daga wnn fushin da yakeyi…Taheer ya runtse idanunshi don baison jin sautin kukan nn ko kadan…ganin da gaske ba Dena kukan zatayi ba yace”baby mana..kawai sai ki kirani kisamin kuka sbd kinsan banaso koh”…batace mai kala ba sai kukanta da take cigaba dayi…yasa hannu tareda haigitsa suman kanshi yace”ohk ohk am sorry toh..yanxu ki dena kukan”…nan ma batace komai ba..Kuma bata bar kukan ba…a raunane Taheer yace”baby plss nace am sorry koh..kece fa kikaimin laifi and you are making me apologize.. sbd kinsan banason kukan koh..baki damu daniba koh”…Saida ta share hawayenta snn tace”nidai kayi hakuri toh..bazan Kara ba..kawai ka dena yin fushi”…ya dan lumshe ido hadda sauke ajiyan zuciya kafin yace”alright na dena baby..nima duk a takure nake sbd fushin da nakeyi dake din..amma na dena”..tana murmushi tace”na gode daddyna”… yace”Nima na gode babyna..ynxu fadamin kinyi missing dina ko bakiyi ba”…yana rufe baki tace”I missed you like crazy..jiya ko bacci banyi sosae ba”…Taheer dake jin dadin hiran nasu sosae..ya shafa gemunshi snn ya kwanta tareda dora pillow kan chest dinshi yace”idan akwai abun da yafi missing dinki baby wlh nayi..am about going crazy..ko abinci ban iya ci..haka kawai kin tafi kin barni da rungumar pillow”.. murmushi mai sauti ta saki kafin tace”nima ai pillown nake runguma daddy.. afterall ba dadewa zamuyi ba”…a hankali taji yace”baby”…itama a hankalin tace”yes daddy”…Taheer ya sake narka murya yana sakin wasu nufarfashi yace”I love you”…itama ta maimaita”I love you”…ya sake cewa”I want you”…ba tareda tasan me take cewa ba itama tai kasa da murya snn tace”I want you”…Taheer ya saki wani dariya snn yace”don’t worry my baby..Ina zuwa zan fanshe maki duk na kwanakin da kikayi missing”…Layla ta zaro idanuwa waje jin abunda yake fada..harga Allah batasan meta fada ba sai daga baya…bakinta ta tura gaba tace”Ni ba abunda nake nufi knn ba”…yace”ai kin riga kin gama mgn..don haka ki shirya dama Ina zuwa hotel zamu tafi”…kukan shagwaba ta fara mai tana bubbuga kafanta kan gadon tace”nidai aah wlh..ni Allah bazan yadda ba”…yana smiling yace”Hey relax..wasa nake maki”…haka dai suka cigaba da hira har basu san dare ya tsala ba sbd dadin hira…Saida yaji ta fara bacci snn sukai sallama ba don yaso ba..in don tashi ne baiki su kwana suna hiran ba coz ba karamin dadi take mishi ba..

The following day ya kama Friday..ranan ne Kuma zasuyi dinner..

Around 6 na yamma duk sun kusan gama shirin tafiya dinner din…wnn karon lace suka dinga gaba dayansu iri daya..ummi..umma..Nafee..Ramla..Layla da Kuma Hibba..
Ummi ta mikama Layla Nasreen dake hanunta tace”je ki nemo Ramla duk inda take ki Kai mata ‘yarta..don iskanci shine tasa kafa ta tafi ta bar mana ‘yar duk ta cika mana kunne da ihu”…ba musu Layla ta amsa Nasreen din snn ta fita daga part din nasu..Kai tsaye main hause din ta nufa tana tunanin ta Ina zata fara neman Ramla…a parlor taci karo da wata aunt dinta sai ta tambayeta ko taga Ramla..ta nuna Mata wani daki tana fadin”suna ciki itada amarya tun dazu..kwalliya ake musu”…ba bata lokaci Layla ta nufi dakin da aka nuna Mata…ta tura kofan ta shiga…suna ciki an gama ma amarya make up ana Shirin fara yima Ramlan sai gata ta shigo..Layla ta Mika Mata Nasreen dake ta tsala ihu tace”tun dazu take kuka anty Ramla”..Saida Ramla ta amsheta snn ta juya wurin da amarya Asma’u take…tana murmushi tace”Ya Ma’u bakiga kyan da kikai ba wlh”… Asma’u na dariya tace”thank you. .sai kizo ki zauna ayi maki tunda Allah ya kawoki”…Layla ta zare ido hadi da girgiza Kai tace”Aah Ya Ma’u nagode”… Asma’u tace”wlh baki isaba yarinya”…Layla ta sake bude idanu tace”Ya Ma’u kiyi hakuri dn Allah..daddy baya son make up nasan idan yaga nayi bazaiji dadi ba”…Ramla dake gefe tana feeding Nasreen tace”come on kije ayi maki da Allah..daddyn naki ai ba gani zaiyi ba tunda sai gobe zaizo”…tana rufe baki Asma’u tace”yes kizo kawai ayi maki kafin Ramla ta gama itama sai ayi Mata”…Layla ba don taso ba suka tilasta ta zauna aka fara Mata make up din…basu wani dauki tsawon lokaci sunayi ba tunda very light make up akayi Mata…ita kanta bayan an gama data kalli kanta a mirror sai da ta furta MashaAllah sbd kyan da taga tayi…dinkin jikinta straight gown ne dayabi ya lafe a jikin nata..ya kuma fito da ainihin surarta…mayafinta blue black Wanda yai matching da lace din nata..kasancewarta fara sosae sai colour din ya sake haskata…Daurin kanta Zara Buhari daya matukar yi Mata kyau…an zubo jelan gashinta zuwa tsakanin wuya da kafadanta…she looks so breathtaking…ita kanta mai make up din kallonta kawai takeyi kmr zata hadiyeta…ana gama mata ta sake amsan Nasreen ta rike snn aka yima Ramla.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button