Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Vote and follow me on Wattpad@ummuashraf22 please.luv u guys

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

03

Fuska daukeda murmushi yake kallonta sai kawai ta fada jikinshi ta fashe da kuka,ya rungumeta gam yana shafa gashin kanta yace it’s ok kukan ya isa haka nn,ba tareda ta dagoba tace “am so sorry dady kayi hakuri don Allah”ya sake cewa “it’s ok ynxu fadamin akwai inda ke maki ciwo?ta girgiza Kai alaman aa,ya dagota Yana kallonta yace” baby are u sure ba inda ke maki ciwo ynxu,ummi tacemin kin kwana da zazzabi jiya”ta langabar da kai “tace ai kaine kaketa fushi dani daddy Kuma na baka hakuri kaki hakura”yaja hancinta yana murmushi yace”to ynxu na dena fushin baby,shima zazzabin ya tafi?ta daga Kai tana murmushi “alright”ya fada snn ya mike zuwa toilet dinta,ruwan wanka ya hada mata yasa Mata maclean a brush snn ya fito yace oya shiga kiyo wanka I’ll wait for u here,ta sauka daga gadon tana kokarin cire dan rigan baccin jikinta yace”baby wai bana hanaki cire kaya gaban mutane ba?ta Dan turo baki tace daddy ai ba kowa a dakin naga,it’s only me and u”ya gyara zama yana

kallonta fuska a daure yace “ko keda wane ban yadda ki cire kaya gaban wani ba ko gaban ummi ne”toh daddy”ta fada snn ta nufi toilet,,bayan kaman 6 mins ta fito daure da dan towel dinta iya cinya,ya taso ya kamo hanunta ya zaunar gaban mirror snn ya janyo mata lotion dinta na shafawa ya miko mata karamin towel na goge jiki yana smiling yace “yi sauri ki shirya toh”ba musu ta tsane jikinta snn ta fara shafa lotion din kafin ta gama ya fiddo mata kaya har inners,,ta sa snn ta koma gaban mirror ta shafa powder ta goga eye pencil a idonta sai dan chapette a lips dinta,kallonta kawai yake riga da skirt ne na atampa dinkin ya zauna daidai a jikinta…ta Mika mai dankwali tana murmushi tace “daura min daddy”…baice komaiba ya karba ya zaunar da ita gaban mirror ya shiga daura Mata….dama ya saba daura Mata dankwali… hakanan yana zaune part dinshi ma wataran zatazo tace ya daura mata tun bai iyaba har ya fara koya….ta juyo tana kallonshi da faraa bayan ya gama daurin tace”daurin yayi kyau daddy,thank u”ya kama hanunta suka fita parlor….saida ta gaisa da ummi da Mama hauwa snn yace suje dinning taci abinci….ummi ta kama haba tana kallon hauwa tace”kinga yarinya kmr ba itace ta kusa sume min ba jiya Amma ki ganta ynxu kmr warce zataje gasar kyau sbd uban ya shiga ya lallabota….mama hauwa tayi dariya kawai.

Shi yaja Mata kujera ta zauna snn yayi serving dinta yace “oya yi sauri kici unguwa nakeso muje”tana kallonshi tace “daddy Kai kayi break fast din ne?….shi sai ynxu ma ya tuna rabonshi da abinci tun break fast din jiya….yaja kujera ya zauna itama tayi serving dinshi snn suka faraci.
Parlor suka dawo bayan sun kammala yace baby je dauko hijab dinki zamu fita….da murnarta ta tafi daki ummi na kallonshi tace in Kuma zakuje? shopping zamuje ummi ko zakije kema?ta girgiza Kai tace ni bazan iya wnn gantalin nakuba Taheer…gadai sako zan bada sai ku biya gidan Ramla ku Kai Mata…. zan kirata sai in Mata bayani…..yace “ba damuwa ummi sai ki bama baby ta taho dashi”….to shknn sai Kun dawo”snn ta mike xuwa dakinta…ta dauko saqon tabama Layla kmr yanda yace……a cikin mota ta sameshi ta bude front seat ta shiga itama….gidan Ramla suka fara zuwa bayan yayi parking yace”baby yi sauri ki Kai mata sakon ki fito”tace
Daddy bazaka shiga ciki ba”….ya Dan shafa Kai yace kice ina gaisheta kawai….ba saina shigaba…kafin ma tayi mgn ya bude mata mota yace “oya jeki fito Ina jira….ta sauka ta shiga gidan bayan some mins suka fito tareda Ramlan da katon cikinta don da gani ta kusa haihuwa…. ta karaso side dinshi tana smiling tace yaya Ina wuni”….ya amsada lfy Lou Ramla ya jikinki?…ta danyi murmushi tace “Alhamdulillah ya aiki”….aiki alhamdulillah muna sauri shiyasa ban shigoba…tayi murmushi kawai don tasan dama koba sauri yakeba bai zama lallai ya shigaba….gidan Yaya nafisa data girmeta ma bai shiga balle ita da yake ganinta yar karama….ya zaro kudi daga aljihu ya Mika Mata… tayi godia snn yaja motar suka bar layin….Saida suka hau titi Layla tace”dady Ina zamuje?….ya juya ya kalleta sai yadanyi murmushi yace” zance Zaki rakani”…..ta wara ido hadda gyara zama tace “are u for real dady?don Allah da gske?….kawai taga ya kwashe da dariya sai ta koma gefe tana turo baki….daidai wani boutique na kayan mata taga yayi parking…..ta juyo da sauri tana kallonshi ya daga Mata gira yace”ba nace zamuzo a siya hijabs ba”… dan murmushi kawai tayi…yaa bude mota ya fita itama ta fito suka shiga ciki.

Bangaren Hijabai suka fara nufa…..ya shiga deban mata maka makan Hijabai Yana zubawa cikin basket….. itadai kallonshi kawai take da mamaki ganin uban hijaban da yake diba da alama ko irgawa bayayi….yana gamawa da nan suka nufi wurin dogayen riguna…..nanma ya ringa daukan duk Wanda tai masa kyau Yana tarawa…. itako murmushi kawai take tana kallonshi….dama sun saba indai zasuje shopping to shi zai dauka mata komai Kuma luckily duk abinda ya dauka yanayi Mata kyau and daidai size dinta yake dauka…..daidai da panties da bras nata duk shi yake siya….yasan perfect size nata na koma da komai….bayan ya gama da nn sai shoes da bags….nanma ya Debi son ranshi snn yace” muje wurin cosmetics”….ta riko hanunshi tace” dady ya isa haka please,wancan ma daka siyo ko half dinsu banyi amfani dashiba”….ya zare hanun nashi yace muje dai ko perfumes sai a dauka…..bata sake mgn ba tabi bayanshi….. tasan kota ce aah ma ba yadda zaiyi ba……a ranta sai ayyana irin son da daddyn nata yake mata take……. ita badon an fada Mata bashi ya haifeta ba da bazata taba ganewa ba cox son da yake Mata is beyond expectation shiyasa itama duk duniya babu Wanda takeso kmr shi…..ko iyayenta batajin tana musu son da take mai ko don tafi sabawa dashi ne oho?……haka tasa mai ido ya debi perfumes dinma son ranshi snn suka tafi counter……ya biya kudin through pos snn aka Kai musu kayan mota suka tafi…..basuyi nisaba ya kalleta yace”what do u want to eat?….hadda wani gyara zama tace “dady ice cream nakeso da chocolate”….ya girgiza Kai yace”No Banda wnn fadi wani abun dae”…..ta marairaice dady Allah nidai su nakeso ko kadan ne ka siyamin plss…..ta karashe mgnr da sigar lallashi…..ya kalleta ganin yanda ta wani narke yace”in siya maki ice cream da

chocolate salon in period dinki yazo kisani a gaba kinamin kuka kina cewa zaki mutu koh….i won’t”…..ya karasa yana makale mata kafada kmr yanda takeyi…..tayi murmushi tace dady don Allah ko kadan ka siyamin plss”…..naji zan siya amma ba dayawa ba”…..tace thank u my dady…..daga nn bai sake cewa komaiba har suka isa wani eatry me kyau….bayn an kawo musu abinda sukai order sun faraci kenan ya daga kanshi…..kmr ance ya waiga gefenshi yaga wani saurayi zaune Dan nesa dasu……banda kallon Layla ba abinda yake….ko abincin dake gabanshi bai taba ba yayi concentrating kawai a kanta yana kallo kmr ya samu tv….wani irin bacin rai yaji ya tasomai……ya maida kallonshi ga Layla dake cin abincinta hankali kwance…..duk sai yaji abincinma ya fita a ranshi…..batai aune ba sai gani tayi ya mike ya kama hanunta Yana kokarin janta subar wurin… tace dady what’s wrong…..bakaci abincin bafa…..ko kallonta baiyiba ya cigaba da janta har suka fita a wurin….ya bude mota ya sata ciki snn ya zagaya shima ya shiga yaima motan key suka fita a eatry din….har suka hau titi Layla kallon mamaki take mai….bata San meya bata ranshi ba all of a sudden….cikeda damuwa tace dady don Allah me ya faru?…ya juyo ya kalleta sai yayi Dan murmushi yace”it’s nothing kawai naji banson wurin ne….don’t worry zanyi mana takeaway a wani wurin saimu wuce gida”….batace komaiba har suka isa wani eatry din wnn karon shi kadai ya shiga sai gashi ya fito da ledoji ya zubasu back seat snn ya shiga suka dauki hanyar gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button