Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Taheer na sauka ya bude kofan sai yaga driver ne ya kawo musu breakfast..ya amsa snn ya maida kofan ya rufe…ya ajiya basket din kan dinning snn ya sake haurawa sama…ya bude dakin nata ya sameta kwance tanata faman smiling…ya karasa ciki hanunshi rungume a kirji yace”to tashi muje muyi breakfast”…ba musu ta mike..shi Kuma ya sake kama hanunta suka fita daga dakin..bayan sun isa dinning yaja mata kujera ta zauna shi Kuma ya nufi kitchen don dauko plates da cups da zasuyi amfani dashi…yana daukowa ya dawo..sai ya shiga bude wormers din yana ganin abinda ke ciki…saida ya gama snn ya dawo da idonshi kanta yace”me kikeso a ciki”…maimakon ta amsa mashi sai ta mike tsaye tana duba wormers din daya bubbude…tayi pointing finger dinta kan Wanda ke daukeda fried plantain tace”one”…ta nuna Wanda ke daukeda pepper soup tace”two”…sai tea flask dake daukeda shayi da yaji different ingredients tace”three”…sai Kuma wani small one dake daukeda fried egg shima tace”four”…Taheer dake kallonta yana murmushi yace”is that all”…tana murmushin itama ta daga mai kai alaman yes…ya shiga zuba mata duk abunda ta lissafa din ita Kuma ta koma ta zauna inda take tanata aikin binshi da kallo…Saida ya gama ya tura Mata komai gabanta snn yace”oya Bismillah”…tace mai”thank you”..snn ta fara cin abincin…shima yai serving kanshi snn ya shiga ci a hankali…baya cikakken minti 2 bai dago ya kalleta ba..he don’t know why bai taba gajiya da kallonta…Sun dauki almost 30 mins snn suka gama…yana kallon duk abubuwan da tace zataci ba wanda ta cinye duka…duk Saida ta rage..yai murmushi tareda kada kai..snn ya kwashi duk abubuwanda suka bata yai kitchen dasu…da sauri itama ta mike ta dauki sauran da bai dauka ba tabishi kitchen din dasu…ta ajiesu cikin sink kmr yanda taga ya ajiye sauran…sai taga ya shiga nannade hanun rigarshi…ta kwalo idanu waje tana fadin”daddy me zakayi”…yana ci gaba da nannade hannun nashi yace”wanke wanke Mana”…ta karasa gaban sink din da saurinta tace”Ni zan wanke daddy…ai basa da yawa”…yana girgiza kai yace”no babu abinda zakiyi baby..just sit down and watch kinji…ba sai kinyi komai ba”…ta makale kafada tana cewa”nidai I want to do it daddy..Mami tace kar in yadda in ringa bari kana aiki da kanka..so bakai zakayi wanke wanken nn ba ni zanyi”…Taheer dake kallonta yace”I see…ita tayi miki wnn huduban knn koh”…Layla ta daga Kai da sauri…ya karaso inda take tsaye gaban sink din yana fadin”ok..tunda hakane let’s do it together”…yana rufe baki tace”to nine zanyi sabi sai kanayin dauraya”…ya daga Mata Kai alaman toh…ita Kuma ta dauko morning fresh dake ajiye a wurin ta hada kumfa sosae snn ta fara wanke wanke…tanayi yana daurayewa har suka gama..dayake ba wani abu masu yawa suka bata ba…Saida suka maida komai inda yake snn yaja hanunta suka fita yana ce Mata”now it’s time to look around the house..let’s start from outside”…Layla dai binshi takeyi har suka fita compound din gidan…Yana da girma sosae ga flowers da aka zagaye compound din dasu…car park na daga can gefe wanda 2 of his cars ke Parke a wurin…suka dawo cikin gidan nn ma katon parlor ne sosae..dake daukeda duk wasu abubuwa na more rayuwa…akwai bedroom mai daukeda toilet a nn cikin parlon snn akwai another toilet dake cikin parlor…sai dinnig area shima nada girma..daga gefenshi Kuma kitchen ne mai daukeda store a cikinshi…da suka haura sama nan ma it’s another parlor sai dai shi wnn bai Kai na kasan girma ba…babu abunda babu a ciki tun daga kayan kyale kyale har zuwa furnitures da sauransu…shima yana daukeda mini dinnig daga can karshe…sai kofofi guda biyu dake opposite to each other amma da akwai distance sosae a tsakaninsu…left one din suka shiga…Wanda shine na Layla.. corridor ne mai daukeda two bedrooms kowanne da toilet…shima dayan is the same da natan..Wanda shine na Taheer din…Layla sai baza ido take duk inda suka shiga tana kalla tana smiling har suka gama…nan parlon sama sukai branching ya kwanto ta jikinshi yana shafa jelar gashinta dake yawo tsakanin wuya da bayanta yace”so how do you see the house”…ta sake lafewa a jikinshi snn tace”it’s very beautiful daddy…I like it”…Saida yai kissing gashin nata snn yace”Alhamdulillah you like it”.

Bayan Sati daya…

Cikin satin nan tana ganin zallar soyayya wurin Taheer…dukda ba wani abune ya shiga tsakansu ba amma yanda yake kulawa da ita is something she can’t ignore…ya nuna Mata ita din yakeso and nothing else…wnn dalilin yasa kullum she’s falling for him…his kindness is something da bata taba gani wurin wani ba…gaba daya week din nn sunyishi ne a gida…shi baije clinic ba don ya dauki hutu…itama bataje makaranta ba…sedai almost everyday sunayin karatu dashi a gida…she really loves him that ko kadan bata son matsawa daga kusa dashi sbd yanda yake taking very good care of her…she loves him so much abun har mamaki yake bata…one thing dake dan damunta is yanda taga kmr baida wani feelings a kanta…a yanda taji ana fada in mutum na sonka bazai iya resisting beauty dinka ba…amma it’s like daddy gaba daya ma baida wani feelings a kanta…har yanxu ba abunda ya taba hadasu banda peck da yake yimata wnn kam tana shanshi kmr me…in tayi tunanin ta fadama wani sai taga kmr ist not right..sai ta share batun kawai taci gaba da zuba mai ido.

Shiko Taheer a nashi bangaren yasan there’s a progress tsakaninshi da Layla and kullum cikin godiyan Allah yake… yana kokarin keeping distance dinshi sbd baison karya promise din da ya daukan Mata…but Allah ya sani he’s disturbed…yana cikin damuwa..these days ko baccin kirki bai samu…the moment yajita jikinshi yake loosing duk wani strength nashi…he really wants to have her amma yana tausayinta..and yana so yayi keeping promise dinshi…yasan a yanda yakejin Layla cikin zuciya da gangar jikinshi.. duk rananda ta shiga hanunshi ba karamin wahala zai bata ba…wnn ma yana daga cikin dalilinda yasa yake kokarin danne feelings dinshi…he believe komai nada lokaci and nasu time din na nan zuwa..so he won’t rush..he’s going to wait for the perfect time to come.

Yau ya kama Sunday shi da ita gaba daya suna gida…ita batada lectures yau…shi Kuma evening duty yake..so sai 2 zai bar gidan…Yana zaune parlon kasa yana wasu aiyuka cikin laptop dinshi…Layla ta sauko da gudu tana fadin”daddy nidai ka kaini in gaida su ummi yau plss”…Taheer ya dago idonshi yana kallonta…tana sanyeda dan riganta iya guiwa..gashinta da har yanxu ba kitso yana daure da ribbon a tsakiyar kan nata…saida ya saki smile snn ya dauke system dake kan laps dinshi ya ajiye gefe…yai balancing kan kujeran sosae yana dubanta da idanunshi da suka kankance yace Mata”come here”…ba musu ta karasa saukowa daga stairs din ta karaso parlon..zata zauna kusa dashi ya kamata ya zaunar kan laps dinshi…ya zagaye kugunta da hannayenshi yace”me kike cewa”…ta dan juya tana kallonshi baki a tunzure tace”I said inaso ka kaini in gaida su ummi yau..tunda evening zakai sai ka barni a can…in ka dawo daga clinic din sai ka biyo ka daukeni”…Taheer yasa hannu yana sake matseta a jikinshi yace”banji me kikace bafa baby..say it again”…wnn karon harara ta watsa mai tana fadin”nasan ka jini daddy…nidai don Allah ka kaini kaji”….Saida ya juyo da face dinta yai cupping da hannayenshi…yana kallon tsakiyar idonta murya can kasa yace”ni bazan iya driving ba baby…banida lfy”…ya karasa mgnr tareda kwantar da kanshi a chest dinta…Layla ta dan zaro idanu tana kokarin dauke kan nashi tace”to..to..na hakura daddy…ka sakeni sai in dauko maka magani”…cikin zuciyarshi yace”my medicine is only you”…sai Kuma a fili yace Mata”ni ba maganin da zansha…kawai idan Zaki iya driving din muje ki kaimu”…ta shiga girgiza kai da sauri..har yanxu kokari take ta dauke kanshi dake jikinta amma kmr magnet yaki tashi…saita dena kokawan da takeyi kawai tareda lumshe eyes dinta…shiko Taheer he’s far gone…lokaci daya mood dinshi ya canxa…gudun kar yai loosing control dinshi sai ya mike daga jikin nata…ya shiga kallonta yana kokarin kakalo murmushi yace Mata”bari in sake wanka idan naji zan iya sai muje”…bai jira cewarta ba ya mike tareda haurawa sama…Layla Kam binshi tayi da ido ganin yanda yake tafiya da kyar..da alama yanajin jiki sosae…mikewa tayi itama tareda haurawa saman…tayi hanyar dakinshi zata shiga wayanta dake hanunta ya fara ringing…sai ta fasa shiga snn ta koma zuwa dakinta…Saida ta rufe kofa snn tayi picking tareda fadin”babe how far”…a daya bangaren Hanna tace”ke zaa tambaya how fa ai amarya…ya gida ya amarci”…Layla na girgiza kai tace”Allah ya shiryeki”…da sauri Hanna tace”Ameen…amma bani lbri..ya rayuwar auren take..I mean kina jin dadinshi kuwa”….wani kasaitaccen murmushi Layla ta saki data tuna yanda Taheer ke mata cikin sati dayan nn…ta tabbata da haka kowane miji kema matarshi da baa samu marital problems ba…Saida Hanna ta sake cewa”hello”…snn tace”it’s really amazing…ban taba tunanin haka auren yake ba”…Hanna ta kwashe da dariya tana fadin”kice daddy ba daga nn ba…ko dayake ai dama daga ganinshi Majnoon ne…kinsan Layla da Majnoon fa kan soyayya suka mutu”…Layla dake sauraran shakiyancin Hanna tace”malama spare me wnn surutun naki…ya school”…Hanna ta danja tsaki tace”school wahala wlh Jakada..nima jiya ban samu shiga ba sbd banida lfy”…Layla ta dan zaro idanu snn tace”umh kodai kodai”…”ke ba wani kodai kodai wlh…fever ne kawai”… cewar Hanna knn…itakam Layla dariya ta saki kafin tace”ban yadda dakeba wlh…dama tun tuni na fara noticing changes a jikinki..so ba wani fever morning sickness kawai kikeyi hajiyata”…sai ta Kara sakin wani dariyan…daidai lokacin Taheer ya turo kofar dakin ya shigo…tai saurin cewa Hanna”babe Ina zuwa..zan kiraki ltr”…tanajin Hanna na fadin”Majnoon ya iso knn”…itadai ta kashe wayarta tana fatan Allah sa baiji abunda ta fada ba…ta daga ido tana kallonshi sai taga ya dauke kanshi gefe… muryanshi can kasa yace”ko kin fasa zuwa ne”…sai ta mike tana fadin”naga bakada lfy ne daddy…mu barshi kawai duk ka samu lfy sai muje”…tana rufe bakinta yace”don’t worry i can manage..kiyi sauri ki shirya zan jiraki downstairs”…Kai kawai ta iya daga mai…shi Kuma ya juya ya fita…ta bishi da kallo duk sai taji tausayinshi ya kamata..to ciwon mene ke damunshi haka..zata cigaba da mai addu’a Allah ya bashi lfy.(ji uwar gulma????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button