Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Ramla bata haihuba sai wurin 2 na dare…ummi taso kiranshi a Daren Amma tace Bari zuwa Safiya tasan yanxu bacci yakeyi…

Washegari…

Bayan ya dawo daga masallaci ya dauki wayanshi ya shiga Kiran ummi…nan take sanar dashi good news ta sauka lfy..snn an samu baby girl…a lokacin yace gashi nn zuwa…ko wanka bai tsaya yi ba yasa kaya kawai ya fita…lokacin da yaje an gama musu komai sallama kawai suke jira…da kanshi yaje office din doctor ya amso sallama snn yazo yace an sallamesu…mijinta dake wurin da wata aunt dinshi sukace zasu tafi da ita gida zasu kula da ita a can tunda haihuwan fari ne…ummi ta roki alfarman a barta ta tafi da ita…haka suka daukota suka nufo gida mai gidanta Kuma yayi alkawarin zai biyosu da kayanta Dana baby.
Wannan knn

Mai jego da baby na samun kulawa sosae wurin ummi…umma itama Saida akai kwana ukku da haihuwa tazo…kusan kullum sai anyi rigima da Layla kan daukan baby amma ummi Sam zatace baza’a bata ba wai ba wani hankali gareta ba????

Yau ma kmr kullum umma nayiwa jaririyar wanka…ummi Kuma na gefe tana ninke kayan babyn da aka wanke…for the second time Layla ta sake cewa”kinji ummi Dan Allah ki bani in dauketa ko na minti 5 ne”…ummi ba tareda ta kalleta ba tace”sai kiyi Kuma ai yarinya…ba mahaukaciya nakeba da zan dauki yarinya sabon haihuwa in baki kije ki wurgar Mata da ‘ya”…yanxu ummi nice zakice bazan iya daukan baby ba…shekara na 17 amma ace bazan iya daukan jariri ba”..Layla ta fada tana turo baki…ummi Kam banza Tai da ita taci gaba da abinda take…umma data gama yima jaririyar wanka ta mikama ummi tana fadin”ai tsakaninki da Layla sai Allah Yaya…yanxu mutum na shiga Zaku bashi kunya..da nace dai kiyi hakuri ki barta ta dauketa mana”….ummi ta tabe baki tace”ai sai kuyi”snn ta amsa yarinyan ta sa a bayanta ta goya…Layla sai ta fara hawaye(abunku da ta6ararriya)…ita kanta Ramla dake zaune kan gado tana sauraren su dariya suka bata…ta juya zata fita sai ga Taheer ya shigo dakin…sai ta fasan fitan taje ta fada jikinshi tana kuka….yasa duka hannayenshi ya rungumeta Yana shafa bayanta idonshi a kan Ramla yace”waya tabamin ita?…ba tareda tayi mgn ba ta nuna ummi da hanunta tana kokarin boye dariyan dake son kufce mata….ya wani rausayar da kai a shgwabe yace”ummi mana…laifin me tayi don Allah…you could’ve told me…ni nasan yanda zanyi daita…banson kukan nn nata wlh”….ummi ta zabga mai harara tace”sannu shugaban marasa kunya…ai ba tsoronku na faraji ba da zan dauki jaririya sabon haihuwa in ba Layla ta dauka…haka kawai taje ta doka musu yarinya da qasa tasa mukhtar ya kullacemu”…Taheer bai sake mgn ba Saida ya zauna kan kujera ya zaunar da ita kusa dashi still tana jikinshi…wnn karon maimakon ummi sai ya maida kallonshi ga umma yace”umma a bata ta dauka mana pls…rikewa fa kawai zatayi ba wani wurin zataje da itaba…umma na dariya tace”sha’anin Yaya ne sai Allah Taheer…ba yanda banyi ba ta bata yarinyan ta dauka ko a zaune ne amma taki….Ummi ta mike zata bar dakin tace”sai kuyi tayi ai…kema Aisha na fuskanci har yanxu akwai sauran kuruciya tareda ke…in ba hakaba Ina Zaki goyi bayan a bama ta6ararriyar yarinyar nn jaririya ta dauka…Laylan da ko jikinta ma da kyar take daukanshi tsabar son jiki…wnn duk ya gama ta6ar6arata wlh(tayi pointing Taheer da hannunta)…Allah dai ya fiddamu kunya a wajen yaron nn Usman… InshaAllah bazaiga laifina ba saidai yayita ganin na uban…Allah ya shiryeku….tana gama fadan haka ta fita a dakin abunta….umma ma ta mike tareda kwashe kayan da tayima baby wanka duk ta kaisu inda ya dace snn ta fice tana dariya….Taheer yakai dubanshi ga Layla da har yanxu ke kuka a jikinshi…cikin sigan lallashi yace”kukan ya isa haka mana baby…kar ki damu ni zan dauki yarinyan da kaina in baki ki dauka so ki dena wnn kukan kinsan banaso…Saida ta share hawayen snn ta dago tana kallonshi tace”daddy wai ummi fa har yanxu kallon kid takemun…ya zaai ace bazan iya daukan jaririya ba sai kace mahaukaciya…Taheer yai murmushi yace”don’t mind her tanaso ta saki kuka ne kawai…snn tazo tana ce maki ta6ararriya….ki dena biye Mata kinji…ta daga mai Kai a hankali…ya mike itama ya mikar da ita tsaye suka fita daga dakin…Ramla ta bisu da kallo kawai zuciyarta na Mata sake sake.

Ana gobe suna mutanen porthacourt suka iso…nan gida ya sake kacamewa…da yawa daga family dinsu ma na kano duk sun iso.
Ranar suna yarinya taci suna Nasreen…mijinta yayi rawar gani sosae hakama ‘yan uwanta dana mijin nata.

Bayan kwana biyu…

Zuwa yanzu mutane duk sun koma…Nafeesa kawai ya rage da yaranta suma Kuma gobe zasu tafi…mama hauwa da umma na kitchen sunata girke girke don babban bako zasuyi daga Dutse…Usman ne zaizo ganin amaryar sa????tunda Taheer yaji lbrin zuwan nasa dama yasa a ranshi yau duk bazai zauna a gidan ba…tun safe ya fita ko gaisawa da iyayen baiyiba…ummi sai mita take wai sirirkinsa zaizo kuma ya kama hanya ya fice(Niko nace ummi ai ba sirikinshi bane rival dinshi ne????).
Nafeesa da mai gidanta wato mahaifin Layla duk sunyi farin ciki da jin batun Usman din da Layla…sedai Allah ya tabbatar da alkhairi.

4:00pm daidai Taheer ya shigo cikin gidan…sakamakon kiranda ummi ta ringa rafka mai kan yazo su gaisa da Usman kafin ya wuce…Kai tsaye part dinshi ya wuce…mamaki ya kamashi ganin kofar parlonshi a bude…kodai a bude ya tafi ya barta?…bai sake kawo komai a ranshi ba ya shiga ciki…abinda ya gani ya sashi sandarewa a nan inda yake…tareda zura musu ido kmr ba gobe….Layla ce zaune kan one seater…tana sanye cikin dogon riga na material…bata daura dankwali a kanta ba sai mayafi data Dora a kan…Usman Kuma na zaune gefenta hanunshi rikeda glass cup mai daukeda drink yana kokarin kaiwa bakinta….zuciyarshi yaji tayi wani bugu da karfi…sai Kuma ta koma ta cunkushe a wuri daya…yanda zuciyarshi ta cunkushe hakama ranshi gaba daya yaji ya cunkushe…yanata kokarin ya bude baki yai mgn amma ya kasa….he never thought haka akeji idan akaga masoyi tareda wani sai yanxu….zuciyarshi zafi takemai yanajin tamkar ya karasa ya shake Usman har sai ya Dena numfashi…how dare he trying to feed her…how dare he”

Da sauri Usman yaja baya tareda sukuyar da kanshi kasa….ba karamin kunya yaji ba…ita Kuma Layla mikewa tayi zuwa gareshi tana mai murmushinta me kyau tace”welcome back my daddy….tun dazu ummi ke nemanka….Saida ya tattaro sauran jaruntan daya rage mai kaff snn Yana kakalo murmushi yace”actually…I…I was occupied with work ne a office so bansan time ya wuce haka ba….Usman ya taso daga inda yake yazo ya durkusha a gabanshi…still idonshi qasa yace”barka da yamma daddy…fatan mun sameku lfy”…a hankali yace lfy qlou Usman ya su alhaji da hajiya?….ya amsa da suna nn lfy..duk suna gaisheku…..”MashaAllah”kawai ya fada snn ya juya ya fita daga dakin kmr ana tunkudashi….part din ummi ya nufa don yasan ko ya bar gidan ma ummi ba Dena kiranshi zatayi ba…duk suna zaune parlor da gudu su Al’ameen sukaje suka rungumeshi suna mai oyoyo….ya hadasu ya rungume gaba daya a jikinshi yanajin yanda har yanxu heart beat dinshi bai koma normal ba.
Ya karasa parlon ya nemi wuri ya zauna gefen nafeesa ya jingina jikin kujeran tareda lumshe idanunshi….bai San tsautsayin daya kaishi part din nashi ba yasan for sure abunda ya gani bazai taba gogewa cikin zuciyarshi ba.
Nafeesa na kallonshi cikeda tsokana tace”my big barchelor bro how far”…ya bude ido yana hararanta snn yai kokarin daidaita kanshi yace”yarinyar nn kin rainani wlh….kika sake cemin barchelor saina Kira mijinki nace mai ya Kara aure dama ke kin fara zama cus”….Nafeesa ta zaro ido tana dariya tace”ai ba tsoron kishiya nake ba…don Allah ka kirashi ka fada mai din kaga idan bai gwasaleka ba”…ya girgiza Kai kawai snn ya sake lumshe idon tareda komawa yai luff a jikin kujeran…nafeesa ta bishi da kallo snn a nutse ta fara mgn”let’s keep joke apart bro Allah ya kamata kasan me kake ciki…it’s high time u settled down with your own family….Ina mgnr Wanda ummi ta fadamin??da sauri ummi tace”kema dai kya fada mai nafisa maybe ke yaji naki mgn….tuntuni nace zanje kano in sanar da kawunshi yazo kan mgnr auren Amma kememe Dan nn ya hanani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button