Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yinin ranar mutane sukaita zuwa dubiya sosae don baa sallamesu ba…Taheer da kanshi yace su bari zuwa gobe idan yaga yanayin jikinta dana babyn ba matsala sai su tafi…haka akaita fama da Layla wajen bama baby nono..duk ta kama nonon sai tasa kuka wai ita zafi takeji…Saida umma ta kusan dukanta snn aka samu tayi shiru…
Abbansu ya Kira ta wayan ummi yayi barka snn ya hadata dasu Al’ameen suma sun dade suna hira hadda kira video call aka nuna musu babyn suka gani…Taheer kam bayan anyima baby wanka an shiryata tsaf cikin kayanta yayita snapping dinta pictures kala kala hadda su video sai kace mace…haka yabi almost duk contacts dinshi yayi musu sending yana cewa Allah ya albarkaceshi da samun diya mace…Friedns dinshi da yawa sunzo sunga baby a ranan cikinsu hadda Yusuf… Alhamdulillah Kuma daga baby har mamanta suna cikin koshin lfy..

Idan akwai Wanda sukeson zuwa suna suyi mgn da wuri sbd asasu cikin list????????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

53

Not Edited..

Washegari da safe aka sallamesu bayan an tabbatar da baby da mamanta suna cikin koshin lfy…Taheer ya kwashesu sukayi gida…suna zuwa ummi tasa mama hauwa ta dora ruwan zafi wai zasuyi wankan jego…ita Kuma umma ta karba babyn itama ta fara yi Mata wanka…

Ruwa na tafasa ummi ta hada ruwan wanka ta kaishi bathroom din dakinta…Layla da ido ya raina fata taji kmr ta kurma ihu don ba son wankan nn take ba…haka ummi tasata agaba suka shiga bayi…ana fara zuba ruwan a jikinta ta saki wani razanannen ihu da har Taheer dake part dinshi sai da ya jiyo ihun…ya fito daga wanka da sauri ko gama wankan baiyi ba ya dauraye jikinshi ya fito daure da towel..jallabiya kadai ya iya zurawa snn ya fita daga part din nashi da sauri…yana shiga nasu part din yaci karo da Mama hauwa a parlor…da sauri yace Mata”lfy mama hauwa nakejin kukan baby..tana Ina?..”Saida hauwa tayi dariya snn tace”ba wani wlh..wanka ne kawai ake Mata shine take wnn kukan”…Taheer ya zare idanu kafin yace”wane irin wanka Kuma mama hauwa”…a takaice tace mishi”wankan jego”…bai sake tsayawa yin mgn da itaba ya nufi dakin ummi inda nan ne yakejiyo sautin kukan nata…umma na zaune dakin tanayima baby wanka…Taheer ko bi ta kansu baiyi ba kawai ya karasa tareda tura kofan bayin…Saida ya shiga ciki sosae snn kmr zaiyi kuka yace”ummi dn Allah kiyi hakuri a bar wankan nn haka tunda bataso plss…tun daga part dina fa na jiyo kukanta”…a fusace ummi ta dago hannunta rikeda towel da takema Layla wanka dashi tace”fita daga bayin nn tun kafin inci ubanka wlh..wane irin iskanci ne wnn inama yarinya wanka kawai zaka fado mana cikin bayi..wane irin rashin kunya ne wnn”…Taheer ya sake rausaya kanshi yana kallon Layla dake sheshshekan kuka a hankali yace”ummi dan girman Allah kiyi hakuri ki bar wankan nn haka..kinga fa dinki ne a jikinta and wnn ihun da takeyi yana iya sawa dinkin ya warware Kuma baa son haka..nidai dn Allah kiyi hakuri ki kyaleta ko wani maganin ne sai a nemo a bata a madadin wankan jeg”…kafin ya karasa mgnr ummi ta jefeshi da wani mini bucket dake ajiye kusada Layla…tana huci tace”bazaka fita ba koh”…sum sum ya juya tareda ficewa daga bathroom din..duk ranshi a jagule…cikin dakin ya koma ya samu wuri ya zauna Yana kallon umma data gama yima babyn wanka tana Sanya Mata kaya yace”umma kiyima ummi mgn plss…wankan nn fa ba dole ne sai anyishi ba…tunda bataso sai a rabu da ita..ni bazan iya gani tana Shan wahala hakaba dn Umma kiyi wani abu kinji…kinga dai wahalan da tasha umma bai kamata Kuma a sake bata wani wahalan ba yanxu”…umma Kam dariya ta saki sosae don maganganun nashi ba karamin dariya suka bata ba…dama tunda taga ya shiga bayin tasan abinda zai biyo baya knn…Saida ta gama shirya baby ta Mika mashi ita ya amsa snn ta shiga kwashe kayan da tayi amfai dasu..duk ta maidasu inda ya dace…tana kokarin fita daga dakin Taheer yace”umma bakice komai bafa”…sai juyo tareda komawa ta zauna kusa dashi…har yanxu face dinta da murmushi tace mishi”ai ban San me zance maka bane Taheer…bazan iya da rigiman nn naka ba wlh”…tana rufe baki yace”umma kawai fa mgn zakiyi da ummi kice a hakura a wankan jegon tunda baby bataso..nasan idan ke kika fada zata saurareki”…umma na dubanshi tace”nidai bazanyi mgn kan a fasa yi Mata wankan jego ba gsky..sbd wankan ba karamin taimaka Mata zaiyi ba..Kuma ai ba ruwan zafi sosae ake Mata wankan dashi ba..sai da aka sirkashi sosae..ai munsan tanada dinkin a jikinta don haka bazaayi sakacin da har dinkin zai warware ba…so ka kwantar da hankalinka”…Taheer ya bude baki zai sake yin mgn umma tace”ya isa da Allah..kar Kuma in sakejin kayi mgn kan wankan jego..idan ba hakaba kuma zakaga bacin raina wlh..tunda nema kake ka maida kanka lusari sai abinda mace takeso zakayi Mata”…bata jira ko zaiyi mgn ta juya tareda ficewa daga dakin..shi Kuma ya sauke ajiyar zuciya cikin ranshi yasan tunda ta fadi haka to da gaske takeyi..shi bawai wankan ne baiso na..wnn kukan da takeyi ne baisonji…bayason abinda zai daga Mata hankali kwata kwata…ya maida idanu kan ‘yarshi daketa wutsil wutsil da kafafu tana yatsine fuska kmr zata fara kuka…bai San lokacinda ya saki murmushi tareda kissing goshin yarinyar ba…”Hello Sweetheart”..ya fada kmr yana mgn da babba…ya dagota ya mannata da chest dinshi..sai ya shiga sauke ajiyan zuciya a jere a jere..wato Allah ne kadai yasan irin soyayyan dake tsakanin ‘da da iyayenshi…bai taba tunanin haka iyaye keji akan ‘ya’yansu ba…wani irin pure love ne tsakanin iyaye da ‘ya’ya…duk yanda zaa kaiga yima mutum bayani bazai taba ganewa ba har rananda ya haifi nashi na kanshi…ubangiji da kanshi yace ‘ya’ya sanyin idaniya ne ga iyayensu…babu shakka wnn mgn haka take don yanda yakejin son yarinyar nn is beyond expectation…shiyasa ubangiji yace yanajin kunyar duk wanda ya mutu bai taba haihuwa ba…sbd bazai taba experiencing wnn bond dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye ba(Allah ka azurtamu da zuri’a dayyiba????????)
Yana nn rungume da ita su ummi suka fito daga bathroom…da mamaki sosae ummin ke binshi da kallo don bata yi zaton Yana dakin ba…ta karasa inda yake kawai sai ji yayi ta karbe babyn dake hannunshi…ya bude idonshi da sauri sai Kuma ya sauke ajiyar zuciya ganin ummi ce ta karbeta…a fuska a daure ummi ta nuna mishi kofa tace”tashi ka bar min daki..kuma kar ka kuskura ka sake tako kafa ka shigo min nn don ranka zaiyi mummunan baci wlh”…baice Mata komai ba ya mike tareda kama towel dinshi dake cikin jallabiya ya rikeshi gam..snn ya fita daga dakin..shi Sam ya manta Ashe ko wankan bai gamaba ya fito…ya saki murmushi Yana shafa lallausan gashin kanshi daya tuno da yarinyarshi…kallonta ne duk ya mantar dashi damuwan da ya shiga…a hankali ya furta”I love you sweetheart..Allah ya raya min ke ya maki Albarka”…

Yinin yau ma dai sunata Shan baki yan barka…Ramla ma tun safe tazo gidan…da yawa daga cikin Friedns din ummi dana umma Wanda suke kusa duk sunzo barka suma…Haka iyalan Yusuf ma yau yini sukayi a gidan hadda yaransu.

Bayan kwana uku…

Yau kwana hudu cif da haihuwar Layla…yau ne Kuma Nafeesa da Mijinta Awwal suka zo ganin baby..shi zai koma yau sbd yara itakuma Nafee sai bayan suna zata tafi…
Tun dazu Taheer ya tafi airport daukosu…bai dade da zuwa ba jirginsu yayi landing…suna fitowa suka hangoshi don haka suka nufi inda yake..tun daga gaisuwa Taheer sai ya kasa sakewa dasu…bai san meyasa yakejin wani hadadden kunyarsu ba yanxu…duk sai yajishi a takure…suma da suka ga kmr nauyinsu yakeji sai suka barshi…a haka suke tafe in silence har suka karasa gida… Taheer ya dauki uban kayan da Nafee ta zo dasu ya shiga ciki…suma duk cikin suka shiga…sun samu su ummi a parlor..ita Kuma Layla na daki don har yanxu ko daman fitowa parlor ummi bata bata ba wai don jikinta ya dahu…wai tanada danyen jiki bazata na fitowa tanashan iska sosae ba…a parlon suka zauna bayan sun gaisa umma ta kwance babyn dake goye a bayanta ta fara mikama Awwal…cikeda farin ciki sosae ya amsa yarinyar hannu bibbiyu…ya Kira mata ido yana kallonta with so much love…yayi Mata addu’a snn ya mikama Nafee da takeji kmr ta kwace babyn daga hanunshi sbd kaguwan da tayi ta dauketa…Yana murmushi yace”ubangiji Allah ya rayata..yayi mata albarka..Allah yasa cikon addini ce”…gabaki dayansu suka hada baki wajen cewa Ameeenn….ita ma Nafee ido ta kurama babyn sosae tana kallonta…tun a kallon farko ta gano tsantsar kamannin da takeyi da babanta…bata dauko komai na Layla ba sai haskenta…hakan yasan babyn take kyakyakyawa da ita tubarakallah…Saida tayi Mata kiss itama ta Mata addu’a snn tace”kullum su Al’ameen sai sunyi zancen yarinyar nn…kullum sai ance anaso azo aga babyn Ya Layla da daddy”…sukasa dariya…Awwal ne ya tambayi Layla…ummi ta mike tana cewa”Bari in kirata..kasan mai danyen jiki Saida zaman daki”…daga haka ta shiga dakinta jimm kadan sai gata ta fito hanunta rikeda na Layla dake sanye cikin dogon riga na atampa…suka karaso parlon ummi ta zaunar da ita kusa da ita snn itama ta zauna…Layla dake cikeda farin cikin ganin iyayenta tace”Abba sannunku da zuwa..Ina yini”..Yana murmushi yace”lfy qlou Layla..ya jikin naki”..tace”naji sauki Abba..Ina su Ramadhan”…yace”su Ramadhan na gida Layla sbd school..amma ana gobe suna zasuzo InshaAllah dasu zaayi suna”…tana murmushi tace”Allah ya kaimu”…sai ta kalli Nafee itama ta gaisheta…bayan sun gama gaisawan ummi na duban tace”to Taheer sai muji wanne suna kakeson sama yarinyar..idan Kuma ka bamu zabi sai mu zaba Mata”…Taheer dake murmushi at thesame time Yana shafa kanshi yace”dama yau nakeso inyi Mata huduba ummi..a kawota inyi yanxu sai in fada maku sunan dana sa Mata”…ummi tace”aah ka fara fada Mana sunan dai muji koh..duk nn waye bakinka..ai duk mune sbd haka ka fada munaji”…shiru Taheer yayi yana kallonta don Allah ya sani yafiso sai yayi Mata huduba snn yace sunanta wance…Awwal ne yace”Ummi tunda yace yanada zabi a barshi ya sa Mata duk sunan da yakeso…ai shine mahaifinta”…yana gama mgn ya kalli Nafee dake rikeda yarinyar har yanxu yace Mata”bashi ita yayi Mata huduba”…ba musu Nafee ta mike tareda mikamai yarinyan…Taheer ya amsheta da hannaye biyu…Saida ya fara yi Mata Kiran sallah a kunnenta duk biyun snn yayi Mata huduba da sunan daya dade da zabar Mata…su ummi duk suna kallonshi…bayan ya gama ya dago tareda mikama Nafee Yarinyar…face dinshi daukeda murmushi yace”nayi Mata huduba da sunan Ummata..Aisha..”gaba dayansu tsitt sukai suna kallon kallo don ba Wanda ya kawo sunan da zai sa Mata knn…shi Kuma cikeda tabbatarwa yace”yeah..she means the world to me..na tabbata ba don umma ba aurena da baby bazai taba yiwuwa ba..dama tun tana ciki nasama raina indai mace aka Haifa sunan umma ne da ita”…yana rufe baki umma da hawayen farin ciki ya wanke Mata fuska..ta bude mai hannayenta tana cewa”zo nan”..ba musu Taheer ya mike tareda fadawa jikinta…ta rungumeshi gam tana shafa kanshi tace”thank you so much son..I really appreciate..Allah ya maka albarka kaji”…Taheer na gyada Kai yace”Ameen Ummata..I love you so much”…umma tace”I love you more my son..I love you”…duk kallonsu kawai sukeyi kowa yana dariya…bayan sunyi breaking hug din ummi ma tace”Nima zo indan rungumeka ba don halinka ba”.. da sauri Taheer ya fada jikinta itama tayi hugging nashi gam..tana bubbuga bayanshi tace”Allah ya maka albarka..Allah Kuma ya raya mai sunan kanwata..Allah ya raya Aisha”…Saida ya dago daga jikinta snn yace”Ameen Ummi..Nawal…Nawal nakeso ana kiranta dashi”…ummi ta kama haba tace”Oh Taheer yanxu ko nickname din bazaka bari uwarta ta zabar Mata ba”…yace”ummi nasan itama bazata qi zabina ba..and Nawal mean gift shiyasa nakeso ana kiranta dashi tunda she’s a gift from Allah”…gabaki dayansu da suke cikin parlon ba Wanda baiyi murna da wnn suna da aka sama yarinya ba.. especially Nafeesa da takejin kmr anyi Mata albishir da aljannah…bata da burin da ya wuce taga zumunchinsu ya Kara karfi ta dalilin wnn hadin Kuma Alhamdulillah Yana Karfi din….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button