Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan sun isa gida..yana gama parking ta shiga kokarin bude motan zata fita…Taheer yasa lock tareda komawa yai relaxing kan kujeran da yake.. idanunshi na kanta yace”ai ban sallameki ba”…Layla ta dena kokarin bude motan da take tareda komawa ta zauna itama…yadan daure face dinshi yace”baby banason kina zuwa makaranta a haka wlh..banaso”…Layla ta bude idonta sosae tace”hijab dina ya kai har qasa fa daddy”…tana rufe baki yace”to kuma fuskanki da kike yawo dashi a haka kowa na kalla fa..bakisan yanda kika koma ba koh”…Layla ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin tace”shknn..daga gobe zan fara sa niqab idan zan fita”…Taheer ya saki smile yace”good girl..May Allah bless you”..tace”Ameen Ameen..yanzu xn iya tafiya”…Saida ya cire lock din dayasa snn yace”yes ma’am..ki ajiye wayanki kusa..zan Kira”..”toh”tace dashi snn ta bude motar ta fita..shi Kuma ya bita da kallo yanajin kmr ya bita cikin gidan..he can’t get enough of her at all..son da yake mata is different.

Bangaren Hajia Anty Sameera kuwa..tayi bincike kmr yanda tace zatayi..an Kuma tabbatar Mata da Taheer ba kowa ya aura ba face Layla..wnn yarinyar me kama da aljanu..yarinyar da taji ta tsaneta dama from d beginning..ranar taci kuka ta godema Allah..don takaicin wai duk fadin duniya Taheer ya rasa wa zai aura sai wnn ‘yar..wnn abar da ko ita kanta ta kusa haifanta…an tabbatar mata da yarinyan Base University take..snn bata tare gidan Taheer ba har kawo yanxu..wnn dalilin yasa ta kudiri aniyar shiga tsakaninsu nor matter what.
Wannan kenan..

Bayan sati guda…

Zuwa yanxu abubuwa kadan ne basu kammala ba na shirye shiryen biki…Nafisa ma zata taho cikin satin nn..su kuma yaran sai gab da biki zasuzo tareda mahaifinsu.

A bangaren ummi ta dage kan lallai saita koyama Layla girki..duk ta dawo daga school da wuri dama zaa turata kitchen ace sai tayi girki..

Yauma tun safe ummi ta turata kitchen wai Mama hawwa ta koya mata yanda zatayi tuwon shinkafa da egusi soup…a karo na uku Layla ta sake fitowa daga kitchen hanunta rikeda ludayin miya tace”ummi don girman Allah kiyi hakuri..wlh karatu nakesonyi”..ummi tai Mata banza tana cigaba da ware cards din biki da aka kawo Mata..Layla har ta juya zata koma kitchen din taji Taheer yayi sallama..sai ta fasa komawan ta tsaya…shi Kuma ya karasa kusada umma ya zauna snn yace”umma gani”…ta miko mai cards din dake gefenta tana cewa”invitation cards ne dama aka kawo daxu..shine nace bari in baka ko zakayi inviting friends dinka..wnn na dinner ne..dayan Kuma na mother’s Eve..kamu na Mata ne kawai so ba sai an baka ba”…Taheer ya rike cards din da take miko mai a hanunshi..idanunshi kan Layla da har yanxu ke tsaye da ludayi a hannu yace”lfy kuwa”..da sauri ummi ta dago tana dubanshi tace”lfy Mana..dambe ka samemu munayi da zata tambayemu ko lfy”…still idanunshi a kan Layla yace”baby me kikeyi a nan wurin”..wnn karon a kufule ummi tace”Kai wai Ina ruwanka da ita ne..girki nasata tayi..ko kana nufin haka zaa dauketa a kaita gidan nata ba tareda ta iya komai ba”…ummi na rufe baki yace”ummi indai don ni zaa koya mata girkin wlh na yafe…idan lokacin da zata koya yayi zata koya ai”…ummi na girgiza Kai tace”kasan wani abu Taheer..yarinyar nn dama da an likama wani ya aureta billahillazhi an cuceshi..yarinyar da bata iya komai ba sai shegen shagwaba kmr jaririya..amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane..sai ya manna maka kaje kayita fama da ita..dama ai ba wani ne ya lalata ba daya wuce kai..don haka ba Wanda ya kamata ya kwasheta sai kai din..sai kaje kaji idan dadi ne auran macen da bata iya girki ba”..Taheer da mgnr ummin ya bashi dariya..sai ya saki murmushi kawai yana cewa”eh naji koma menene ummi..ni ba girkinta na auraba..ita na aura”…ummi dai bata sake tanka shi ba..Yana duban Layla yace”jeki ajiye wnn abun a kitchen kije kici gaba da karatunki”…aiko da sauri ta koma kitchen din ta ajiye snn ta sake fitowa ta shige dakinta..umma dake sauraron draman nasu tana dariya tace”wai Kai haka ake rayuwa ne..ace duk wani abu daya kamata bazaka bari yarinyar nn ta koya ba..to idan bata iya girki ba kaine zakana zama kanayi muku girkin ko kuwa”…still Yana murmushi yace”sai in ringa siyowa umma..ko Kuma in dauki mai aiki da zatana yi mana girkin In biyata”…umma ta girgiza Kai tace”wato gak a majnoon koh..to ba gata kake yimata ba wlh..tun wuri ma in zaka canza ka canza”…bai sake cewa umma komai ba ya mike tareda ficewa daga dakin..ummi ta bishi da uwar harara tana dan rainin hankali kawai”????

Yau Wednesday Layla sun fito daga class..ganin akwai sauran time kafin another lecture..suka nufi cafeteria don cin abinci itada Hanna…table daya suka zauna..Hanna na duban Layla tace”what will you like to have”…Layla ta fada mata abinda zataci snn ta bada order..
Bayan an kawo musu abinci sun faraci..sunadan hiransu jefi jefi..kmr daga sama sukaga mace a gabansu..a tare suka dago kawunansu suna kallonta..Layla ta zare ido sosae tace”Anty Sameera”..Sameera ta saki wani matsiyacin murmushi snn taja empty kujeran dake kusa dasu ta zauna…ta shiga bin Layla da wani kallo tana cewa”so kece kika shiga tsakanina da mijina koh”…da mamaki Layla ke binta da kallo..kafin tayi mgn Sameera ta sake cewa”let me give you this worning..daga yanxu..I mean as from today..ki fita harkan mijina..Taheer mijina ne ba naki ba..so kibar wani jin dadi don an aura masa ke a sadaka..idan Kuma bakiji Mena fada maki ba..wlh wlh kinji rantsuwar musulmi..baki isa ki zauna da doctor lfy ba..yanda kika sa ya fasa aurena sbd ke..kema baki isa ki zauna dashi matsayin miji ba..Taheer mijina ne ni kadai..Kuma babu wadda ta isa inyi sharing dinshi da ita”..da sauri Hanna ta mike tana fadin”Hey.. Hlow..wacece ke..who do you think you are da zakizo ki samemu haka kawai ki fara mana ihu a Kai..have you lost it..anya ko kinada lfy”..a fusace Sameera ta kalli Hanna tace”ba dake nake mgn ba..so stay away”..tana rufe baki itama Hannan tace”ko ba dani kikeba ai da aminiyata kike..yanxu qatotuwarki dake ko kunya bakiji ba..kixo kina fada da yarinya karama a kan namiji..wa yace kiyi sake har ta kwace maki shi din”…Sameer ta daga hannu zata Kai Mata mari kawai taji an rike hannun nata…Layla ta kama hanun Hanna ta shiga janta suka bar wurin…Sameera ta bisu da kallo zuciyarta na tafasa…Saida sukayi nisa da wurin sosae Hanna ta kwace hanunta tace”wai meye hakane Jakada..ya mace zatazo tana faffada maki maganganu Kuma kiyi banza da ita..snn ni da nake rama maki kin wani janyoni kin fito Dani daga wurin..what’s wrong with you”…Layla batace komai ba..Saida ta samu wuri suka zauna snn tana kallon Hanna tareda dafa shoulder dinta tace”calm down mana babe..ni banga abun daukan zafi a nan ba”..Hanna ta ture hanun Layla dake kan kafadanta tana hararanta tace”ai bazaki gani ba dama..kawai mace tazo har inda muke ta raina mana hankali Kuma ki hanani ramawa…that aside..naji kmr tana mgnr kin kwace mata miji fa..Jakada kina nufin wai all this while kinada aure amma baki taba fadamun ba”…shiru Layla tayi na tsawon lokaci..batasan ta ina zata fara fada Mata cewa daddy is her hubby ba…Hanna ta dafa kafadanta tace”hlow..tunanin me kike Kuma”…Saida Layla ta sauke ajiyar zuciya snn ta shiga bata lbrin irin soyayyar da Taheer din ke Mata..alakar dake tsakaninta dashi..da yanda aurensu ya kasance da kuma shirye shiryen bikinsu da akeyi yanxu..da mugun mamaki Hanna ke kallonta tace”Amma gsky Jakada bakida kirki ko kadan..yanxu badon hakaba..da bazaki fadamin zaayi bikinki ba knn koh”..da sauri Layla na girgiza kai tace”wlh inata so in Fadi maki kawai bansan ta Ina zan fara bane”..ta bude bag dinta ta dauko cards da taketa faman yawo dasu ta Mika Mata tana cewa”take these..cards ne na gaba daya events din da zaayi..sun kusa sati cikin jaka na rasa ya zaai in baki..so ni waccan matar ma taimako na tayi”…Hanna tasa hannu ta amsa cards tana fadin”duk da haka baki kyauta min ba..amma kinsan wani abu..kwata kwata banyi mamaki da kikace daddy is your husband ba..don wani special kallo da naga yana jifanki dashi nasan dole Wanda akema tsanstar so akema wnn kallon”..Layla na murmushi ta girgiza kai tace”Hanna you are too much..dama sa mana iso kikeyi knn koh”…Hanna tace”no ba wani sa ido fa..abune da yake a fili..amma kinsan menene babe..ya kamata fa ki dage..ki kula da mijinki sosae..yanda kika samu yana maki irin wnn son..Nanda nn zaki mallake abinki a hannu..kinga ba ta yanda waccan witch din zata nemi shiga tsakaninki dashi”…Layla ta mike tareda kama hanunta tace”naji…yanzu ki mu tafi kar a fara lecture bamu komaba”…Hanna ta mike itama suka nufi hanyar clss dinsu tana cewa”gsky kina bukatn lecture akan yanda ake kula da miji Jakada..dole ma in baki sirrin yanda nake kulawa da Habibi na..shiyasa kikaga kullum Kara Sona yake”…Layla dariya kawai tayi tana girgiza Kai..ai Hanna sai a barta kawai..dama ya lafiyar kura..da can da batasan she’s married bama kullum karatu take mata kan yanda zatai handling saurayi and everything..yanxu kuwa da ta san tanada auren ai sai inda manta ya kare..tasan idan aka fara Mata lectures din kmr yanda ta fada..har sai taji ya isheta ma gaba daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button