Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yau Friday…ya kama saura sati biyu daurin auren Taheer…Layla ta samu ummi ta sanar da ita Usman ya kirata…ya ce Mata akwai wani aiki daya kawoshi Abuja…so yanaso yazo ya ganta…ba bata lokaci ummi ta aika a gyara bq inda zaa saukeshi…ita Kuma Layla ta tafi daki ta shirya.

4 pm daidai Usman ya karaso gidan…Layla ta shigo dashi ciki…in no time aka cika mai gaba da kayan ciye ciye.

5 Taheer ya dawo gida…bayan ya gama duk abinda ya saba ya nufi part dinsu…ummi…umma duk suna zaune parlor…ya karasa shima ya zauna duk ya gaishesu…umma tace”ga abinci can a dinning”…ya wani langabe Kai yace”umma feed me plss…idan da kaina zanci bazan iyaci da yawa ba…ba musu umma ta mike tana murmushi tace”to muje dinning din in baka”..shima ya mike suka nufi dinning din…ummi na binsu da kallo tace”yo ba dole ma Layla tayi iskanc da ta6ara ba a gidan nn…kalli fa uban ma da kanshi abinda yakeyi don Allah…katoton namji kaman kai ka wanice bazaka iya cin abinci da kanka ba sai an baka…Allah ya kyauta”su dai basu ce Mata qala ba…umma ta shiga bashi abincin a baki har yace ya koshi…suna dawowa parlor Layla ta shigo ciki…Kai tsaye inda yake ta nufa…ta zauna kusa dashi tace”daddy Ya Usman ne yazo…he said I should ask you..wai yanaso ya kaini shopping”ta karasa mgnr kanta a kasa…shiru Taheer yai na ‘yan mintina yana binta da kallo…sai Kuma a hankali ya janye idonshi a kanta snn ya daga Mata Kai alaman she can go…da fara’a Layla ta mike tayi pecking left cheek dinshi snn tace”thanks my daddy”…snn ta juya da sauri ta fita…ummi ta kama haba tace”lallai yarinyar nn batada kirki…dubi yanda tayi kmr bata ganmu a wurin nn ba Aisha…tayi mgn da uban kawai tasa kanta ta wuce sai kace shi kadai ne keda iko a kanta…to zata dawo gidan nn ta sameni”…umma murmushi kawai tayi batace komai ba…shiko Taheer abun duniya duk ya isheshi…wani wai zai kaita shopping tsabar rainin hankali…sai kace an fada mai tana bukatan wani abun…zaman parlon ma yaji duk ya gundureshi…sai ya mike kawai ya fice zuwa part dinshi.
Layla bata dawoba sai after magrib…sukayi sallama da Usman ya koma…ba yanda basuyi dashi ya kwana ba amma Sam yaki yadda…ya fada musu akwai hotel da sukai lodging…so a can zasu kwana tareda colleagues dinshi…
Layla ta shigo gida da Kaya Niki Niki a hanunta…ta nuna ma su ummi snn ta wuce zuwa dakinta.

Washegari Nafeesa da iyalanta suka iso…wnn karon hadda maigidanta…zaibi flight din 6 zuwa Dutse.
6 din kuwa daidai Taheer ya kaishi airport ya wuce.

Gida ya fara cika…ko da yaushe cikin hidima suke…an gama hada lefe tun last week amma Taheer yace a Bari sai an shiga satin biki sai a Kai…ba don ummi taso ba haka ta hakura sbd magiyan da umma ke Mata.

Kuyi managing plss..nasan baida yawa..am not feeling too well shiyasa…amma InshaAllah gobe zaku samu da yawa..thanks????????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattapad@ummuashraf22

17

Bayan kwana biyu suna zaune gaba dayansu a parlor…Ramadhan ya shigo parlon hanunshi rikeda waya…ya mikama mamanshi yace”Mami gashi Abba na Kira”…da sauri Nafeesa ta amsa wayan tayi picking tareda sallama…tayi shiru tana sauraron abinda yake fada a daya bangaren…sai Kuma ta mike tsaye da sauri tace”Subhanalillahi”…duk suka dawo da hankalinsu gareta…ta sake yin shiru tanajin me yake fada kawai sai ta fashe da kuka tana”innalillahi wainna ilaihi rajiun”…gaba daya sukayo kanta kowa na tambayan abinda ya faru…ita Kam kuka kawai take tana salati…Saida tayi kusan 3 mins snn cikin sheshsheka tace”Umma Usman ne”…Duum Layla taji gabanta ya Fadi jin an ambaci Usman…da sauri ta karaso inda suke itama tana zare ido…a kidime ummi tace”Nafisa kiyi mgn mana…meya faruda Usman din?…”He is no more…yayi accident a kan hanyarshi na komawa gida”…Nafisa ta fada da kyar…gaba dayansu salati suka saki…ummi tace”ban gane yayi accident ba Nafisa…baa jirgi suka tafi ba dama?…Saida nafisa ta share hawaye snn tace”jirgi sukabi amma a kano suka sauka…a hanyanshi na komawa Dutse sukayi accident din”…lokaci daya duk suka gigice…Layla kuwa dama tunda taji ance he is no more…ta toshe bakinta da hannu tareda rugawa zuwa dakinta…ta fada kan gado ta shiga rusa kuka kmr ranta zai fita(am also crying baby????)…kuka take tana tuna every single moment da sukayi spending tare…she remember irin yanda yake sonta…yanda yake riritata yana fada mata mata how much she means to him…”innalillahi wainna ilaihi rajiun…taketa maimaitawa tana jujjuya Kanta from one side to another.

A can parlor kuwa…Taheer da shigowanshi knn suka sanar dashi rasuwan…shi kanshi ji yai kaman kafafunshi bazasu iya daukanshi ba…yanxu Usman din ne ya rasu… innalillahi shima ya shiga fada har karshe sai Kuma ya mike zumbur yana kalle kalle….”Ina baby”ya fada yana binsu da kallo…nan da nan Kuma hankalin kowa ya dawo jkinshi…Sam ba Wanda ya lurada bata parlon…da sauri Taheer ya nufi dakinta…tana nan inda take Kuma har yanxu bata bar fadin innalillahi tana kuka ba…da hanzari ya isa kan gadon ya zauna tareda sa hannu ya janyota jikinshi…kmr abinda take jira knn ta rungumeshi gam tana Kara karfin kukan da take…su ummi duk suka biyoshi dakin suna kallon yanda take kuka…ba Wanda bata bama tausayi ba a cikinsu…Taheer daya rasa ta inda zai fara lallashinta kawai shima sai ya fara hawayen…Allah kadai yasan yanda yakeji sbd kukan nan da takeyi…abubuwa biyune suka taru suka tsaya mai…na farko kukan nata dako a mafarki bai son jinshi…sai Kuma kishin wanda takeyin kukan dominshi…dukda Usman din is gone amma ya kasa hana zuciyarshi jin kishin kukan nata…umma ce ta karaso inda suke tace”ya zaka sata a gaba kaima ka fara kuka Taheer…Kai daya kamata ka lallasheta Kuma sai ka biye Mata kuyita kuka sai kace ba namiji ba”…a hankali yasa hanu ya goge hawayenshi…itama ya dago fuskanta ya shiga share Mata nata…ta rike hannayen nashi a nata tace”daddy don Allah da gaske ya Usman ya mutu…da gaske ya tafi bazan kara ganinshi ba daddy?…still Yana share Mata hawaye ya daga mata Kai alaman yes…sai ta sake fashewa da wani kukan tace”Dan Allah daddy kace ba gaskiya bane…ummi Dan Allah kuce mafarki nakeyi ba gaskiya bane… yacemin zaizo daurin auren daddy…Dan Allah kuce masa kar ya tafi ya barni…he means a lot to me don Allah kar ya tafi ya barni”a hankali Taheer ya janyeta daga jikinshi tareda mikewa tsam ya fice daga dakin…bazai iya jin abubuwan da take fada ba sam…da sauri Nafisa itama ta fita daga dakin tana fashewa da kuka …she really feels for her daughter…wani tausayinta taji ya kamata… ummi ce tayi karfin halin karasawa inda suke ta kamo Layla ta rike da kyau tace”Dan Allah ki dena kukan nn Layla…so kike ki jama kanki wani ciwon…kiyi hakuri kiyi mai addu’a kinji”…kawai ta fada jikin ummi tana fashewa da wani kukan.(me neman kuka ne dama aka jefeshi da kashin awaki????)

Taheer tunda ya shiga daki ya kwanta sai ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi…Allah ya sani baiji dadin mutuwar Usman ba amma bai San dalilinda yasa yakejin kishin kukan da Layla takeyi sbd shi ba…wnn ya nuna Layla na son Usman knn…wani abu yaji ya tokare mai a makoshi…gaba daya ji yake inama baije inda takeba.

Da dare Taheer ya shigo dakin Layla da har yanxu ummi da umma ke ciki…ya kalli Layla da dakyar aka samu tayi bacci bayan maganinda aka bata Wanda shine ya sata baccin…ya samu wuri ya zauna gabanshi na faduwan abinda zai fada yace”Ummi dama inaso ne ki Kira uncle ki fada mishi anyi mutuwa snn don Allah ummi kice mai inaso a dan daga bikin nn ko sati biyu ne a Kara kinga bazai yiwu ayi biki ana cikin alhinin mutuwa ba”…yana gama mgn yayi kasa da kanshi praying Allah yasa ummi ta yadda…umma na girgiza Kai tace”aah bai kamata a daga biki ba Taheer…Wanda ya mutu ya riga ya mutu addu’a kawai yake bukata”…a hankali ummi tace”aah Aisha bai kamata ayi biki a wnn halin ba…yaron nn fa shine yake neman auren Layla…ko don wnn bai kamata ayi bikin ba…zan Kira uncle din naka ko sati biyun sai a Kara”…wani dadi Taheer yaji da ya dade baiji irinshi ba…bai taba tunanin ummi zata yadda cikin sauri haka ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button