Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Mum Ashraf✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

10

Washegari Monday da wuri yai Shirin office as usual ya shiga part din ummi ba kowa parlor don haka ya wuce bedroom din ummi…tana zaune kan dadduma tana lazimi Layla Kuma na kudundune cikin blanket a kan gado…ya karaso cikin dakin ya zauna yana mamakin ganin Layla….a nan kenan ta kwana baa dakin nata ba…Ummi ta shafa adduanta snn ta juyo tana kallonshi”ummi Ina kwana”ya fada yana Mata murmushi…ta amsa da”lfy Lou Taheer ya jikinka..jiya Layla tacemin wai kanka ke ciwo..ya Dan shafa Kai yace”naji sauki ummi…sai ya kalli Layla dake kan gadon yace ummi a nan ta kwana ne?..ummi ta ninke daddumarta snn tadanja siririn tsaki tace”ai Layla dai Allah ya nunamin ranar nutsuwarta..kawai sai farkawa nai naji mace a bayana ta wani makaleni kmr zata koma ciki..Taheer ya danyi murmushi ganin yanda unmin ke mgn snn yace “ummi to mene a ciki donta makaleki ummi… dadi ma ya kamata kiji baby ta kwanta a jikinki…tun bai rufe baki ba ummi tace”Allah ya sawake..mudai Layla Kuma ai sedai Allah ya fiddamu kunya a gurin mijinda zata aura…yarinya sai son jiki kmr kyanwa..ta wani makaleni ta hanani bacci kmr jaririya…haka zaayi Mata aure taje tana makale miji ta hanashi bacci knn…dukda yanda mgnr ummin ta sokeshi jin ta ambaci mijin Layla saidaya danyi murmushi jin abinda ta fada din..yasa hanu ya yaye bargon data lulluba dashi don yasan tana jinsu Sarai ba bacci takeba…ta juya baya da sauri tana turo baki…yai murmushi yace”yau ni din ake juyama baya baby…batace komai ba sai kawai ji tayi ya janyota zuwa jikinshi…cikeda takaici ummi tace kaidai Allah ya shiryeka wlh..ya yarinya zata aikata laifi ina fada maka maimakon ka mata fada sai ka wani janyota zuwa jikinka…Kai har yanxu kallon jaririya kakema Layla koh…bazaka dinga tsawatar Mata akan laifi ba saidai ka ringa sangarta ta koh…yai murmushi yasa hanu ya manne Layla daketa mustu mustsu a jikinshi gam snn ya kalli ummin yace”laifi nayi mata fa shine zan bata hakuri…ummi ta saki salati tace”to kuwa abun naku ya zama innalillahi wainna ilaihi rajiun…. wlh tun wuri ma kayi ka fito da matarka…kayi aurenka ka tafi can ka barni inyiwa yarinyar nn tarbiyyan daya Dace…don wnn halin da kake koya Mata Sam ba halin zaman gidan miji bane…tana karasa fada ta fice daga dakin tanata bambami.
Bayan fitanta ya Kai dubanshi ga Layla da tayi luff a jikinshi kmr ba ita ce ke kokawa dashi ba dazu…yasa hanu ya janyeta yanajin yanda abubuwa da dama ke Kai kawo a cikin jini da tsokarshi game da ita…Sam baima ji abinda ummi ke fada da kyau ba cox his heart has gone so far da babu abinda yake tunawa sai ita sai Kuma muradin kasancewar tareda ita har mutuwa…ganin zata fara mai kuka ya girgiza Kai tareda janyota jikinshi yace”baby mana…don’t cry plss…am sorry for sending you away last night hakan bazai sake faruwaba kinji”…ta dago tana kallonshi snn ta jijjiga mai Kai…yai murmushi yace kin hakura?nanma Kai ta sake dagawa…ya manna Mata kiss a forehead dinta snn ya mike yace “alright ki koma baccinki baby na tafi aiki…tace sai ka dawo snn ta koma ta kwanta shi kuma ya fice a dakin…ya samu ummi da Mama hawwa a kitchen yai musu sallama ya tafi ummi nata fadan don me bazai tsaya yayi breakfast ba.

Koda yaje clinic ayyuka sunmai yawa sosae amma duk da haka batun auren Layla na nan makale a zuciyarshi he wish zuciyanshi na iya mantawa da batun son Layla ya cigaba da rayuwarshi kmr yanda yakeso Amma inaa…ya kasa gane wane irin abune wnn…wane irin jarabawane wnn…why Allah zai jarabceshi da son Layla bayan bazai sameta ba…yai saurin istigfari jin zai fara kauce hanya ya cigaba da aikinshi.
Around 5 sai ga Yusuf yazo…bayan sun gaisa Yusuf ke tambayanshi abunda ke damunshi…yai shiru kmr bazai fada ba sai Kuma daga karshe yaima Yusuf bayanin komai…ya Dora mai da fadin shawaran daya yanke na zai amince da auren matukar Layla ta amince…shawarwari sosae Yusuf ya bashi tareda bashi kwarin guiwa kan abinda yake Shirin yi…snn ya bashi shawaran ya samu ya fidda mata shima yayi aurenshi if possible kafin ayi na Layla don hakan zai taimaka wajen mancewa da son Layla snn zai faranta ran umminshi… Taheer yayi naam da wnn shawara ya Kuma tabbatarwa Yusuf hakan zaayi Amma zai fara mgn da ummi…sai da sukai sallar magrib snn Yusuf ya tafi gida shima Taheer din ya nufi gida feeling exhausted.

Saida ya fara shiga part dinshi yai wanka yai changing zuwa kananan kaya snn ya nufi part din ummi…tana zaune parlor tana kallon news..ya zauna kusada ita suna kallon tare Saida aka gama ummi tace”ga abincinka can a dining”…yace “I want to talk to you first”ummi ta gyara zama snn tace umhum Ina jinka…yai shiru na ‘yan seconds snn yace”ummi na fitar da matar da zan aura”…zaro ido ummi tayi cikeda tsantsar farin ciki sai Kuma ta mike ta fara sujada Saida ta gama ta koma mazauninta still tana murmushi tace”Allah alhamdulillah..Allah na gode maka daka amsa addu’ata”..Taheer shiru kawai yai yana kallon yanda mgnr daya fada ta Sanya mahaifiyarshi farin ciki haka..sai ya sake samun kwarin guiwan abinda zaiyi indai zai faranta ran ummi haka to he is ready yai aure ko baya son matar sbd farin cikin ummi…”kasan wlh duk a dame nake kan mgnr aurenka Taheer… tunanina ko bakada lfy shi yasa baka shaawar auren Amma yanxu alhamdulillah Allah ya maka albarka ya tabbatar da alkhairi…ya amsa da ameen cikin ranshi ko mamaki yake wai shi suke tunanin baida lfy…yai murmushi kawai don yasan da lafiya yanama mutum yawa to da shi zaice yamai yawa indai lafiyan abinda suke tunani ne…ummi ta sake mai tunani da fadin”to wacece ita snn a Ina take?..ya Dan sosa Kai yace”sunanta Sameera ummi..a nan Abuja take ai zan kawo miki ita kafin manya sunyi mgn…ummi ta sake murmusawa tace “to Allah ya nuna mana Taheer Allah ya tabbatar da alkhairi…ya sakeyin shiru na ‘yan seconds snn yace ummi baki tambayeni mgnr da mukai da alhajin Dutse ba…ummi daketa murmushi har yanxu tace ai nasan idan mgnr daya kamata in sanine zaka fadamin so I don’t have to ask…shima yai Dan murmushin snn a hankali ya fada Mata duk yanda sukai da alhajin snn da shawaran daya yanke..shiru yai yana ganin ynd farin ciki ya sake mamaye zuciyar ummi.. Saida ta furta Alhamdulillah sau uku snn tace”Amma naji dadin wnn mgn Taheer.. Allah ya tabbatar da alkhairi…kmr sun San ko kullum zullumina bai wuce tunanin mijinda Layla zata auraba..kasan maza yanzu ba cika gane halinsu akeyi a wajeba…musamman Layla da takeda kyau kana ganin tun yanzu yanda maza ke rububinta Ina ga Kuma nn gaba in ta sake zama yammata…idan kuwa aka tsyar Mata da miji shknn duk Wanda yazo sai ace anyi mata miji…snn kaga har yanxu hankali ba wani isanta yayi ba kullum adduana Allah ya bata mijinda zai dauki childishness din nn nata sai gashi Allah ya kawo…ai Usman baida matsala Allah ubangiji ya muku albarka gaba daya…a hankali Taheer ya amsa da ameen can cikin ranshi ko ji yake inama zai iya fitowa fili ya bayyana irin qaunar da yake Mata tunda su sun kasa ganewa…wai ace har yanxu duk cikinsu ba Wanda ya iya gano tsantsar qaunar da yake Mata…su kullum dauka sukeyi shi babanta ne and bai da right din da zaice he loves her…ya mike kawai batareda yacema ummi komai ba ya nufi dakin Layla…bude kofanshi yayi daidai da lokacinda towel dinta ya subuce daga jikinta yai kasa…ta zaro ido da sauri ta dauko towel din ta sake daureshi a jikinta tana rarraba idanu…ya dauke kanshi a hankali daga kallonta lokaci daya wani irin kasala ya diran masa…ya isa bakin gadonta ya zauna yama rasa da wanne zaiji…Layla ta dafe kirji tareda sakin ajiyan zuciya Allah ya taimaketa daddy ne and akwai pant da bra a jikinta…gefen gadon ta karsa itama ta zauna snn tace”daddy sannu da dawowa…maimakon ya bata amsa sai cewa yai”baby bakida hankali koh..wato a gaban kowama haka kike kunce towel kowa ya kalleki ba kaya abi?..ta marairaice tace”Allah daddy ba haka nakeyi ba yau ne kawai..gaba daya towels din nawane basada girma shiyasa amma kayi hakuri”…a hankali yaketa sauke ajiyar zuciya snn yace”idan kin gama shiryawa ki sameni part dina zamuyi mgn dake”..a hankali tace toh..shi Kuma ya mike ya fita a dakin gaba daya da kyar ma yake iya tafiya duk abubuwa sun taru sun cikamai brain bai ma San da wanne zaiji ba…baibi takan abincinshi dake dinning ba ya wuce abinshi don ummi dama ta koma dakinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button