Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yana shiga ya fada kan gado Yana tunanin…yanxu shknn zai hakura da Layla shknn yanxu yanaji yana gani zata auri wani bashi ba.. innalillahiwainnailaihirajiun…duk sa’adda yai tunani makamancin haka ji yake inama Allah zai dauki ranshi ya huta…a yadda yake kishin Layla gani yake bazai iya jure ganin tana tarayya da wani namiji har suyi aure snn har su hada shimfida…innalillahi ya sake maimaitawa sau uku yana me jin kmr ya cire zuciyarshi ya cillar ko zai samu sukuni…shknn shi yanxu bai da guts din da zaice yana sonta sbd kowa kallon babanta yake mai…ita kanta Laylan kallonda takemai knn…”this whole thing is killing me”…ya fada a hankali yayinda hawaye suka shiga sintiri kan kaykawan fuskanshi..bai hanasu zuba ba don yasan shine kadai samun saukinshi…jin an bude kofar parlor yasashi saurin mikewa ya shige bathroom don yasan itace and bayaso tazo ta sameshi a halinda yake ciki…Layla ta ajiye abincin dake hanunta a parlo snn ta shigo dakin nashi ganin bai nn yasa tai tunanin kilan yana toilet…ta zauna kan gado tareda daukan wayanshi dake gefe ta shiga yin game dashi…tana nn zaune ya fito Yana sanyeda bathrobe…ya karasa gaban mirror ya fesa perfumes kadai snn ya nufi closet dinshi ya zira milk jallabiya ya maida bathrobe din toilet snn ya dawo ya zauna kusa da ita…a hankali ya karbe wayanshi dake hanunta yace”mgn fa zamuyi”batace komai ba ta juyo tana fuskantarshi..sai kawai yaji ya kasayin mgn..so yake ko kalma daya ta fito daga bakinshi Amma inaa…banda kallon lips dinta da suke nan ja babu abinda yake…haka nan yaji gabanshi ya shiga faduwa…heart dinshi ya fara beating at a faster rate…kmr ana janshi haka ya cikata gab din dake tsakaninsu…ya tallabo fuskanta da duk hannayenshi…kallon ido cikin ido sukema juna yayinda ita bada wani manufa take kallon nashi ba…shi kuwa ji yake yau idan baiyi kissing bakin baby ba zai iya mutuwa…ya dade yana controlling desire dinshi a kanta amma na yau is beyond him…baijin zai iya hakura this time around…a hankali ya shiga circling lips din nata da finger dinshi yanajin yanda feelings keta rushing into him(abunku da tuzuru????)..a hankali ya lumshe ido har ya sunkuyo Yana gab da hada bakinshi da nata sai Kuma ya saketa yai saurin janye jikinshi a nata Yana salati…ya mike da kyar yana hada hanya ya koma toilet din ya rufe don bazai iya hada ido da itaba…yanxu wane irin kallo zata mai…”what am i doing..what has came over me..oh Gosh why can’t i control my feelings…ya rabbi kana gani…rabbi don’t let me suffer plss…not again…Allah ka bani juriya Allah kar kasa na aikata abinda daga baya zanzo Ina Dana sani plsss…ya ya karasa mgnr tareda durkushewa nn toilet yana hawaye wani kan wani.
Ita kuwa Layla har ga Allah bata kawo wai wani abu zaiyi Mata mara kyau ba…kawai dai tayi tunanin peck zaiyi mata kmr yanda ya saba sai Kuma taga ya fasa snn ya koma toilet yana tafiya kmr dan maye…”what is wrong with my dady plss…what’s happening”..ita kadai take maganganun nn sai a hankali ta mike ta fita a ranta tace kilan yau daddy is emotional shiyasa yake acting weird..but she prays Allah yasa ba wani abu ke damunshi ba…zata cigaba da mai addu’a kmr yanda ya bukata.
TAHEER…
Saida ya tabbatar ta fita snn ya fito daga toilet din yaje yayi locking kofar snn ya dawo ya sake kwanciya akan gadon…har yanxu bai bar tunanin meya hau kanshi da har ya kusa sashi aikata abin kunya har haka ba…me yasa yau ya kasa controlling abinda ya dade yana controlling tun tuni…ya sani ba tun yau ba yakeda sha’awan lips dinta…amma ai bai taba attempting kissing dinta ba sai yau…ya sauke ajiyar zuciya wato kmr yanda sonta ke growing very rapid a zuciyarshi hakama desire dinta knn…”well I must definitely put a full stop to this…if not watarana zanyi abin kunya”..Allah ka bani juriya da ikon danne abinda nakeji plss.
Don’t forget to vote and follow me on Wattpad@ummuashraf22
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
11
Wannan Daren ma kmr wancan Sam Taheer bai samu bacci ba sai dayai sallahn asubah…hakan yasa bai tashi da wuri ba sai after 10….bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya as always ya nufi part din ummi…tana zaune parlor tana kallon wani program ya zauna kusada ita bayan sun gaisa tace”ya ciwon kan naka”….yace “to da sauki zaace ummi nasan stress ne idan na samu hutu zai Dena…tace”ya kamata dai ka samu kayi hutun gsky”…yace InshaAllah..baby bata tashi bane?Ummi tace “kmr dai bata tashin ba don tunda na fito banji duriyarta ba…ya mike Yana fadin bari in duba mgn nake sonyi da ita…tana tsaye gaban press dinta tana neman kayanda zata saka ya shigo dakin..ta juyo da murmushi a fuskarta tace”good morning Daddy”Yana murmushin shima ya amsa Mata”morning..zo muyi wata mgn”ba musu ta dawo gefen gado ta zauna tareda maida hankalinta gareshi…Saida ya kauda kanshi snn ya fara mgn”Usman ne dama yace Yana sonki and he wants to marry you”Layla ta zare ido da mamaki tace ban gane he wants to marry me ba daddy..wane Usman din ma kke mgn in the first place?ya kamo hannayenta ya rike snn a hankali yace”dama mgnr daya kaimu Dutse knn…Alhaji ya fadamin Usman yace Yana sonki Kuma suna son hada aurenki dashi amma sai da amincewarki…idan bakiso ba Wanda zai maki dole”Layla tayi shiru na tsawon lokaci tana tunani kafi tace”daddy to Kai yanxu zakamin aure ne?bakace sai na gama school zakamin aure ba”Taheer ya lumshe ido ya bude snn yace”haka na fada baby Amma bazan iya musu da Alhaji ba…kinga a ka’ida Yana da right din da zai badake ga duk Wanda yakeso amma sbd karamci irin nashi sai baiyi hakan ba..ya kirani ya sanar dani snn yace a tambayeki..amsanki kawai muke sonji kina sonshi ko baki sonshi??Saida tadan tabe baki snn tace”am not used to loving u know..ban taba son kowa ba apart from you sai su ummi so ban San ya so din yakeba..amma daddy Kai ka amince ne..I mean kanason in aureshi?Taheer yai shiru kawai Yana kallonta ji yake inama zai iya fitowa ya sanar da ita shima yana sonta..inama zai iya nuna Mata babu Wanda ya Dace da ya aureta face shi…tunanin hakan yasa zuciyarshi ta sake karyewa da kyar ya daga Mata Kai alaman ya amince…sai ta saki murmushi tace”Nima na amince daddy..ban San ko Ina sonshi ba amma na amince sbd Kai..nasan InshaAllah with time zanyi developing feelings for him”ya Dan kakalo murmushi snn yace “alright bari inje in kirashi sai in sanar dasu kinyi accepting..bai jira cewarta ba ya fita a dakin da sauri..baibi takan breakfast din bama ya wuce abinshi.
Yana shiga daki ya Kira alhaji ya sanar dashi ta amince..alhaji ya nuna farin cikinsa sosae snn yace zai sanar da Usman ta amince ko a waya sai su fara mgn da ita kafin ya samu lokaci sai yazo Abuja su sake fahimtan juna.
A bangaren Taheer kuma ya yanke ma kanshi hukunci zai fara yin baya baya da Layla..a tunaninshi hakan ne kadai zai saukaka mai abinda yakeji gameda ita… snn kuma bazai iya jure yana kallonta tana waya da wani a mtsayin Wanda zata aura ba…so it’s better ya rage shiga harkanta kawai…kazantar da baka gani ba akace tsafta ce.
Wannan kenan
Kwanaki nata tafiya yayinda shakuwa me karfi ke shiga tsakanin Layla da Usman…dukda bai taba zuwa Abuja ba amma kasancewarshi mai raha da son mutane cikin lokaci qarami Layla ta fara sabawa dashi snn ga uwa uba soyayyan da yake gwada mata…duk da har yanxu bawai zatace ta fara sonshi bane but tanajin dadin kasancewa tare dashi.
Saidai wani abu dake damunta shine canji data gani tattare da daddynta..Sam bata San laifinda ta aikata mai girma haka da har zaisa daddy ya fita harkanta gaba daya..he no longer cares about her kmr yanda yakeyi a baya…abun ba karamin damunta yake ba kuma ta rasa wanda zata fadawa…ko mgnr aurenshi da anty Samira a bakin ummi taji tasan da Dane da bakinshi zai fada Mata tunda yasan tanaso yai auren…gaba daya she’s confused bata San laifinda ta aikata ba…kodai don tayi accepting Usman ne??ta tambayi kanta sai Kuma wata zuciyar tace ba haka bane ay Saida ya nuna amincewarshi snn itama tayi amma why daddy zai juya Mata baya haka?