Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Kamar yanda umma ta fada ta samu Taheer a part dinshi…Yana zaune parlor yana kokarin Kiran Sameera don misscalls kusan 10 ya gani nata umma ta shigo….ya ajiye wayan a gefe Yana kallonta da murmushi yace”umma kece?…Saida ta zauna kusa dashi snn tace”nice mana Taheer…ai nace maka zanzo”… ya jinjina Kai alamar hakane snn ya maida hankalinshi gareta…cikin zuciyarshi Yana addu’a Allah yasa ba asirinshi ne zai tonu ba…Sam bayaso kowa yasan Yana kaunar Layla don abun kunyane a gareshi…”inaso ka fadamin tsakaninka da Allah meya hadaka da Layla”mgnr umma ta dawo dashi daga tunanin da yake…ya dago yana dubanta a rikice yace”umma cewa tayi nayi Mata wani abun ne?…umma na girgiza Kai tace”bata fadaba…amma na tabbata akwai laifin da tayi maka…Taheer yai shiru kawai yana tunano abunda idanunshi suka gane mai dazu…umma ta dafa shoulder dinshi tace”bai kamata kana fushi da ita ba irin haka…kasan dole hakan yai affecting dinta don ba haka ka sabar Mata ba…it’s better kayi mata fada if possible ma ka zaneta…ai she’s your kid…ba Wanda zaiyi questioning dinka don tayi laifi ka mata hukunci”….da sauri ya dago yana kallon umma…har cikin ranshi yaji kalmar duka data ambata…sai Kuma ya shiga girgiza kai yace”umma ni…ni Taheer kike ganin zan iya daukan hannu na in zane baby dashi?…no…never…umma wnn abune wanda ko a mafarki ban jin zai iya faruwa so ki dena ma mgnr duka plss…babu laifinda zatamin ince zan daga hannu in dora a jikinta da sunan duka…bazan ma iya bane”….shiru umma tayi tana kallon yanda duk ya gigice kawai sbd tace ya daketa…cikin zuciyarta kuwa tunani ne kala kala…to kodai yaron nan son Layla yakeyi ne?ta tambayi kanta sai Kuma da sauri ta kawar da tunanin tace”it can never be possible…ya akai ma nayi wnn tunanin…hanunshi da taji ya riko nata yasa ta dawo daga tunani da take ta dubeshi…yana murmushi yace”umma wnn mgnr a barta for God sake…kema ki manta kawai kije kiyi baccinki it’s getting late”…bata sake cewa komai ba tayi murmushi kawai snn ta mike tana kallonshi tace mai”to Saida safe”ya amsa da Allah ya tashemu lfy umma…Yana binta da kallo har ta fita….ya sauke ajiyar zuciya tareda jingina jikin kujera yana tuna maganganun umman…”wai in zaneta”kam duk ranar da hakan ya faru nasan nima for sure saina Zane kaina…Allah ma ya kiyaye.
Washegari….
Flight din 10 Usman yabi…don bai samu tafiya jiyaba ummi tace ya kwana kawai tunda dare yayi…nan ya kwana a boy’s quaters… first thing in the morning yai sallama dasu ya tafi…ba tareda yayi sallama da Layla ba…don baccin karya tayi tanajinshi taki fitowa…a cewarta shine Wanda ya hadata fada da daddynta.
Da yake su Nafeesa jirgin 2 zasubi so Usman ya rigasu tafiya.
Taheer ma bai fitoba sai around 1 lokacin ya gama shirinshi tsaf..Yana saukesu airport zai wuce clinic coz he’s on evening duty today…bayan ya dawo daga masallaci ya nufi cikin gidan…sun gama shiryawa…don haka aka Debi kayansu aka kai mota…shima ya gaisa dasu ummi yace su Nafeesa su zo ya kaisu akwai patients da zai duba by 2.
Bayan sun gama sallama da koke koke finally dai suka shiga mota aka tafi…Layla na zaune front seat sanyeda zumbulelen hijabinta…fuskanta ya kumbura sosae sbd kuka…hankalin Taheer ba karamin tashi yayi da ganin yanda fuskan nata ya komata…dukda har yanxu bai huce ba amma tausayinta yakeji sosae…bayason abunda zai bata ranta Sam…har suka isa airport ba wani walwala tattare dasu…bayan sun gama fitowa a mota…Nafeesa na kallonshi tace”to bro mu zamu tafi sai ranan da ka kiramu Kuma”…yadan bude ido yace”rananda na kiraku Kuma?..tana dariya tace”Ina nufin muda mu dawo sai bikinka…Dan Allah bro ka daure dai kayi auren nn ko don ummi”ya Dan kakalo murmushi yace Mata”karki damu yarinya…very soon zaku sake dawowa InshaAllah”tana murmushi ta jinjina kai tace”Allah ya yadda…and for your information…wannan(ta nuna Layla dake tsaye gefe)itace yarinya badai niba…yara ukku gareni so mind you ka Dena Kiran wnn sunan”…dariya kawai Taheer yai snn yace”naji…Bari inzo in wuce banso lokaci ya kure ban isa ba…Allah ya saukeku lfy…ta amsa da ameen sai munyi waya…sukayi sallama da Layla snn suka nufi waiting area…su Kuma suka shiga mota suka tafi.
Bai zama lallai ku jini gobe ba sbd zanyi tafiya..amma idan na samu dama zanyi ko Dan kadan ne so ayimin uzuri pls????????thanks
Ummu Ashraf loves you loads❤️
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
This page is dedicated to my sis#Amina Aminu Kibia(Maman Maimunatou)I luv you♥️????
14
Ko a hanya ba Wanda yace kala…ita Layla tana Satan kallonshi…Kuma tanaso tamai mgn amma ta kasa…da kyar tayi gathering courage tace”Daddy”..ya Mata banza yanaci gaba da driving dinshi…ta share hawayen idonta a hankali ta sake cewa”daddy plea…maganan ya kakare sbd wani wawan burki da taji yaja…ta shiga waige waige taga suna gefen titi snn ta dawo da kallonta gareshi…kallon nata yake shima fuskan nn a tamke…saika rantse bai taba dariya ba…a kausashe ya fara mgn”I think I’ve told you…I’ve worned you kar ki sake yimin mgn…for as long as am concern bamu hada komai dakeba…so stay away from my life…and am staying away from yours too”..da sauri ta shiga girgiza kai tana sake fashewa da kuka…tama kasayin mgn…shi Kuma ya kunna motan snn yaci gaba da tafiya…yanaji tanata kukanta baice Mata kala ba har ya isa kofar gidansu…yai parking nan waje ba tareda ya kalleta ba yace”you can go”…ba tareda ta kalleshi ba itama ta bude motan ta fita da gudu…daidai zata shiga gidan tayi tuntube da gate din ji kake timm ta Fadi a kasa…mai gadi dake gefe Yana kallonta ya taho da sauri yana salati…yana Shirin dagata Taheer daya iso wurin shima da gudu yace”don’t touch her”…a tsorace mai gadi yayi baya ya shiga zare idanu yana kallon Taheer din…bai taba ganinshi cikin yanayi irin wnn ba…shiko Taheer daukanta kawai yai yayinda taketa rusa kuka ya nufi cikin gidan da ita…ummi ta mike da sauri tana kallonsu tace”na shiga uku ni Maryam…me zan gani haka…Taheer meya sameta?…baice Mata kala ba ya nufi dakin Layla…kan gado ya ajiyeta tareda daga kafanta yana dubawa…he’s praying Allah yasa bataji ciwo ba…ya kwashi kusan 15mins yana examining jikinta ganin ba wani ciwo ya ajiye Mata kafan a hankali snn ya fita…part dinshi ya koma ya dauko pcm ya dawo…a parlor yaci karo da Mama hauwa…tana fara’a tace”aah likita zaa tafi wurin aikin ne?..yai Dan murmushi yace”tafiya zanyi wlh mama…gashi na kusa makara ga wnn…ya Mika Mata maganin hanunshi snn yace”ki taimaka ki mikama baby pls..kice Mata lallai ta tashi tasha yanxu sai ta koma ta kwanta”…mama hauwa ta amsa tana fadin”yanxu kuwa zaa Kai mata likitan likitoci…Allah ya tsare”ya amsa da ameen Yana murmushi snn ya juya ya fita…ita Kuma ta nufi dakin Layla don ta isar da saqo.
Kwana biyu umma ta Kara snn ta koma kano ba don ummi taso ba haka ta kyaleta ta tafi.
Bayan Sati uku…
Yanxu Ramla nada sati hudu knn da haihuwa…inda a gobe suke Shirin tafiya kano gaba dayansu…ita Ramla idan taje sai ta cika kwana 40 da haihuwa snn zata dawo yayinda ita Kuma ummi zataje kan mgnr neman auren Taheer da takeso kawunsa yazo ya nema mai…dole ummi tasa Taheer daukan leave na one week a office don da farko cewa yai shi bazaije ba…ita kuwa Layla ba wani farin ciki take da tafiyan ba sbd yanda har yanxu Taheer bai bar fushi da itaba.