Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Daga masallaci ko part dinshi bai koma ya nufi cikin gidan…duk sun shirya shi kadai suke jira…Nafisa ta dubi Al’ameen tace”kaje ka Kira Layla idan Kuma bazataje bane muyi tafiyarmu…yarinya sai shegen nawa”…Dan hararanta Taheer yayi yace”sai in fasa kaikun ma wlh…ai tasan ni zan kaiku so dolene ku jirata”…dariya nafisan tayi tace”Allah ta cika nauyi da yawa ko yaushe sai an jirata”…ya bude baki zaiyi mgn Layla ta shigo parlon Al’ameen na bayanta…kaff yaji yawun bakinshi ya kafe karkaff…mgnr da yakeson fada ya makale a bakin…wani irin kyau yaga tayi tamkar Wanda zataje gasan kyau…Arabian gown ce a jikinta a black…tana da adon manyan flowers yellow masu stones a jikinta…tayi veiling da mayafin abayar… fuskanta ko powder babu sai kwalli da tasa a idonta…takalmin kafarta vine slippers ne shima yellow…sai wayanta dake rike a hanunta…umma da fitowanta knn itama…tai tsaye tana kallon yanda yake binta da ido tamkar bai taba ganinta ba…suna hada ido da ita ya sunkuyar da kanshi da sauri tareda juyawa ya fice daga parlon.
Special thanks to my WhatsApp people..but bana ganin comments dinku yanxu…Aren’t you guys enjoying the story??
If No then I need to see ruwan comments plss…you know feedback is Always important..thank u????????
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
18
Yana zaune cikin mota suka fito…Layla ce karshen fitowa tana rikeda hanun hibba…ya sake kafeta da ido yana jin ciwon fitan da zatayi a haka…ba don umma da yaga namai kallon tuhuma ba…da bata isa ta fita da wnn kayan ba wlh…duk ranshi ya kara baci…tana isowa ta bude front seat ta shiga tareda dora hibba a kan laps dinta…Taheer yai ma motan key suka fita daga gidan…Saida suka hau kan titi snn ya kalli Nafisa ta mirror yace”ranki ya dade ina Muka nufa?..dariya tayi tace”ko inama bro ai Kaine Dan gari…duk inda kasan zamu samu kaya masu kyau”…bai sake mgn ba ya dauki hanyar store din da suke siyayya…tafiyan 15 mins ne ya kaisu wurin…bayan yayi parking duk suka bude motan suka fita…Layla ta Dan saci kallonshi…ganin fuskar nn a tamke ta fita daga motan da sauri…duk ya hade fuskan nn wlh tsoro yake bata…Taheer na ciki yana binsu da kallo har suka shiga ciki…ya kifa kanshi da starring motar Yana sauke numfashi…bai san wane irin kishi yake dashi a kan yarinyar nn ba.
Ganin sun dauki kusan 40 mins basu fitoba…sai ya bude motan ya fita…Kai tsaye ya shiga ciki…Nafisa ya fara cin karoda ta dau duk abinda takeso Al’ameen na tura kayan a trolley…gaban counter suka karasa…shima Taheer din ya karasa snn ya bada atm dinshi don a cire kudin a ciki…ya kalli Ramadhan dake tahowa hanunshi rikeda wasu kayan…yace”Mami ga wani mutum can ya tare Yaya ya hanata tahowa…wai Yana son mgn da ita”…tun kafin tayi mgn Taheer ya dubeshi da sauri yace”where is she?…da hannu Ramadhan ya nuna mai wurin da take…bai sake cewa komai ba ya nufi wurin da sassarfa…ranshi in yayi dubu to a bace yake…Nafisa ta bishi da kallo kawai snn ta maida hankali kan fito da kayan data siya din.
Taheer na Shan corner ya hangota tsaye da wani namiji…bai iya ganin face dinta cox ta juya baya amma he can clearly see yanda guy din ke Mata murmushi…ya karasa wurin da sauri…ba tareda yace komai ba kawai yasa hannu ya shiga janta daga wurin…guy din ya sha gabansu yana kallon Taheer din yace”don Allah please…mgn kawai zanyi da ita ba jimawa zatayi ba”…yana gama fadan haka yasa hannu ya kama dayan hanun Layla dake rikeda wayarta Yana kokarin ya jata kawai yaji saukan Mari a kuncinshi…ya saki hanun nata da sauri tareda dafe inda aka mareshin…Layla batasan lokacin da ta saki wayan nata a kasa ba…tareda sa duka hannayen nata ta toshe bakinta dasu…hawaye ya shiga bin kuncinta wani kan wani…Taheer na kallon guy din dake dafe da cheeks dinshi har yanxu…cikin muryar gargadi yace”don’t you ever…kar ka kuskura ka sake ganinta kayi tunanin yi Mata mgn talkless of dora filthy hands dinka a jikinta”…Yana gama fadan haka ya kama hanun Layla ya shiga janta da mugun sauri…sai da ya bude mota ya turata ciki snn ya zagaya shima ya shiga…dama already su Nafisa na ciki…yaja motan da wani irin gudu suka fita daga wurin…Nafisa na tambaya meya faru…da kyar Layla na kuka ta fada Mata abunda ya faru…ta karasa da fadin”wlh ba laifina bane Mami…ki tambayi Ramadhan Ina cikin tsaiwa na yazo ya faramin mgn”…Nafisa da mamaki ya isheta tace”sai ki dinga kula daga yanxu…ba kowanne namiji ne zaka tsaya kana mgn dashi a wani wurin ba”…shidai Taheer yana jinsu…amma bazai iya bude baki ma yayi mgn ba…don haka yayi musu shiru…yanajin Nafisa nata Mata fada har suka karasa gida…bayan duk sun fito…Nafisa ta zagaya side din da yake…ta Mika mai atm dinshi tana murmushi tace”godia muke bro…Allah ya saka da alkhairi”…sai da yadan kakalo murmushi snn yace”bake nayiwa ba ai…’ya’yana nayiwa”..still dai tana dariyan tace”to ‘ya’yan naka ma sun gode..Bari mu karasa ciki”…Kai kawai ya iya daga mata…ita Kuma ta juya ta nufi cikin gidan… Al’ameen da Ramadhan suka dauki kayan suka bi bayanta dashi.
A hankali Layla ta kalleshi tace”daddy don girman Allah kayi hakuri…wlh it’s not my fault”…Saida ya watsa Mata wani kallo snn yace”ai it’s my fault tunda ni nace kisaka wnn kayan ki fita”…Yana gama fadan haka ya bude motan ya fita…batada zabin daya wuce ta fitan itama…don haka ta bude motan ta nufi gidan tana rusa kuka.
A parlor ta taradda su Nafisa…sun baje kayan da suka siyo su ummi na kalla…umma ce ta fara lurada ita tace”ke meye haka…Zaki shigoma mutane kina kuka?…Layla batace komai ba kawai ta wuce dakinta…Nafisa ta basu labarin abinda ya faru…ummi tace”don kyautawa bata kyauta ba…amma meye zai ringa hanata kula samari ko ance mashi bazatayi aure bane…Nafisa na kallon ummin tace”ummi ai ba cewa akai bazata kula samari ba…amma at least a fara neman izini tukun…ba mutunchi bane ta tsaya kula saurayi a waje”…a fusace ummi tace”to idan bata kulasu a wajeba…taya zaayi har su samu number dinta ko Kuma su San gidansu…idan bata kula samari ba sanyata a gaba zamuyi muyita kalla ko kuwa shi Wanda yake hanata kulasun zai aureta ne”…Nafisa dai shiru tayi donta fuskanci ummi bazata fahimcesu ba…umma kuwa dama shiru tayi tana sake sake cikin ranta.
Taheer tunda ya shiga daki bai sake fitowa ba sai asubah…Yana dawowa daga masallaci yai wanka ya shirya…ko cikin gidan bai shigaba ya tafi clinic abinshi…bai son ganin kowa a halinda yake ciki…don ya fuskanci zuciyarshi na gab da tona mai asiri.
Umma tun tana sa ran shigowan Taheer din har ta fitar da rai…har part dinshi taje taga a kulle…ta Kira wayanshi Kuma yaki yin picking…to me yake damun yaron nn ne?
8pm daidai umma tayi sallama parlon Taheer…jin shiru baa amsa ba sai kawai ta tura kofar bedroom dinshi ta shiga…Yana kwance rigingine a kan gado…yayi pillow da hannayenshi…idanunshi na kallon sama…da gani ba karamin zurfi yayi cikin tunani ba…Saida umma ta zauna gefenshi snn tasa hanu ta dan bugeshi…firgigit ya mike tareda zare ido yana kallon umman da baisan lokacin da ta shigo ba…haka nan yaji gabanshi ya Fadi ganin kallon da umman ke mai…ya Dan kakalo murmushi cikin in Ina yace”umma ai…ba…banji shigowanki…ba”…still umma na kallonshi tace”dama yaushe zakaji shigowana bayan kayi nisa cikin tunani”…bai sake cewa komai ba yai kasa da kanshi…saida umma ta daure fuska snn tace”dago idanunka ka kalleni mgn zamuyi”…ba musu ya dago idanun nashi ya kalleta…gabanshi ya sake faduwa ganin fuskarta a daure…wnn alama ne na mgnr da zasuyi mai muhimmanci ce…Saida umma ta dauke Kai snn tace”so nake ka fadamin tsakaninka da Allah Taheer me kake boyewa a cikin zuciyarka…ya dago da sauri zaiyi mgn ta daga mai hannu”kar kacemin ba komai don nasan karya kakeyi…yau bazan bar dakin nan ba sai naji damuwarka Taheer…sai naji abinda kaketa boyewa a ranka that’s weighing you down haka…kar kacemin mgnr biki ne don nasan it’s not…idan Kuma bazaka iya fadaba there are two things involved…ko ka sanar Dani abinda ke damunka…ko Kuma in fita harkanka for good…kar ka sake considering Dina as mahaifiyarka don daka daukeni uwa…bazaka boyemin abunda ke damunka ba…ko a hanya ka ganni kar ka nuna ka sanni Taheer don bazan taba kulaka ba…matukar baka sanar dani abinda nake sonji ba…to ka manta kana da wata kanwar uwa mai suna Aisha…ka manta akwai wani relation a tsakanina da Kai don zan yankeshi for good”…a gigice Taheer ya kamo hanunta Yana hawaye…ya shiga girgiza Kai yace”umma kar kiyimin haka plss…wlh bazan iya fadan abunda ke damuna ba…ko na fada umma ba amfani zaiyi ba..so it’s better kar in fada din…don Allah kiyi hakuri umma kar kice zakiyi breaking ties dani wlh mutuwa zanyi”…a hankali umma ta zame hanunta daya rike gam…tace”it’s ok tunda bazaka iya fada ba…but i want you to put this at the back of your mind…daga yau…bani ba Kai Taheer…ko a hanya ka ganni kamin mgn bazan kulaka ba”…tana gama fadan haka ta mike zata fita daga dakin…da sauri Taheer ya mike ya sake riko hanunta yace”umma na shiga uku…idan kikace haka umma wlh zan iya mutuwa…bazan iya fadan abunda ke damuna ba umma…zuciyata ta cuceni…kunya nakeji umma idan na fada zaku tsaneni”…ganin yanda yake kuka wiwi…umma ta kamashi suka zauna bakin gado…tayi cupping fuskarshi idonta har ya kawo kwalla sbd tausayinshi tace”look at me Taheer ba Wanda zai tsaneka…ba Wanda zaiga laifinka Taheer..don Allah say it…zakaji sauki a cikin ranka…the burden is too much for you…tell me son…I promise bazan ga laifinka ba and zanyi supporting dinka”…ya Dora hanunshi kan nata still yana hawaye yace”umma zuciyata batamin adalci ba…umma I…I…kmr zai fada sai kuma ya shiga girgiza Kai yace”umma am shy plss…bazan iya fada ba”…a hankali ta sauke hannayenta a fuskanshi tana kokarin mikewa ya rikota da sauri Yana cewa”am sorry zan fada umma…just don’t leave me plss”…umma na kallonshi tace”umhum Ina sauraronka”…a hankali yai kasa da kanshi yanajin yanda bugun zuciyarshi ke tsananta gudu kmr zata fito…ya dago ya kalli umma…ganin kallonshi itama take sai ya dauke Kai tareda goge hawayen da suka ki tsayawa a idonshi…cikin raunanniyar murya yace”umma I..I..i love…am in love….with…b..a..b..y”…ya fada words din a rarrabe…a hankali ya juyo da fuskarshi gareta…yanaso yaga reaction dinta…but sai yaga fuskanta normal…ko alamun mamaki ma babu…hannu umma tasa ta rungumeshi tace”why will you punish your self son…why did it take you so long to say”… Taheer wani dadi yaji ya lullubeshi…a hankali ya sauke ajiyar zuciya…at least umma bataga laifinshi ba…”am talking to you son…meyasa kaketa boyewa all this while baka fada ba”…ummi ta fada tana hawaye itama… seriously Taheer ya bata tausayi…ta tabbata Kuma ba karamin so yakema Layla ba…shima Yana hawayen yace”umma tsoro nakeji…ban taba tunanin zan samu support din kowa ba…snn inajin kunya umma yarinyar nn fa uba ta daukeni…she calls me daddy…ban San lokacinda son da nake Mata ya koma hakaba umma…zuciyata batamin adalci ba”…da sauri umma ta Dora hanunta Kan bakinshi tace”stop saying that…Allah ne ya Dora maka…and na tabbata duk duniya babu Wanda zaizo Layla fiyeda yanda kake sonta…so I will support you son…zan sanar da duk Wanda ya kamata ya sani…after all ba muharramarka bace so akwai aure a tsakninku”…wani irin sanyi Taheer yaji Yana sake shiga zuciyarshi…ya dade baiji heart dinshi very okay kmr yanzu ba…wato gaskyn umma ne da tace the burden is too much for him…umma ta riko hanunshi tana kallonshi tace”I want you to come back to your old self Taheer…ka ragema kanka wnn damuwan snn ka ringa cin abinci…I promise zanyi iya bakin kokarina kan mgnr amma sai naga ka dena damuwa..bikinka yau saura 10 days so ya kamata ka nustu ka maida jikinka snn ka dauki hutu wurin aiki cox you are going to be ango soon”…umma ta karasa mgnr da murmushi…lokaci daya Taheer yaji ranshi ya dan baci jin an ambaci bikinshi…ya rausayar da kai tareda kamo hanun umman yace”naji zan dena duk abinda bakiso umma…but plss ki fara tsaida mgnr auren nn tukun”…umma ta Dan wara ido tace”hope bada gaske kake ba koh”…Yana turo baki yace”da gske nake Mana umma…bana son auren nn wlh”…umma ta shiga girgiza Kai tace”kaima kasan wnn Kuma ba mai yiwuwa bane…tunda nace zan taimaka maka…ka hakura ayi bikin…nayi maka alkawarin InshaAllah Layla batada miji sai Kai”…wani irin dadi yaji ya sakeji a cikin zuciyarshi…””InshaAllah Layla batada miji sai Kai””wnn word yafi komai yi mai dadin ji…umma na kallon yanda yake blushing tace”bari in kawo maka abinci yanxu kaci…anjima sai mu karasa mgn…tun bata rufe baki ba yace”no mu karasa yanzu plss umma…ya gyara zama snn ya cigaba”umma kina ganin ummi zata amince kuwa…’yan uwan mahaifin baby suma kinaga bazaa samu matsala ta wurin su ba?…am scared umma nasan bai zama lallai su yadda ba”…idon umma na kanshi tace”why kake ganin bazasu yadda ba?…yace”umma sbd nayi mata girma…mum dinta mafa na girmeta umma nasan bazasu bani itaba”…ya kamo hanun umman ya rike yace”wlh umma idan ban auri baby ba mutuwa zanyi…duk ranar da akace an daura Mata aure da wani umma mutuwa zanyi na sani”…umma na girgiza mai Kai tace”ka Dena wnn tunanin and be positive…Ni nasan ba Wanda bazai yadda ba… Taheer you are a good man…ba Wanda bazaiso hada zuri’a dakai ba…ballantana Layla da kakeda iko a kanta…ko wani ka kawo kace kanaso ya auri Layla nasan duk Wanda kake tunanin bazasuki yadda ba..bare Kai da kowa ya shaida irin kaunar da kake Mata…Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai ni nasan me zanyi”…cikeda farin ciki Taheer ya rungumeta yace”thank you so much ummata…Allah ya Kara lfy da nisan kwana…Allah ya saka maki da gidan aljannah”…da murmushi itama umma ta amsa da ameen snn ta mike tace”Bari in kawo maka abinci”baice komai ba har ta fita Yana binta da kallo kawai Yana washe fuska kmr gonar auduga????he can’t believe yau shine ya fadama umma wnn mgnr…