Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Kitchen umma ta nufa direct…ta gama hada mai abinci a tray zata fita daga kitchen din sai ga Layla tazo daukan ruwa…umma na kallonta idanunta har sun kumbura sbd kuka…ta Mika Mata tray din hanunta tace”karbi ki kaima Taheer wnn…daga nan ma sai ki bashi hakuri”…ba musu Layla ta amsa tray din snn ta juya ta fita…gabanta har faduwa yake tasan sai ya Mata fada yanzu.

Yana nan zaune inda umma ta barshi…idanunta a kasa ta shigo dakin…shi Kuma Yana ganinta ya mike da sauri ya amsa tray din hanunta ya ajiye nan kasa snn ya kama hanunta ya zaunar kusa dashi…da mamaki sosae Layla ke kallonshi…itada take tunanin zai koreta yace ta bar mai daki sai taga akasin haka…what’s wrong with him?…a hankali ta dago ta kalleshi taga shima kallon nata yakeyi yana smiling… murmushi ta saki itama tace”daddy kayi hakuri plss…I promise bazan Kara ba”…still Yana kallonta yace”na hakura baby…yanxu zuba Mana abincin muci nasan kema bakici abincin ba”…ba musu ta durkusa ta shiga zuba musu abincin…tna gamawa ta janyo stool ta Dora abincin a Kai snn tace”na gama”…baiyi mgn ba ya dauki spoon ya Debi abincin ya nufi bakinta dashi…ba musu ta bude bakin ya zuba Mata abincin…haka yaita bata har Saida tace ta koshi…ya dauki drink ya bata shima Tasha snn ya rufe abincin…tana kallonshi da fara’a tace”daddy you are in a good mood today…what’s the good news?…wani murmushi ya saki Yana cewa”you guess right baby..am in a good mood..but bazan fada maki ba…it’s a surprise”…Layla ta turo baki tace”why daddy plss… remember am your baby fa… your friend…so bai kamata muna keeping secrets ma junanmu ba”…wani murmushin ya sake saki Yana shafa gemu yace”yes you are my baby…my friend…yai kasa da murya yanda bazata jiba snn yace”and you are my wife”…sake turo bakin tayi tace”then tell me daddy”…bakin data turo ya kama da hanunshi snn yace”I promise I will tell you amma ba yanxu ba”…tana kallon cikin idonshi tace”are you sure”…ya dauke idonshi da sauri snn ya daga Mata Kai…wasu electric abubuwa yaji suna transfer daga idonta zuwa nashi…ya sake juyowa ya dan kalleta sai kawai yaji ta sakala hannayenta a kafadanshi tace”am also happy daddy…tinda naga you are happy”… murmushi kawai ya saki snn ya mike yace mata”Bari inyi wanka”…tace”daddy bakaci abincin bafa”…ba tareda ya juyo ba yace Mata”Wanda kikaci ya ishemu..am not hungry”…Yana gama fadan haka ya fada bathroom…ita Kuma ta mike tareda tattara kayan ta fita dasu.

A bangaren hajiya umma kuwa..tun dazu tana daki tana tunanin Wanda ya kamata ta fara tunkara da wnn mgnr…ta dai San ko giyar wake tasha bazata fara tunkaran ummi ba don tasan rikici ne zaayi shi da ita…tafiso ma ummin ta zama itace ta karshe da zaa fadama mgnr.

Bayan ta gama tunane tunanenta…daga karshe dai tayi deciding ta fara sanar da Nafisa…inyaso ita Kuma ta sanar da mijinta.

Washegari…

Ganin ummi bata tashi da wuri ba…umma ta kira Nafisa dakinta tace”mgn nakeso muyi Nafee”…Nafisa na kallon umman tace”inajinki umma”…a nutse umma ta shiga Mata bayani…tun daga lokacinda ta fara zargin Taheer din son Layla yake.. har zuwa yanda sukayi dashi jiya…shiru Nafisa tayi tana jinjina al’amarin…ko kusa bata taba kawo wai soyayyan da Taheer kema Layla sone irin na aure ba…yanxu dama duk sbd Layla yayita zama yaki fidda mace yai aure…umma ta katse Mata tunani da fadin “kinyi shiru Nafee…ko bakiji dadin al’amarin bane?…da sauri Nafisa ta shiga girgiza Kai tace”ko kusa ba haka bane umma…kawai dai Ina mamaki ne da mutum kmr Taheer zaice Yana son Layla…na tabbata son da yake Mata ba kadan bane…na kuma san da kyar idan Layla zata samu Wanda zai sota kmrshi…nidai indai ta bangerena ne umma bani da matsala wlh…na amince ???? Allah ya tabbatar da alkhairi…cikeda gamsuwa umma tace”yawwa Allah miki albarka…yanxu ki dauki waya ki Kira Awwal ki sanar dashi”…Nafisa na girgiza Kai tace”idan ke kika kirashi sai yafi daukan abun serious…umma ta danyi shiru tana tunani sai Kuma yace”to mikomin wayata gata nan a bayanki”…Nafisa tasa hannu ta dauki wayan a bayanta snn ta mikama umma…nan da nan umma ta lalabo number Awwal ta shiga dialing dinta…cikin ranta tana addu’a Allah sa bazaa samu matsala a bangarensu ba… ringing biyu yai picking da sallama yace”umma barka da safiya”…umma ta amsa da”barka dai Awwal ya Karin hakuri Kuma??yace”Alhamdulillah umma ya shirye shirye”…itama tace”Alhamdulillah Awwal dama inaso muyi wata mgn ne”…yace”to Ina sauraronki umma”…a hankali umma ta shiga mai bayani shima…tun daga farko har karshe…yai shiruu a daya bangaren Yana sauraren abinda take cewa…Saida umma ta gama snnn tace”naji kayi shiru bakace komai ba”

Tofa anzo wurin????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

19

Jin yayi shiru umma ta sake cewa”Hello”…da sauri yace”eh Ina jinki umma…wnn ai abin farin cikine umma baima kamata a tambayeni ba…kunada iko da Layla tamkar yanda nakeda iko da ita…zanyi mgn da Alhaji duk yanda mukai dashi I will let you know…nasan InshaAllah ma bazai ki amincewa ba…Allah ya tabbatar da alkhairi…cikeda farin ciki umma tace”shknn na gode sosae son Allah yayi Albarka…ya amsa da Ameen Ameen Umma..duk yadda mukai da Alhaji zan kiraki”…umma tace to Ina sauraronka..Allah ya jishemu alkhairi…tana ajiye wayan ta dubi Nafisa da tsantsar farin ciki tace”yace duk yadda sukayi da mahifinshi zai kirani”…Nafisa tace”nasan ma bazai ki amincewa ba”…umma tace Allah yasa”…Nafisa ta danyi shiru for some secs snn tace”amma umma wa zai fadama ummi”…umma tace”so nake naji yanda sukai da mahaifin nashi…idan sun amince zan kira Uncle din Taheer in sanar dashi…shi Kuma sai ya kirata ya fada Mata…nasan dai da kyar idan baayi rigima da itaba amma komai mai wucewa ne..

A bangaren Taheer kuwa…he’s eager yaji amsan da umma zata bashi…tace she’ll talk to duk Wanda ya kamata…and hakan yana nufin har ummi knn…Saida gabanshi ya fadi daya tuna ummi fa bai zama lallai ta aminceba…Karan shigowan text a wayshi ya dauki hankalinshi…ya dauko wayan ya duba tareda sakin murmushi yace”Alhamdulillah”..snn ya mike zuwa part din ummi…Nafisa ce zaune kadai a parlon sai hibba dake jikinta…wata irin kunya da bai san yanada itaba..yaji ta kamashi…zuwa yanxu yasan dole taji mgnr…duk sai ya daburce kmr ya fita daga dakin haka yakeji…Nafisa na kallonshi ta lura kmr kunyarta yakeji…sai tayi murmushi tana cewa”hope dai ba kunyana kakeji ba bro”…Taheer yayi diff…kmr ruwa ya cinyeshi…wai yau shine kejin kunyar Nafisa..his younger sister…ko da yake ai dole ma yaji kunya…shi kanshi duk ya tuna cewa Laylan da yake mutuwar so fa diyar qanwarshi ce sai yaji kunyar kanshi…kwamacala knn????yana in Ina yace daita”what kind of kunya Kuma?…you know ba haka bane.. it’s just that ban kula dake a wurin ba”Yana gama fadan haka bai jira jin me zatace ba yasa Kai ya fice…Layla ta fito daga dakinta da sauri…tana kallon Nafisan tace”Mami kmr naji muryan daddy yanxu a parlon nn…I want to talk to him”…Nafisa da har yanxu bata bar murmushi tana mamakin sudden change din Taheer din ba tace”yanxun nn ya fita”…Layla bata sake cewa komai ba ta bi bayanshi da sauri…Yana dab da shiga part dinshi ta sameshi…bata mai mgn ba Saida ya bude parlor ya shiga snn ta shiga itama…ya zauna Yana kallonta yace”so kina bayana knn”…tace”yes daddy I want to talk to you”…”alright am all ears”…ya fada yana gyara zamanshi…Layla tace”daddy naji kmr ance post ume result dinmu is out fa”…yasa hanu yai cupping fuskanta…Saida ya manna mata peck a goshi that last for 2-3 mins snn ya daga idonshi a kanta yace”da gaske ne ya fito baby..and you’ve made it…I mean kinyi passing”…Layla ta zaro ido tanajin good news…kawai tai hugging dinshi tight tana fadin”am so happy daddy”…Yana shafa bayanta shima yace”am happy for you too baby…now tashi muje in sayo maki gift”…ta dago tana kallonshi excitedly tace”da gaske daddy?..yace”yes tashi”…ba musu ta mike…ya kama hanunta suka fita daga parlon…tace”daddy zan dakko hijab Dina”…yace”no get into the car…zamu siya a can”bata sake mgn ba ta bude mota ta shiga tana mamakin wai yau daddy ne yace ta shiga mota bako hijab..what has came over him?…shima shiga motan yayi…harga Allah yasan inta koma ciki zatace fita zaiyi da ita…shi Kuma yanxu kunya yakeji…bai taba sanin yanada kunya ba sai yanxu…so it’s better su fita a haka tunda she’s decent and motan nada tint…
Saida ya fara tsayawa ya sai mata very long hijab ready made daya Kai Mata har kasa…snn ya koma cikin motar ya bata…tasa..snn yaima motan key…suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button