Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Ummi na ganin Layla ta shiga daki ta shiga bin umma da Nafisa da mugun kallo…cikeda bacin rai tace”yanxu Aisha abinda kikayi kin kyauta knn…kin kyauta da kika goyi bayan Taheer akan wnn ta’asar da yake Shirin aikatawa…kinyimin adalci knn Aisha”…a hankali umma ta taso daga inda take ta zauna kusada ummi…a tausashe tace”don Allah kuyi hakuri Yaya…nasan idan na fara fada maki bai zama lallai ki amince bane…amma Yaya Taheer Yana son yarinyar nn…Yana sonta fiyeda yanda zakiyi tsammani Yaya…Yana ta azabtar da kanshi kan abinda ba Haram bane aikatashi…yanata boyewa ne Yaya sbd yasan bai zama lallai ya samu support dinmu ba…don Allah yaa kiyi tunani a kan wnn al’amarin…kiyi tunani da kyau Yaya…nidai banga aibu a yin auren nn ba…Saida umma tayi shiru snn ummi tana dubanta tace”kin gama”…a sanyaye umma ta daga Mata Kai alaman eh…ummi taci gaba”to wlh duk abunda akuyi bazan Bari ayi wnn ta’asar Dani ba Aisha…ta maida kallonta ga Nafisa tace”kema sbd bakida hankali baki San inda ke maki ciwo ba…shine kika goya musu bayan a dauki Layla ‘yar mitsitsiya a bama wnn zabgegen mutumin…mutuminda da yayi auren wuri zai haifi kmrta…salon yaje ya kasheta koh?…to Baku isaba wlh…duk kunyi kadan…ai nike gaba daku gaba dayanku…shima Taheer din ai bazai dawwama a wajeba…zai dawo gidan nn ya sameni sai naci nutuncinshi wlh”..ummi ta karasa mgnr tana hucii…daga umma har Nafisa dai ba Wanda yace takk…sun San hakan zata faru dama.

Taheer ko Yana fita Kai tsaye ya wuce office din Yusuf..cikin ranshi yanata addu’a Allah yasa ummi bazata ki amincewa ba…idan ummi tace bata yadda ba yasan for sure zai iya mutuwa…yanda yake son Layla gani yake wlh indai bai aureta ba…to duk ranan da akace ta auri wani mutuwa zaiyi for sure…he can’t stand seeing her with another…he just can’t…yana kishinta fiyeda tunani…yana Kuma yi mata sonda har ya koma ga Allah baya tunanin akwai halittar da zaiso a doron kasa bayan ta.

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

20

Yana isa office din Yusuf yayi parking nan waje..snn ya shiga ciki…Yusuf dake cike wasu files ya dago yana dubanshi snn yace”maza yau Kaine a office dina Kuma”…Taheer ya nemi wuri ya zauna snn yace”is that how to welcome a guest”…Yusuf yai dariya tareda ajiye pen dake hanunshi yace”ko ba guest ba…to Kai ba guest bane a nan”… murmushi kawai Taheer yayi snn ya gyara zama yace”guy you know what?…da sauri Yusuf ya girgiza kanshi yace”bani insha my friend…angon Sameera”…Taheer yadan yatsine fuska jin ya ambaci Sameera snn yace”mafarki na ya kusa zama gsky…am soon going to get married to the love of my life”…ya karasa mgn da murmushi…Yusuf ya danja tsaki yace”na sani Mana guy…yau saura kwana nawa ma?…wani harara Taheer ya maka mai kafin yace”meyasa baka ganewa ne wai…cewa fa nayi..am going to get married to the love of my life ba Sameera kaji nace ba”…Yusuf ya Dan bude idanu snn yace”maza ka sake batar Dani fa…just go straight to the point”…tsaki Taheer yaja snn yace”to kwanan nn zakaji na auri baby”…Yusuf ya wani zare ido kmr Wanda yaga abun tsoro snn yace”guy are you for real…I mean anya kuwa bakaci Kai ba?…Taheer ya saki dariya snn yace”kafa naci ba kai ba…kana nan zaune zan kawo maka ita har gidanka bayan munyi aure”… Yusuf da mamaki ya kasa barinshi ya mike daga inda yake ya dawo kujeran dake kusada Taheer ya zauna snn yace”maza fada min yanda akai pls..how comes…ya akai kayi convincing ummi and everyone”…ba bata lokaci Taheer yamai bayanin duk yanda sukayi da umma…wani irin ihu Yusuf ya saki yana cewa”mutumina baka da dama wlh…yanxu ba kunya saika auri ‘yarka kace zakayi rayuwar aure da ita koh”…Taheer yace”mind you..ba ‘yata bace…Mata tace”… Yusuf ya sake sakin wani dariyan yace”ai dole kace ba ‘yarka bace yanxu…tunda kana sa ran aurenta…Shege Kanata yaudaran mutane da wani baby..baby..nan ko baa san kaunar aure kake Mata ba”…tsaki Taheer yaja snn yace”pls be serious Mana Yusuf…ban son irin wnn wasan”… Yusuf ya tsaida dariyan da yake snn yace”ok ok am sorry friend…yanxu ka fasa auren Sameera knn?…Saida Taheer ya Dan tabe baki snn yace”sunce tunda an riga anyi mgn wai dole sai na aureta”… Yusuf na gyada kai yace”so yanxu ka yadda da Sameeran knn?…Taheer yace”idan ma ban yadda da ita ba Yusuf ya zanyi…sunce saina aureta snn zaa bani baby ba yadda na iya ai…dole zan aureta ko banaso”…Yusuf yace”idan na fahimceka knn kana nufin…ka auri Sameera yanxu..bayan wasu shekaru Kuma sai ka sake auren Layla abi”…Taheer ya girgiza Kai da sauri yace”wani irin bayan wasu shekaru…tabbb..ai bana tunanin ma zan Kai shekara daya nan gaba ban aureta ba…kana nufin in barta knn tayita zuwa school salon wani ya ganta ya makale Mata koh”… Yusuf na zare ido yace”kaifa kace bazaka yi Mata aureba sai ta kusa gama sch…shine yanxu zakace bazaka Kai shekara daya ba”…a dan fusace Taheer yace”that doesn’t matter… everything has changed now”… Yusuf yai Dan dariya snn yace”dole kace it doesn’t matter mana tunda Kai zaka aureta…ni mamaki kake bani wlh”…Taheer ya saki murmushi yace”bazaka gane bane Yusuf…I love her…da kasan yanda nakeji akanta da duk bazakayi wnn mgnr ba wlh…ko shekaran ma I don’t think zaa Kai ban aureta ba coz am eager you know…I can’t wait”…Yusuf ya shiga girgiza Kai Yana dariya yace”mugu…ka gama gane musu yarinya snn kazo ka aureta…duk ba abinda baka saniba a jikinta”…tsaki Taheer yaja tareda daukan car key dinshi ya mike tsaye…Yana kallon Yusuf Rai a Dan bace yace”matsalana dakai knn wlh…Dan iska ne Kai…ya zaayi ka wani ce nasan komai a jikinta sai kace wanka nake sata a gaba ina mata”… Yusuf bai Dena dariya ba yace”yo na nawa Kuma…ai saidai kar a kuma”…Taheer bai sake cewa komai ba kawai ya fice daga office din…baiga amfanin mgn da wnn Dan iskan ba…da sauri yusuf yabi bayanshi yace”sorry doctor…wasa nakeyi wlh…pls come back akwai mgnr da nakesonyi da Kai…Taheer yai mai banza yaci gaba da tafiyarshi…sai da kyar Yusuf ya lallabashi suka koma ciki.

A can gida kuwa ran ummi idan yakai dubu to ya baci…tun dazu take Kiran wayarshi switch off…wato ma Yana sane ya kashe Mata waya…to ya gama duk guje gujen nashi zai dawo gida ya sameta.

Taheer bai dawo gidaba Saida ya tabbatar duk sunyi bacci…Kai tsaye ya wuce part dinshi shima ya kwanta.
Da asuba dama kafin ya fita masallachi Saida yai wanka ya shirya…ana idar da sallah bai koma gidan ba ya wuce clinic..shi kanshi yasan wnn gudun da yake kara tunzura ummi zaiyi but he have no choice…gaba daya tsoronta ma yakeji.

4:30 pm akayi knocking office dinshi..ya bude idanunshi da suke lumshe..a hankali yace”come in”…umma ta bude kofa ta shiga ciki…da mamaki yake kallonta kafin yace”umma kece”…ta karasa ciki ta zauna snn tace”nice mana”…Taheer ya shiga Sosa Kai yana cewa”I never expect you umma…daga gida kike?..ta girgiza Kai tace”daga gidansu matarka muke…munje munkai lefe nace suyi dropping dina a nan…wato bazaka dauki hutun ba dai koh”…yace”zan dauka umma sai gobe”…umma ta tabe baki tace”yanxu Taheer kana ganin wnn guje gujen da kakeyi shine zai sa Yaya ta amince da mgnr nn…baka ganin wnn abun Kara bata ranta ma zaiyi koh”…a hankali Taheer yace”na sani wlh umma…but I have no choice…tsoron haduwa da ummi nakeji wlh…Ina tsoron jin abinda zai fito daga bakinta”…umma na girgiza Kai tace”duk da haka wnn ba solution bane..yanxu inaso ka biyoni muje gida..Kuma duk abinda Yaya zata ce karka sashi a rai ya dameka…nasan yanda zanyi InshaAllah…indan Kuma kanaso in zare hanuna a lamarinka sai kaita zama kar kazo muje gidan”…Taheer ya mike da sauri yace”kiyi hakuri umma…let’s go”…itama batayi mgn ba ta wuce suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button