Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Taheer…
Kusan 2 hours sukai spending kan matar kafin su gama,Yana fitowa direct office dinshi ya nufa gaba daya hankalinshi na kanta,,koda yaji office din a rufe gashi duk wayoyinshi na ciki,wata nurse ya samu yace ta Kira mai sister Sara ba bata lokaci saiga Sara tazo,yace kicema baby na dawo ta kawomin key”cikeda girmamawa tace ai batazo wurina ba sir Amma bari in duba office din Dr Salees,,har ta fara tafiya ya dakatar da ita yace u mean tun dazu tana tare dashi knn?..No sir am not sure kawai dai nasan tinda batazo wurina maybe sun hadune shine taje office dinshi ya firzar da iska snn yace it’s okay u can go bari in duba da kaina ta amsa mai snn ta juya ta tafi shi Kuma ya nufi office din Dr Salees din,,,tun daga bakin office din yakejiyo dariyarta snn ga mgn nn kasa kasa yana jiyowa,wani irin bugawa zuciyarshi tayi yai saurin dafe kirjinshi tareda jingina a jikin bango,,ya Kai kusan minti 3 a haka kafin ya bude kofan ko knocking beyiba,,tana zaune kan 2 seater dake office din shi Kuma Yana zaune dirshan a kasa yana facing dinta ya wani sunkuyo Yana mata mgn a hankali ita Kuma tana murmushi,,wani irin jiri yaji ya daukeshi yai saurin dafa bango still daya hanunshi dafeda kirjinshi,,jin motsin
mutum yasa gaba dayansu suka juyo Layla da sauri ta karaso inda yake tace daddy what’s wrong are u okay?yai kokarin daidaita kanshi fuska ba walwala yace bani key”ta koma inda key din yake da sauri ta dauko kafin ta juyo har ya fita a office din tabi bayanshi da sauri ba tareda ta dauki wayanshi data bari nan ciki ba,,,a kofar office dinshi ta sameshi ta karasa ta bude office din tana kallonshi kafin tayi mgn ya shige ciki ya barta nan tsaye,jiki a sanyaye ta shiga itama,Yana kwance kan 3 seater sai yanxu ya cire hanunshi dake dafeda chest dinshi idanunshi na kallon sama,,tana kokarin zama kusa dashi yace”Don’t u dare”ba da karfi yai mgnr ba Amma a yanayin daya fada tasan ba karamin bacin rai yake cikiba,,tai saurin matsawa baya jikinta na rawa sai kawai ta durkusa a wurin tafashe da kuka,,ya runtse ido baya son jin kukan nn Sam,,har ynxu zuciyarshi bata dawo normal ba,,ya mike zaune Yana kallonta da idonshi daya sauya kala yace where is my phone?ta share hawayen idonta ta mike zata fita yace Ina zakike Kuma?ta juyo tana kallonshi tace zanje in dauko wayan ne,na barshi a can,,,ya mike zuwa table dinshi ya Kira messenger yace ya dauko mai wayan snn ya koma ya zauna,,bayan 2 minutes messenger ya kawo mai wayan ya dau keys dinshi Yana kallonta yace muje”ba musu ta shiga gaba Yana bayanta suka fita daga office din,yai locking snn suka shiga elevator,,sai share hawaye take tana sheshsheka a hankali.
Ko staff dinshi dake mai Allah ya kiyaye hanya yau bai amsa su kmr yanda ya saba ba ya shiga mota kawai itama ta shiga suka fita daga clinic din,ko a cikin mota sai Satan kallonshi take tana share hawaye duk yana lurada ita amma baiyi mgn ba,yasan indai zata cigaba da kukan nn to raunana mai zuciya zatai shi Kuma yafison yanuna Mata abinda ta aikata na daidai bane,da wnn tunanin ya isa gida ko ciki bai shigaba yai parking idonshi a kan hanya yace “shiga gida”ta juyo tana kallonshi idanunta duk sunyi ja tace daddy pl…bata karasa ba ya katseta ta hanyar daga Mata hanu tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya ya sake cewa ki shiga gida mana u’re weting my time,,a hankali ta bude motan ta fita ko kullewa batai ba ta shiga gida da gudu,,ya kwantar da kanshi kan starring motan yana jan numfashi,yafi minti 4 a haka kafin yaja motan ya koma clinic.
Don Allah kuyi hakuri da errors da zaku gani ban samu nayi editing bane but zaa gyara InshaAllah.thank u all.
And please kuyi following Dina a Wattpad@ummuashraf22 sannan kuyi voting????
Mum Ashraf✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf✨
Wattpad@ummuashraf22
02
Koda ya koma clinic din gaba daya kasa aikata komai yayi duk zuciyarshi ba dadi,dama shi haka yake indai ranshi ya baci to gaba daya al’amuranshi tsayawa suke,ya mike kawai ya dau car key dinshi ya fita,ya shiga mota ya bar clinic din,Saida ya hau titi snn yai dialing number da yayi saving da”Friend”a wayarsa ya sa a speaker ya ajiye wayan kan laps dinshi yana cigaba da tuki,a daya bangaren akai picking da sallama,bayan sun gaisa yace Yusuf wai har yanxu baka dawo bane?Wanda ya kirada Yusuf din ya amsa da”na dawo jiya da dare wlh”banyi niyyan kiranka ba kawai da yamma zanje in gaida ummi sai in biyo ta office dinka”ya sauke ajiyan heart snn yace “ynxu kana Ina?”at home,anything for me?yace ok gani nn xuwa bai jira abunda zaice ba ya kashe wayan snn ya dauki hanyan dazai kaishi
gwarinpa inda gidan abokin nashi yake,,tafiyan mintina kalilan ya kaishi gidan ya har ciki ya shiga da mota yai parking Amma bai fitoba ya shiga dialing number Yusuf din,shima baiyi picking call dinba ya fito Yana sanyeda ash jallabiya,ya karaso wurinshi da murmushi a fuska yace “welcome bismillah muje ciki,Taheer yace no ba sai na shigaba kawai kace ina gaida madam da yara,Yusuf ya wani zare ido yace are u for real?kazo har cikin gidan nawa ka wanice bazaka shigaba ai kaima kasan wasa kakeyi wlh,bai sake cewa komai ba ya bishi suka shiga ciki,,nabila matar Yusuf ta cika masu gaba da kayn ciye ciye snn ta zauna suka gaisa da Taheer tace yasu ummi da Layla?yace suna nn lfy wlh,, madallah ace muna gaishesu pls muna nn shigowa InshaAllah,yace ba damuwa Allah ya kaimu,nan ta mike ta bar musu parlon,,Yusuf ya kalleshi da kyau yace to Ina jinka meke faruwa?ya Dan kalli Yusuf din da mamaki kafin yai mgn ya sake cewa tunda na ganka a haka nasan for sure akwai abinda ke damunka,,ya sauke numfashi kafin yadanja siririn tsaki yace baby ce wlh”wace babyn?ya juyo yadan harareshi kafin yace wace mace nake kirada baby idan ba Layla ba,ohk what about her?wani tsakin ya Kara ja yace could u imagine wai yarinyar nn na gani da wani student doc a clinic daxu ya wani sata gaba a office dinshi yana Mata surutu ita Kuma sai dariya take mai,har office dinshi fa ya kaita sbd bashida
hankali,wlh badon nakai zuciyata nesa ba da korashi zanyi daga clinic dina don bazan dauki iskanchi ba wlh,,Yusuf Saida ya bari ya gama mgn snn ya gyara zama yace”so har ynxu kana nn a yanda na sanka knn,fisabilillahi Taheer kanama kanka adalci knn?duk kabi ka dorama kanka abinda kaima kasan ba me yiwuwa bane…a fusace Taheer dake kallonshi yace “mene rashin yiwuwan nashi wai,meyasa kakemin haka ne for God sake,idan bazaka tayani son abinda nakeso ba bai kamata ka ringa kokarin discouraging dinaba gsky,,Yusuf yai shiru ganin yanda yake mgn rai a bace,sai kuma yai Dan kasa da murya yace”ba haka nake nufiba Friend,ya kamata ka fahumceni,Ina guje maka abunda zai jefa rayuwanka cikin wahala ne,kaga dai na farko yarinyar nn kallon uba take maka mahaifi ya kake tunanin zakazo Mata da mgnr SO ta yadda bayan ita ba wnn kallon take maka ba,na biyu Kuma iyayen yarinyar nn,kaga sunyi maka Kara iya Kara a kanta suka dauketa tun tana karama suka baka kuma basu taba nuna maka wai sunfika iko da itaba,hatta ‘yan uwan mahaifinta ba Wanda yake nuna mka Kai din ba ubanta bane to ta yaya kke tunanin zakazo musu da mgnr kana son aurenta su yadda,dukda addini bai hanaba Amma gsky wnn abune mai kmr wuya, beside yarinyar nn qarama ce Taheer mgnr gsky yarinyan nn tayima qanqanta,ga babes nan Wanda suka amsa sunan babes suna binka kmr zasu ma sujada, matured,amma ka tsaya zaka bata lokaci akan ‘yar cikinka, ya kamata ka tsaya kayi tunani Taheer kasan abinda kake ciki,yanxu ka gwammace kayita zaman jiran abinda bakada tabbas din