Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Da daddare Taheer ya shigo dakin ummi as a result of kiranshi da tayi…ya nemi wuri ya zauna kanshi kasa…ummi na mai mugun kallo tace”Ni dai kayima haka koh Taheer…nida na tsugunna na haifeka ban isa ince kar kayi abu ka Bari ba knn…sbd tsabar son Kai Taheer kaje ka hada baki da mutane…saura yan kwanaki bikinka…kasa suka shiga suka fita Saida sukasa aka baka auren ‘yar nan..yanxu Dan Allah bakaji kunyaba Taheer..ace ‘yar cikinka zaka aura.. Layla cefa Taheer..wai meya hau kanka ne these days…to Bari kaji in fada maka..idan ma kana tunanin ni zan dauki Layla in baka wai a matsayin Matarka you are mistaken wlh…yadda kasa aka daura maka aure da ita bada sanina ba..itama bada saninta..haka zan sanya ka saketa ko kanaso ko bakaso…Bari a gama bikin naka ka gani…zakusha mamaki na wlh”…Saida ummi tayi shiru snn a hankali Taheer yace”wlh ummi Ni kaina I have no idea of daurin auren nn da akayi..ban San komai akai ba wlh ummi.. believe me..kawai kirana uncle yayi yace an daura Mana aure but wallahi bani na nemi ayi hakan ba…dn Allah ummi kiyi hakuri ki dena fushi Dani..duk abinda kikeso zanyi amma ummi dn Allah kar kice zaki rabani da baby…I can endure duk wani punishment daga gareki just don’t seperate the two of us plss..I beg you”…tsaki ummi taja tana hararanshi ta nuna mai kofa tace”tashi ka barmin daki malan…bani da lokacinka yanxu..ka Bari a gama bikin nn..sai na baka mamaki wlh”…bai sake cewa uffan ba ya mike ya fita daga dakin hoping he can see Layla ko sau dayane…Amma har ya fita ko motsinta baiji ba…yasan yanxu tana can hankalinta a tashe…maybe ma duk duniya babu wanda ta tsana kmr shi..he is suppose to be happy Layla is now he’s but he is not happy with how things are going at all..he really wants to see situation din da take ciki a yanxu…yasan for sure tana can tana kuka and da kyar idan batayi developing fever ba zuwa gobe…on the other hand Kuma Yana tunanin aurenshi da Sameera…yasan for sure idan ya aureta bazata tabajin dadinshi ba cox baida interest a kanta..that aside ma duk duniya baijin akwai macen da zai hadata da Layla Kuma yayi tunanin yin adalci a tsakaninsu…he can’t…son da yake mata is different..dole ya nemi way out kafin lokaci ya kure mashi and he has only one way out..
Washegari…
Karfe 4 daidai yayi sallama parlon ummi…uncle dinshi ne zaune a parlon..sai umma da ummi…kallo daya zakai musu kagano tsantsar bacin ran dake shimfide kan fuskokinsu…a hankali ya karasa ya zauna..bai yadda ya hada ido da kowa ba…ummi ta mike ta iso inda ya zauna din…ta daga hannu kawai sai ji yai ta wankeshi da Mari…cikin hawaye ta fara mgn”mu zaka wulakanta Taheer…ka nuna ma duniya bamu isa dakai ba…meya shiga cikin kanka da zaka aikata abunda kayi…sbd bakada kunya Taheer ka taka kaje har gidan su matar da zaka aura…kayi sallama da mahaifinta Taheer ka kalli tsabar idonshi kace mai ka fasa auren ‘yarsa..sbd kawai kana takama an aura maka yarinya karama da bama sonka takeyi ba…yaushe ka zama mutum mai son Kai haka…yaushe ka zama mara Imani ban saniba”…Taheer dake dafe da kuncinshi da ummi ta wanke da mari…yai tsitt…dama yasan hakan zata iya faruwa so he’s not shocked…uncle dinshi na kallonshi yace”ba mgn akeyi maka ba kayima mutane shiru”…Taheer da kanshi ke kasa har yanxu yace”don Allah kuyi hakuri uncle…Ni banyi haka don in bata muku rai ba…ko na aureta uncle ba dadin zama Dani zataji ba tunda bana sonta…Kuma ni gsky Ina gujema daukan alhakinta ne…babu macen da zan iya hadata da Layla Kuma ince zan iya adalci tsakaninsu…Allah ya sani nasan bazan iya adalcin ba shiyasa naje kawai na sanar da mahaifinta… snn ubangiji ma da yace mu auri mace fiyeda daya Saida yace idan mun San zamuyi adalci..ni Kuma nasan I can not shiyasa naga it’s better a fasa auren kan in aureta Kuma inzo Ina daukan alhakinta”…har Taheer yai shiru binshi kawai suke da kallon mamaki…uncle dinshi na gyada Kai yace”wonderful..ka aikata abinda kake so Taheer muma kuma yanxu zamuyi abinda mukeso…you deserve punishment kan abinda ka aikata..and do you know punishment daya kamace ka?..a hankali Taheer ya girgiza Kai alaman he don’t know…uncle dinshi ya sake sakin smile yace”badai takamarka ka samu Wadda kake so shiyasa kace ka fasa auren waccan ba…to ita wnn da kakeson ai karamar yarinyace dama..don haka bazaa baka ita ta tare matsayin Matarka ba har sai ta kammala karatunta”….a firgice ya dago Kai Yana duban uncle din nashi…sai Kuma ya shiga girgiza Kai idonshi har ya kawo kwalla yace”uncle don’t do this to me plss…wlh mutuwa z…bai karasa ba ummi ta bige mai baki…ya matsa daga kusa da ita da sauri yace”don Allah kar kumin haka uncle…ku tausayamin plss”…uncle dinshi dake kallonshi Yana murmushi yace”ai na gama mgn Taheer..ba dai mu kaje ka kunyata a idon iyayen yarinyar nn ba?…da sauri Taheer yace”na fasa uncle..wlh na hakura..zanje in samu dad din nata in bashi hakuri..Kuma kuyi hakuri plss”…ba Wanda yace mai kala…ya sake karya murya yace”uncle medicine zata karanta fa…for how long zanyita jiranta uncle har saita kammala karatu”…cikeda takaici ummi ta cillo mai pillow dake gefenta tace”tashi kaba mutane wuri fitsararren banza da wofi…har wani for how long kake tambayan mu sbd bakada nutsuwa”…Taheer ya mike zai fita sai ya kalli umma wai ko zata sa baki..amma sai yaga ta dauke kanta gefe…jikinshi a sanyaye ya fita…yasan tunda tai haka bazatai mgn ba knn…yasan itama bataji dadin abinda ya aikata ba…shi da kanshi yasan what he did was wrong Amma to ya zaiyi.
Daren nn ko runtsawa Taheer baiyi ba…sai kullawa yake Yana kuncewa…gaba daya abubuwan sunzo mai a baibai…yanxu tsakani da Allah for how many years zaiyita zaman jira idan akace Layla sai ta gama karatu… medicine fa…ya zama dole ya nemawa kanshi mafita if not yana zaune wankin hula zai kaishi dare…umma is his only hope…itama Kuma yaga alaman bataji dadin abinda ya aikata ba..but it’s not his fault..harga Allah shi yana gujewa kanshi azabar da ubangiji ya tanada wa mazan da suke banbanci tsakanin matansu ne…snn itama yana guje mata bacin ran miji ya fifita kishiya a kanta…yasan shi ba adali bane when it comes to baby shiyasa ya aikata abinda ya aikata din…amma haka nn zaiyi folding hands yana gani su hanshi matarshi..Anya zai iya kuwa?
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
22
The following day Layla ta tashida zazzabi mai zafi…ummi duk ta rikice ta rasa yanda zatayi da ita…dama duk take rashin lfy to Taheer ne mai jinya…shi zaiyi Mata komai ita ummi saidai dan abinda baa rasaba…gashi sai kuka take Mata anyi anyi tayi shiru taki…dama shi kadai ne ya iya handling dinta gashi kuma yanxu wnn abun ya shigo tsakani…tun dare take ayyana ko kiranshi zatayi ya dubata sai wata zuciyar Kuma ta hanata…ganin dashi ta kwana ummi ta yanke hukunci suje asibiti kawai…ta riko hanun Layla suka fito daga dakinta…Nafisa na tsaye tana jiransu…hanunta rikeda car key..sai umma dake parlor itama tana jiransu…ummi na rikeda ita suka fita daga parlon.. Mama hawwa kadai suka Bari a gidan zata kulada yara…
Suna fita Taheer na fitowa daga part dinshi…ya bisu da kallo ganin zasu shiga mota..cikin ranshi yana tunanin Ina zasuje haka…bai San lokacinda ya nufi inda suke da sauri ba har Yana dan hadawa da gudu…ganin yanda ummi ke rikeda Layla kadai ya san cewa something is wrong…daidai ummi ta sata a mota..tana kokarin shiga itama kawai ta ganshi a gabanta…yana shafa kai yace”am…umm..me..me yake…damunta..ummi?…wani kallo ummi ta zabga mai tareda jan tsaki tace”bani wuri in wuce”…ya rausayar da kai tamkar zai Mata kuka yace”ummi don Allah me yake damunta…kawai fadamin zakiyi sai in baki drugs ki bata”…ummi murmushin takaici ta saki tana kallonshi tace”you have some nerves…bazaka bani wuri in wuce ba saina gaura maka mari a wurin…waye ya ja Mata ciwon idan ba Kai ba..ka saurari haduwa na dakai bazaiyi maka kyau ba wlh…now bani hanya in wuce”…a hankali ya sake cewa”ummi to at least ko hijabi a bata tasa mana..bai kamata taje wani wurin da wadan nn kayan ba”…ganin kallonda ummin kemai bai sake cewa komai ba ya matsa Mata ta bude motan ta shiga…Yana tsaye yana kallo Nafisa taja motar suka fita daga gidan…da sauri ya nufi tashi motar shima ya shiga..yai Mata key snn ya bi bayansu.