Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Daren ranar har ya kwanta yaga ba iya baccin zaiyi ba..sai ya mike zuwa part din ummi…ganin parlon ba kowa sai ya nufi dakin umma…tana kwance kan gado amma ba bacci takeyi ba…ya karasa ya zauna kusada ita sai ya kasa cewa komai…he really don’t know from where to start…umma Sarai taji shigowanshi amma tayi kmr bataji ba…a hankali ya matso dab da ita..yasa hannu ya kamo hanunta ya rike gam cikin nashi…hawaye na sauka kan fuskanshi ya fara mgn”umma don Allah kiyi hakuri ki dena fushin nn Dani..I know I have wronged all of you amma umma it’s not my fault…umma ke shedace na irin sonda nake ma baby…ko nace zanyi adalci tsakaninta da Sameera wlh ba iyawa zanyi ba…bazan taba iya daidaita son da nake Mata dana wata mace a duniyar nn ba umma…shiyasa nayi haka amma dn Allah ki tausayamin kiyi hakuri plss”…sai ya kife kanshi kan hanunta dake cikin nashi ya shiga kuka a hankali…umma ta mike zaune…jikinta duk yayi sanyi..Allah ya sani dama ba karamin tausaya mishi takeyi ba…yanxu daya zauna gabanta yana kuka sai ya sake bata tausayi…ta zare hanunta daya rike snn a hankali ta shiga goge mai tears din tana girgiza mai Kai alaman yayi shiru…Taheer ya sake rike hannayenta yace”umma don Allah kiyi hakuri”…ta Dora kanshi a kafadanta tace”meya sa ka aikata haka Taheer…meyasa bakayi shawara daniba kafin kayi…Saida kasa aka sanar da kowa Taheer lokaci daya kaje kace musu ka fasa auren ‘yarsu…meyasa ka aikata haka Taheer”…tana rufe baki Taheer yace”sbd bazan iya adalci a tsakaninsu ba umma…bazan iya hada sonda nakema baby dana kowa ba…Ina gudun kar in daukan ma kaina alhakinta shiyasa umma amm…bai karasa ba umma ta rufe mai bakin da hanunta jin yanda muryanshi ke rawa…tana shafa kanshi tace”na hakura Taheer…kasan bazan dawwama Ina fushi da Kai ba…but nan gaba kar ka sake yanke irin wnn decision din ba tareda reasoning ba kanaji na koh”…da sauri yace”naji umma…in Allah ya yadda bazan karaba…thank you so much umma I love you”…umma na murmushi tace”I love you too…yanxu let me get you something to eat…nasan yanzu duk ba wani abincin kirki kake ci ba”..ya bude baki zaice ya koshi umma ta rufe mai bakin tana cewa”shshsshh..kar ma ka fara cemin you are full don nasan you are not”…Taheer murmushi kawai ya saki…Yana kallonta ta fita daga dakin…ya sauke ajiyar zuciya tareda kwanciya kan gadon..at least ya samu saukin kuncin da yake ciki.

Few minutes later umma ta shigo da plate cikeda cookies sai tea…ta karasa ta zauna gefen gadon ta Mika mai mug din hanunta tace”oya tashi kasha tea…baiyi musu ba ya mike zaune tareda amsan mug din hanun nata…ta Dora mai plate din cookies din kan laps dinshi tace”gashi nn”…a hankali Taheer ya shiga Shan tea din Yana hadawa da cookies..gskyn ummi ne rabonshi da wani abincin kirki shi kanshi ya manta…Saida ya shanye tea din gaba daya snn ya Mika Mata mug da sauran cookies din yace”thank u so much ummah”…umma na murmushi tace”you are always welcomed my son…yanxu kaje ka kwanta kayi bacci..da safe sai mu karasa mgn”…Saida ya mike snn yace”to umma Saida safe”…tana daga mishi Kai tace”Allah ya tashemu lfy”…tana binshi da kallo har ya fita daga dakin…ta sauke ajiyar zuciya…tasan baisan ummi na Shirin tura Layla porthacourt ba…bata San ya zaiyi ba idan yaji wnn mgnr.

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

This page is dedicated to#Ummu Widad…Maman Aryan…Maman Two…Hafsah Kura…Khadija Yobe.. thanks for the love nd support Allah ya bar zumunchi.. Ummu Ashraf loves u????????

23

Karfe 9 duk sun gama shiryawa don flight din 10 zasubi…su Al’ameen nata fita da kayansu cikin mota…Layla ta fito daga dakin ummi sanyeda riga da skirt na atampa..ta daura dankwalin kayan a kanta snn ta kawo mayafi ta yafashi a kafada…hanunta rikeda wayarta…fuskan nn nata fiyau..da gani ba karamin kuka taci ba.

Da sallama Taheer ya shigo parlon…ya shiga binta da kallo kawai… ganin yanda tayi kyau cikin shigan da tayi…he feel like hugging her right now..ko kadan bai kawo da ita zaa tafi ba..sai Kuma ya kalli su Nafisa duk sun gama shiryawa suma…ya karasa kusa dasu…ya gaida ummi ta amsa a takaice…snn ya gaida umma…yana Shirin barin wurin Nafisa tace”inason yin mgn dakai bro”…ya dakata nn inda yake…ta karaso kusa dashi tace”mu danje daga waje”…ba musu ya shiga gaba tabishi a baya…a balcony suka tsaya…Nafisa na kallonshi tace”nasan bakasan tareda Layla zamu tafi ba..ummi tace mu tafi da ita and kar mu kuskura mu bari ta dawo har sai tace mu dawo da ita da bakinta”…a gigice Taheer ke kallonta yace”I don’t get you…u mean tareda baby zaku tafi wai”…Nafisa ta daga Kai alaman eh…ya firzar da iska a bakinshi tareda zira hannayenshi cikin aljihun wandonshi murya a raunane yace”but how could ummi do this to me…why zaace zaku tafi da ita… u know am not used to living without seeing her around..in Ina ganinta at least zan samu sauki unlike ace bata gari gaba daya…I don’t know why ummi ke punishing Dina haka…tasan babu abinda zatamin inji ciwonshi kmr wnn…wlh Nafisa idan baby ta bar gidan nn bansan ya zanyi ba”…shiru kawai Nafisa tayi tana kallonshi cikeda tausayi…ya mance da duk wani zancen kunya at this point…iyakan gskyrshi yake fada mata…a hankali tace”wlh na sani bro…nasani ba karamin sabawa kayi da itaba..Amma ba yanda zamuyi da ummi…nasan bacin raine yake sata aikata komai…and InshaAllah da zaran ta huce everything will be back to normal again..so kar ka damu kanka plss…anytime you feel like seeing her sai kazo ka ganta…ba Wanda zai hanaka wnn..after all Matarka ce…snn zaka iya kiranta a waya duk kaso yin mgn da ita…da sauri Taheer yace”she won’t pick my calls I know…she hates me to the extent that ko ganina bata sonyi…this whole thing is killing me…ban San ya rayuwa zai cigaba without seeing baby ba…ban San ya zanyi da raina ba”…Nafisa da taji hawaye na ciko idonta tace”don Allah take it easy on your self bro…kar wani ciwon ya kamaka”…Taheer na kakalo murmushi yace”do me one favour plss…kar ki ringa bari tana fita anyhow…snn duk zata fita make sure tasa hijab da zaiyi covering dinta complete…kar ki bari ta fita ba tareda hijab ba plss”…Nafisa na daga Kai tace”InshaAllah I will bro…just take it easy…I promise zanyi iya bakin kokarina inga tayi accepting dinka as hubby…duk wnn abun da takeyi a yanxu nasan she’s shocked ne.. InshaAllah bazata dawwama a haka ba…zata soka da izinin Allah”…wani murmushi yai escaping lips dinshi…shi sai yanxu ma ya tuna da wa yake mgn…idanunshi sun rufe that ko gane me yake cewa ma baiyi ba…Nafisa data lura kmr kunyar abinda ya fada yaji…sai tayi murmushi tace”bari muzo mu wuce bro…nace mu jira ka kaimu ummi tace driver yayi dropping dinmu kawai”…ya daga Kai yace”ba matsala zan biyoku a baya”…Nafisa tace”to shknn…snn ta juya ta koma ciki…cikin ranta tana tunanin wane irin so Taheer kema Layla haka…dubi yanda ya fita hayyacinshi kawai sbd zata bar kusa dashi…tausayinshi sosae ya kamata…ta kumayi alkawarin zata taimaka wajen fahimtar da Layla faidan auren Taheer din da ita.

Shiko Taheer binta kawai yai da kallo yana shafa Kai…he wonders abunda ya hau kanshi har ya saki maganganu a gabanta haka…yanxu shknn bai kara ganin baby…ummi knows exactly how to deal with him…ko a haka ta barshi ma is enough…yana ganin it’s the worst punishment of his entire life…babu abinda zai wahalar dashi fiyeda rashin ganin nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button