Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yau tun safe Ramla tazo gidan…yarinyarta tayi girma sosae…suna zaune parlor gaba dayansu umma na duban ummi tace”Yaya mgnr tafiyata fa wnn satin ne”…da sauri ummi tace”yanzu Aisha bamu gama da mgnr nn ba dama…tun yaushe nake binki kan kiyi hakuri da Kanon nn kici gaba da zamanki nn amma kinki…idan kin koma Kanon ma me zakiyi”…umma tayi yar dariya snn tace”babu abinda zanyi Yaya..kawai gani nai tunda ba bikin ai ya kamata in koma..ko dazu da mukai mgn da Sadiq tambaya na yake ko na koma”..(note:Sadiq shine second son din umma..shi yakebin Nafisa and yana abroad shida wife dinshi da da daya)…ummi ta shiga girgiza Kai tace”don girman Allah Aisha mgnr nn a barta kawai…ke ba miji ba..ke ba ‘ya’ya ba..haka nn ki dage sai kin koma kano…dagani sai ke fa iyayenmu suka Haifa..ko don wnn bai kamata kiyi hakuri muyi zaman mu tareba..shima Kuma Sadiq din sai naci ubanshi wlh..kan meye zai wani ringa damunki ki koma kano shida baya ma qasar gaba daya”…ummi na rufe baki Ramla tace”Dan Allah umma kawai kiyi hakuri kici gaba da zamanki a nn…Ni kainda Banga abinda kikeyi idan kin koma Kanon ba”…Taheer ma da shigowanshi knn yaji suna mgnr yace”gsky suka fada umma..mudai munfiso kicigaba da zamanki a nn plss”…da sauri ummi tace”to ai yanxu sai ki hakura tunda ‘ya’yanki sun sa baki”…Ramla na dariya tace”ummi mu ba ‘ya’yanki bane knn”…ummi tadan harareta snn tace”ga dai uwarku nan a zaune…ni tawa ‘yar tana porthacourt”…dariya kawai sukayi gaba dayansu…umma tace”to shknn..Allah sa hakan shi yafi alkhairi”…Taheer ya mike ya karasa kusada umma tareda manna mata peck a right cheek dinta snn yace”you shall live long ummatah”… murmushi kawai umma tayi tana girgiza Kai…ummi ta danja tsaki tareda kauda Kai gefe…a hankali ya matsa kusa da ita…ba zato ba tsammani kawai taji ya manna Mata peck din itama a left cheek…yana gamawa ya fice daga parlon gaba daya…ummi data saki baki tana bin bayanshi da kallo sai ta girgiza Kai kawai tareda kallon umma tace”ki gaya masa duk ya kuskura ya shigo hanuna bazaiji da dadi ba wlh..aini ba abokiyar wasanshi bace..ko don yaga nayi shiru kwana biyu yana tunanin na manta da abubuwan daya aikata ne…zai dawo har gidan nn ya sameni”… murmushi kawai umma tayi bata dai ce komai ba.
Da dare bayan Ramla ta tafi..Taheer yaje ya lallabo umma wai suje ta fadama ummi ya kamata Layla ta dawo sbd sun fara registration…tana kokarin barin parlon sai gasu sun shigo…bayan sun zauna umma tace”Yaya wai yaushe Layla zata dawo ne…Ashe har sun fara registration a makaranta”…ummi ta kalleta snn ta kalli Taheer da kanshi ke sunkuye kmr Wanda ke gaban sirika tace”Dan nakine ya turoki knn”…umma tace”to tsoron fada maki yake Yaya..duk kin mai dashi kmr stranger a gidan nn”…Saida ummi ta maida idonta ga tv dake aiki snn tace”ko ma me nayi masa ai shiya siya da kudinsa..kuma muddin yarinyar nn bata amince ba ki gaya masa dole sai ya saketa wlh”…umma ta dan kalli Taheer snn tayi murmushi tace”naji yaya in Allah ya yadda zan fada mai..yanxu yaushe Laylan zata dawo”…ummi ta kalli Taheer fuskarta a daure snn tace”yaushe aka fara registration din”…batareda ya dago kan nashi ba yace”yau kwana Hudu knn”…a takaice ta sake cewa”yaushe ne closing date”…shima a takaicen yace”this month end…on 25″…ummi ta mike tareda kama hanyar dakinta snn tace”zuwa month end din sai ta dawo kafin ayi closing”…a tare umma da Taheer suka hada ido snn suka bita da kallo har ta shiga dakinta…Taheer ya wani rausaya kai yace”umma kiji me take fada don Allah…ya kamata ta dawo da wuri…bamusan time din da zaiyi taking dinta kafin ta gama komai ba”…umma ta sauke ajiyar zuciya snn tace”kar ka damu…zan sakeyin mgn da ita.. InshaAllah ko zuwa next week ne sai ta dawo”…Saida ya mike snn yace”to umma Saida safe”…ta mike itama tana fadin”Allah ya tashemu lfy”..daga haka ta shige daki ta kwanta…shima ya wuce part dinshi.
Washegari da safe ummi ta Kira Nafisa a waya..bayan sun gaisa tace”kinaji Nafee…inaso ku bincika idan zaa samu available flight Layla ta dawo cikin satin nn…Ashe har sun fara registration a makaranta”…Nafisa da ba karamin dadin mgnr ummi taji ba tace”to zaa bincika InshaAllah ummi..duk yadda akai zan Kira sai in fada miki”…ummi tace”to shknn..ki gaida yaran gaba daya”…Nafisa ta amsada”zasuji”snn sukai sallama…tana ajiye wayan ta saki wani ajiyar zuciya..Allah ya sani dama tafi son Layla ta koma can…ko ba komai idan Taheer din na ganinta zai Dan samu sauki..snn ita kanta Laylan saita fi accepting dinshi tunda suna tare…matsalarta daya shine yanda Layla bata iya komai ba daya shafi harkan gida…banda gyaran daki babu abinda zatace Layla tayishi ba tareda anyi Mata gyara ba…ko kirgi nn kusan kullum cikin nuna Mata take sbd batason a kaita gidan miji haka..amma kullum da kuka take barin kitchen din..gaba daya Taheer ya gama sangarta ta..babu abinda yake Bari a koya Mata tun tuni…ta mike zuwa dakinda Laylan take don tasan tanacan tana aikin bacci ko kallo..dole ta fito su shiga kitchen din yanxu..Kuma ko kukan jini zatai yau sai tayi musu stew a gidan nn(lallai zakuga stew kuwa????)
Daidai wnn lokacin Taheer na office…haka nan yaji yana son ganinta yanzu…ya dauka wayarshi dake kan table tareda kunna data hoping ya samu Nafisa online sai suyi video call…luckily Kuma ya sameta online din…aiko ba bata lokaci ya kirata video call…lokacin suna kitchen tareda Layla daketa faman tsalle wai kar miya ya digan mata a hannu…tana ganin shi yake kira ta dauki wayan tareda komawa parlor…Saida ta zauna snn tayi picking call din…tana mai murmushi tace”barka da safiya yallabai”…Taheer ya Dan shafa kanshi snn yace”barkda dai..ya gida ya yara”…Nafisa ta Dan wara ido tace”ya yara zakace ko Kuma ya baby”…Saida ya koma ya jingina jikin kujeran da yake Kai snn yace”nidai ya yara kikaji nace”..tace”to yara duk suna nn lfy..sun tafi school…ita Kuma babyn gata can a kitchen”…Taheer ya zare ido tareda mikewa zaune yace”kitchen Kuma..me takeyi a kitchen”… Nafisa ta danyi dariya ganin yanda ya wani zaro idanu snn tace”aiki Mana bro…zan zauna Ina kallonta ne inyita aiki ni kadai Kuma in gama in bata taci..no..it’s not possible”
Kuyi hakuri da short chapters din nn pls..am kind of busy ne these days.
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
25
Not Edited
Taheer dake kallonta da mamaki yace”meyasa Zaki wani turata kitchen sbd Allah..ba girki fa ta sabayi ba konewa kawai zatayi a banza a wofi..don Allah ki kirata ta fito kije ki karasa girkinki da kanki”…kafin Nafisa tayi mgn Layla ta kwala wani uban ihu daga kitchen din…lokaci daya Taheer ya rikice yace”you see..na fada maki ba saba yin girki tayi ba…jeki duba meya sameta”…Nafisa na murmushi ta mike zuwa kitchen din…dariya yake bata wlh…tana shiga ta iske Layla dake tsaye tana zubda hawaye…ta karasa kusada ita tana dubanta snn tace”lafiya kika cika ma mutane gida da ihu haka”…Layla dake kuka kmr Wanda akama dukan tsiya ta shiga nuna Mata finger dinta tace”kingani mai ne ya zubomin a hannu na”…Nafisa taja tsaki ta ajiye wayar kan cabinet snn ta karasa ta kashe gas dinta…tana kallon Layla fuska a tsuke tace”zanyi maganinki ne”…Layla ta sunkuyar da Kai tana hawaye… Nafisa ta karasa tareda daukan wayanta..tana kokarin fita daga kitchen din Taheer da duk yaji abunda suke fada yace”meyasa zakiyi Mata fada plss…tace maki ta kone ko hanun nata baki dubaba kina kokarin tafiya ki barta Kuma”…mamaki sosae ya sake kama Nafisa… Laylan sai kace wata karamar yarinya…kafin tayi mgn ya sake cewa”bata wayan muyi mgn”…Nafisa ta mikama Layla wayar kawai snn ta fita daga kitchen din…Layla ta janyo stool ta zauna tareda share hawayenta snn ta kalli screen din..lokaci daya Kuma tayi kasa da kanta tace”daddy Ina yini”…Taheer dake aikin kallonta ya koma ya zauna..yanajin farin ciki na lullubeshi kafin yace”muga wurin da kika kone din”…ba musu ta dago dan yatsan tana nuna mai…ya girgiza kai ya sake cewa”sorry kinji…nayi Mata mgn bazata kara cewa ki shiga kitchen kiyi Mata aiki ba”…yana rufe baki Layla tace”na kusa barin gidan ma”…ya Dan bude ido yace”Ina zakije”…”Abuja”..ta fada a hankali…Taheer ya sake bude idon nashi da kyau snn yace”u mean kin kusa dawowa gida knn”…ta daga mai kai a hankali…ya saki wani murmushi yana shafa gemu kafin yace”alright kai Mata wayan zamuyi mgn”…da sauri ta mike zata fita daga kitchen din taji a hankali yace”I can’t wait to see you”…ta sake yin kasa da kanta ba tareda cewa komai ba ta fita daga kitchen din…ta samu Nafisa a parlor ta Mika Mata wayan snn ta bar wurin…Nafisa na amsan wayan yace”da gaske baby ta kusa dawowa gida”…Nafisa na daga Kai tace”eh mana..ummi bata fada maka ba”…daga kan shima yayi yana fadin”she never told me”…tace”aikam dai da an samu available flight zata taho..zuwa gobe ko jibi”…yai murmushi yana cewa”thank God she’s leaving..bazaki barni da fargaban kina can kina turata kitchen kina sa tana konewa ba”…Saida ta girgiza kai snn tace”wai don Allah idan Layla bata koyi wnn abubuwan yanxu ba sai yaushe kke so ta koya..kafi son ayita biye Mata duk abinda takeso shi zaayi Mata knn”…tana rufe baki yace”eh nafison ayita biye matan..babu ruwanku”… murmushi kawai Nafisa ta saki tana mamakin wnn al’amari…ace mace bazaa koya Mata girki ba idan sunje gidan nasu zata ha idan shi zai hakura da aikin ya ringa yanayi musu girkin a gida..sai yanzu ma take tunanin wani irin zama zaai duk randa akace ta tare gidanshi ai abubuwanta Kara lalacewa zasuyi…wnn sangartawa har Ina.