Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Taheer na ajiye waya bayan sunyi sallama da Nafee ya shiga murmusawa shi kadai..he’s super happy baby ta kusa dawowa gida..Allah sa a samu available flight din gobe kawai ta biyo ta taho..he can’t wait to see her..he missed her like crazy.
Bayan kwana biyu…
Tun safe Taheer ya gama shiri don zuwa dauko Layla a airport…ko aiki yace bai zuwa yau..zai zauna a gida kawai yayita kallonta…duk saiya fanshe kwanakin da tayi ba tare dashi ba..
Ya mike daga dinnig bayan ya gama breakfast..ko abincin kirki baici ba sbd he’s eager yaje ya ganta…ya kalli wirst watch dake hanunshi yaga it’s 10:30…yai deciding gara yaje ya jirata a can kawai tunda by 12 flight dinsu zaiyi landing…sukaci karo da umma a parlor tana kallonshi with smile tace”wnn kwalliyan Taheer duk na Laylan ne haka”… murmushi kawai yai tareda shafa kanshi baice komai ba…Saida umma ta nemi wuri ta zauna snn tace”ba dai tun yanxu zaka tafi airport din ba”…Taheer yace”yanzu zan tafi mana umma..i can’t wait to see her you know..gra inje in jirata a can”…umma tai murmushi tana gyada kai tace”to a dawo lfy son”…Yana murmushin shima yace”Ameen Umma..na tafi”…har ya juya za fita ummi da fitowanta knn taji conversation din nasu tace”Kai tsaya”..ba musu Taheer ya dakatar da tafiyar da yakeyi tareda juyowa gareta…tana binshi da kallon from head to toe tace”where do u think you are going”…a takaice yace daita”airport”…sai ta shiga girgiza kai tana fadin”kar ka soma..yaushe kaji nace kaje ka daukota..na riga na tura driver yana can yana jiranta..sbd haka kar ka kuskura ka daukota a motarka kaji na fada maka”…da mamaki sosae Taheer ke bin ummi da kallo..wnn wane irin Abu ne for God sake matarshi ta sunna ummi ke cewa bazaije daukota ba sai kace guduwa zaiyi da ita…ba tareda yace komai ba yasa kanshi kawai ya fice daga parlon..ranshi ba karamin baci yai ba wlh..like how on earth ma ummi zata wani tura driver yai picking matarshi bayan he’s around…Kai tsaye Inda motarshi ya karasa..ya shiga tareda yi Mata key ya fita daga gidan…ya dauki hanyan airport direct..idan tasan wata ai bata San wataba..
In few minutes time ya isa airport..ya samu driver din da ummi ta tura yana jiranta a can shima…Kai tsaye ya isa inda yake..drivern ya fito daga mota da sauri yana cewa”sannu da zuwa yallabai”…Taheer yai Dan murmushi yace”yawwa sannu Manu..don Allah inaso ne ka biyoni a baya..zan dauketa in yaso da mun kusa zuwa gida sai ka karasa da ita ciki..snn kar ka sanar da hajiya cewa bakai kayi picking dinta ba”…Manu na gyada kai yace”InshaAllah yallabai”…Taheer ya zaro kudi a aljihu ya Mika mai snn ya koma inda motarshi ya bude ya shiga ciki.
Yana nan zaune jirginsu ya sauka…ya bude mota sauri ya fita yanata baza ido yaga ta inda zata bullo… passengers na fara fitowa yai tozali da ita..tana sanye cikin abaya sky blue…tayi veiling da mayafin rigan shima sky blue…side bag dinta rataye a right shoulder dinta..sai dayan hanun kuma janye da trolley…wani irin kyau na musamman yaga ta karayi masa…baisan lokacinda ya sauke nannauyan ajiyar zuciya ba..sai Kuma ya fara murmushi shi kadai kmr mara hankali…kasa hakura yai ta karaso inda yake..don gani yake kmr ba tafiya takeyi ba…ya nufi inda take da sauri idanunshi kyam a kanta…ita kuwa Layla bata lura dashi ba..tanadai ta dube duben inda zata ga motar gidansu…kmr daga sama taji anyi mata wata kyakykyawar runguma…ta bude idanunta sosae..ko baa fadaba tasan it’s him…sbd a jikinshi kadai takejin kamshin perfume din nn…ta lumshe ido tai lamo a jikinshi don ita kanta bata Isa tace batai missing dinshi ba…ta daga hanu zatai hugging dinshi back..sai Kuma tamaida hannayen ta ajiyesu kasa..kmr dai Wanda ta tuno da wani abun…Taheer kam yana jinta a jikinshi yaji duk wani damuwa da kunci daya shiga tsahon kwanaki sun yaye..gaba daya suka tsere suka barshi da tsananin shauki da kuma begenta…gaba daya ya manta da inda suke burinshi kawai taci gaba da kasancewa a jikinshi har Allah ya dauki rayuwarshi…gaba daya yayi nisan da ko tunanin zataji zafi baiyi ba..don ba karamin riko yai Mata ba…a hankali Layla ta shiga kokarin kwace jikinta a nashi don ji takeyi tamkar kasusuwan jikinta zasu karye..ba karamin force yai applying a hug din ba…daidai saitin kunnenshi tace”let go of me daddy plss..it hurts”…da sauri ya saketa yana kalle kallen wurin kmr dai Wanda baa cikin hayyacinshi yake ba ya dawo hayyacin nashi…ganin idanunta har sun dan canza ya kama hanunta a hankali yace”am sorry plss..kiyi hakuri”… murmushi kawai tayi snn ta gyda mai Kai…yasa hannu ya dauki trolley dinta dake gefe snn a hankali yace”muje”…ba musu ta bishi suka karasa inda motarshi ke ajiye..Saida ya bude back seat yasa kayan nata a ciki snn ya zagayo tareda bude Mata..ta taka a hankali ta shiga..shi Kuma ya rufe Mata kofar snn ya zaga shima ya shiga driver seat..yaima motar key suka tafi.
Saida suka kan titi snn ta Dan kalleshi ta gefen ido tace”Ina yini daddy”…ya juyo shima ya kalleta yana smiling yace”lfy Lou baby..how was the trip”…a hankali tace”it was fine”…ya jinjina kai kawai yana ci gaba da tukinshi…baya minti biyu bai kuyo ya kalleta ba..tayi mai kyau ne fiyeda tunanin mai karatu..on the other hand Kuma yanajin kishin yanda ta taho a haka tun daga porthacourt..ya sauke ajiyar zuciya..Allah kadai yasan adadin mazan da suka kalle mai ita…sai Kuma ya kauda wnn tunanin da sauri don baiso yayi spoiling mood din da yake ciki…
Saida sukazo gab da layinsu ya samu wuri yai parking motar…ta mirror ya duba yaga driver din yayi parking shima a bayansu…Layla dake mamakin dalilinda ya tsayar dasu a nn kmr zata tambayeshi sai Kuma ta fasa…Taheer ya zuba mata narkakkun idanunshi da suka koma red yasa hanu tareda kamo nata hannayen ya shiga murzasu a cikin nashi…yanata kokarin hada ido da ita amma taki bashi Daman hakan..sai ya saki dan gajeren murmushi murya can kasa kmr me yin rada yace”baby I missed you so much…nayi missing dinki kaman inyi hauka..am sorry for hugging you in public daxu..it’s just that I can’t control myself…am sorry plss…pardon my manners”…Layla da kanta ke kasa tanajin tamkar kasa ya tsage ta boye kanta ciki don kunya…ga wani irin bugu da kirjinta keyi kmr wadda tayi race…Saida ta tattaro nutsuwarta tana kakalo murmushi tace mai”it’s nothing daddy..bakayimin laifin komai ba”…idanun Taheer a kanta ya dan dage gira yace”Really”…ta daga mai ka da sauri tace”yea”… murmushi ya saki tareda ka hannayenta da har yanxu ke cikin nashi..yai manna musu peck snn ya sake Mata hanun yace”driver zai karasa dake gida..ni zan shigo daga baya..ummi batasan ni nayi picking dinki ba..so karki fada Mata plss”…tana daga Kai tace”I won’t”snn ta bude motar ta fita…fitowa yai shima ya dau kayanta ya maida waccan motar…da kanshi ya bude Mata back seat ta shiga..ya rufe motan..Saida yaga sun tafi snn ya sauke ajiyar zuciya tareda komawa tashi motar…wani irin farin ciki ya tsinci kanshi a ciki…he wish Yana zuwa gida kawai ummi tace”dauki Matarka ku tafi..ohh da baisan inda zaisa kanshi ba don dadi.
Layla suna karasawa gida ko kayanta bata tsaya dauka ba ta nufi cikin gidan da sauri…tana zuwa ta fada jikin ummi tana fadin”nayi missing dinki sosae ummi”…ummi ta janyeta a jikinta tana murmushi tace”nayi missing dinki sosae Nima”…peck Layla tayi Mata a forehead snn ta mike zuwa wurin umma tai hugging dinta itama snn tayi mata peck din tana fadin”duk nayi missing dinku wlh”…ummi na girgiza Kai tace”duk dabi’un Taheer ba wanda kika manta baki dauka ba..da ba haka kike da rungume rungume da yima mutane kiss ba wlh..duk shine ya bata ki da wnn abubuwan”… murmushi kawai Layla tayi batace komai ba…driver yai sallama parlon tareda shigo da kanta ciki…umma tace”sai a fito Mana da tsarabar mu mu gani”…Layla ta saki dariya tana cewa”Ni ba tsaraban da nayo fa umma..nida ko fita ma banayi”..ummi ta tare ido tace”kiji tsoron Allah Layla..Nafee tacemin duk weekend sai Awwal ya fita daku gaba daya..sbd tsinannen rowa shine zaki cemana wani wai ba fita kikeyi ba”…dariya kawai Layla tayi kafin ta dauki kayan nata tace”to Bari inje daki..yanxu zan fitoma kowa da nashi tsaraban”…tana gama fadan haka ta wuce dakinta da sauri..cikin ranta tunanin ya zama zai kasance take tsakaninta da Taheer…a yanda ta fahimta shifa da gaske son nata yakeyi…ita Kuma yanzu harga Allah bawai bata sonshi bane..kawai batasan yaushe Allah ya Dora Mata wani irin kunya da Kuma tsananin tsoronshi ba…har yanxu rungumar da yai Mata dazu ta kasa mancewa dashi..she don’t know why.