Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari ya kasance Monday..a ranar ne kuma Layla zata je school don fara registration dinta…ta gama shiri da wuri..tana zaune parlor itada umma Taheer din ya shigo…bayan sun gaisa da umma yace”baby I hope dai kin gama shiryawa don tafiya zamuyi yanxun nn”…Layla ta mike tsaye tana cewa”na gama tun dazu daddy..Ina kwana”…ya sakar mata smile snn yace”lfy qlou..how was ur night”…tace”Alhamdulillah”…Taheer ya dubi umma yace”ummi bata fito bane”…umma bata kaiga yin mgn ba ummin ta fito daga dakinta sanyeda hijabi..ta karaso parlon tana duban Layla tace”kin gama shiryawa ne”…Layla tace”eh na gama”…ummi ta wuce gaba tana fadin”to sai ku fito mu tafi”…Taheer ya wara idanun sosae yace”ummi unguwa Zakije ne”…ummi ta dakata da tafiyar da takeyi ta juyo tana mai wani kallo tace”ban gane unguwa zanje ba… registration zan rakata tayi Mana..ko da tunaninka zan bari ku tafi daga Kai sai ita ne”…Taheer da mamaki ya cikashi da kyar ya iya bude baki yace”ban gane me kike nufi ba ummi”…Yana rufe baki ummi tace”Ina nufin tare zamuje Taheer..haka kawai in bari ka fita da ‘yar mutane kaje ka aikata abinda bashi knn ba..yanda ka lalace din nn ai bazan iya bari ka kebe da yarinyar nn ba wlh..Kai ba abin yadda bane”…Taheer ya dafa goshi sbb takaici ko mgn ya kasayi..idan yaso karban hakkinshi ne wajen Layla wlh yasan hanyar da zaibi ya karba Kuma ba tareda duk sun ganeba..saidai bayan abun ya faru su fahimta..amma meyasa ummi kemai haka for Goodness sake…ita kanta Laylan wnn karon bataji dadin abinda ummin tayi ba..ai yace mata shi ba abinda zaiyi mata meyasa ummi zatace haka…itama umma tana zaune ta zubama sarautar Allah ido..tana duban ‘yar uwar tata tace”haba Yaya ya zakice haka… don Allah ki kyalesu suje su dawo ni nasan babu abunda zaiyi Mata wlh”…ummi ta saki wani murmushi tace”ai dama bazaki ganiba Aisha tunda bakison laifin danki”…umma ta mike tareda kamo hanun ummi suka zauna snn tace”don girman Allah Yaya kiyi hakuri ki barsu suyi tafiyarsu..ai yaji abinda kika fada Kuma nasan ko Yana da niyyan yin wani abun yanxu ya hakura..kiyi hakuri kar kice zaki bisu don Allah”…ummi tai shiru kawai kmr mai tunani…sai can Kuma tace”to ki gargadesa wlh..kar ya kuskura ya aikata abinda ba shknn ba don ranshi zaiyi mummunan baci”…da sauri umma tace”bazai ma aikata komai ba da izinin Allah”…ta dubi Taheer dake tsaye kmr gunki tace”wuce ku tafi Taheer..Allah ya bada saa”…Taheer kmr abinda yake jira knn ya fice daga parlon…itama Layla ta mike a hankali tabi bayanshi..cikin ranta ko dariya draman ummi ya bata wlh..wai ba abun yadda bane????

Suna fita bank suka fara zuwa..sunyi saa Kuma basu samu layi sosae ba..nanda nn ya biya kudin daga nn Kuma suka wuce school.

Ya taimaka Mata sosae..duk abinda bata ganeba zai Mata bayani snn inda ya kamata suje tare ya rakata inda Kuma ya kamata taje ita kadai sai ya jirata daga waje…basu suka bar cikin Base ba sai around 3…Kai tsaye ya maidata gida shi Kuma ya wuce clinic.

Around 9:30 ya dawo gida..bayan ya kammala duk abunda yakeyi..sai ya dauki chocolates daya siyo Mata tun ranan da ta dawo ya nufi part din nasu…gaba dayansu suna parlor suna kallo..ya nemi wuri ya zauna shima snn ya gaisa da iyayen…Layla dake makale kusada ummi tace”daddy sannu da dawowa”yai Mata murmushi kawai kafin yai mgn yaga an jefo takadda da biro gabanshi..ya kallesu snn ya daga Kai ya kalli daga inda suka fito..ummi ce ta wurgo mai su idanunta a kanshi tace”rubuta sakin yarinyar nn ka bani yanxu..ai dama na ce maka idan bata sonka bazaayi Mata dole ba”…Taheer ya shiga bin ummin da kallo baki bude..he’s totally speechless..kmr daga sama yaji Layla tace”ummi ni nace maki bana son zama dashi ne”…ummi ta juya tana kallon Layla tace”yo ai ba saikin fadaba ‘yar nn..alamomi sun nuna ba sonshi kike yi ba”…tana rufe baki Layla tace”nidai ba cewa nai bana sonshi ba ummi..ni ban taba ce maki bana sonshi ba”..ummi ta shiga salati tana tafa hannaye tace”Ni Zaki bama kunya Layla..Ina kokarin in kwatar maki ‘yancinki shine zaki watsamin qasa a ido”…itadai Layla bata sake cewa komai ba..ta turo baki kawai tareda dauke kanta gefe..umma dake kokarin yin dariya tace”kinga Yaya sai ki dena shiga harkansu yanxu..tunda ta nuna tanasonshi sai ki bashi matarshi suyi tafiyarsu can gidansu..muma mu huta”..ummi na girgiza kai tace”ko zan bashi yarinyar nn sai yayi Mata lefe wlh..duk wani abu da yasan anayi ma mace kafin a aureta sai yayi ya kawo..snn sai ayi biki ya dauki Matarshi su barmin gida”..Taheer daya kame kmr gunki sbd abubuwa biyu da suka sashi farin ciki da Kuma mamaki…na farko shine bai taba tunanin jin mgnr daya fito daga bakin Layla ba..knn hakan na nufin itama tana sonshi..na biyu Kuma dayaji ummk tace zata bashi matarshi..zai iya cewa rabonda yaji farin ciki irin wnn har ya manta…da sauri ya karaso inda ummin ke zaune ya zauna kusada legs dinta tareda Dora kanshi a kan laps dinta..ya lumshe ido yanajin wani extraordinary farin ciki har cikin zuciyarshi..murya can kasa yace”thank you so much ummina..Allah ya saka maki da alkhairi..ummi Allah ya faranta maki kmr yanda kika faranta min..you are the best”..ummi na shafa kanshi itama tana murmushi tace”lallai sannu majnoon”..umma ma na dubansu cikin farin ciki tace”kwarai kuwa Yaya ga Layla ga Majnoon..Allah yai muku albarka gaba dayanku”… Layla da duk kunya ya isheta ta mike zuwa dakinta..gaba daya batasan ya akai ta saki zance haka ba..sai yanzu takejin kunyar mgnr data fada..ga Kuma su umma suma suna Kara sata jin wani kunyan…Taheer ya bita da kallo bayan ta shiga dakin..ya dago kanshi daga cinyan ummi yana dubanta tace”gobe zanyi miki transfer ummi..sai ayi duk abunda ya kamata”..ummi tace to Allah ya kaimu…yace”Ameen”..snn ya mike zuwa inda ledan chocolates daya shigo dashi yake..ya dauka idonshi na kan ummi yana nuna Mata ledan yace”ummi don Allah in Kai Mata”…Ummi tabi ledan da yake nuna Mata da kallo kmr zatace aah sai Kuma tace”Kai Mata Amma karka dade”..wani dadi ya sake kama Taheer ya nufi dakin nata yana”yanzun nn zan fito ummi”…Ummin tabishi da kallo kawai tana murmushi…Saida ya shiga dakin snn ta dawo da kallonta kan umma tace”Ina sane nayi abunda nayi fa Aisha..nasan da zaunar da ita akai akace ta fada tana sonshi ko batasonshi bai zama lallai ta fada ba..yanzu da nayi haka kinga gashi ko tambayan ta baayi ba ta fada”…Umma ma na dariya tace”Kuma wlh kinyi hikima Yaya..da tambayan nata akai zataji nauyin fada..amma yanxu kiga yarinya kai tsaye ta fada abinda ke cikin ranta..Allah ya musu albarka ya basu zamn lfy”…ummi ta amsada ameen snn tace”yanxu sai mgnr biki.. don gsky bazai yiwu ace bikin Layla guda banyi taron biki ba..dagashi sai ita suka ragemin don haka ya zama dole inyi gagarumin biki kafin a bashi ita su tafi”…cikeda gamsuwa umma tace”hakan ma yayi ai Yaya..Allah ya nuna mana lokacin”..umma tace “ameen zanyi mgn da Alh Adam inyaso sai a tsayar da lokacin bikin”….a takaice dai sun dauki tsawon lokaci suna cigaba da tattauna yanda bikin zai kasance.

Layla kuwa na shiga daki ta fada kan gado tanata sakin murmushi..batasan meke sata murmushi haka ba..kawai ta tsinci kanta cikin excitement…a hankali Taheer ya turo kofar dakin ya shigo…tana ganinshi tasa hannayeta ta boye fuskanta dasu..har yanzu Kuma bata bar smiling ba…shima da murmushi a fuskarshi ya karaso inda take ya zauna..Yana kallon yanda ta boye face dinta yace”baby kunyan ya dawo knn”…ta cire hanun nata da sauri tana girgiza kai tace”no daddy ba kunya nakeji ba”…ya sake sakin wani murmushin Yana kallonta..sai ya bude hannayenshi idonshi cikin nata yace”come here baby”…ba musu Layla ta fada jikinshi tamkar dama abunda take jira knn…Taheer yasa hannunshi tareda matseta gam a jikin nashi..yanajin kanshi tamkar wanda yake cikin gajimare can sararin samaniya sbd tsabar farin cikin da yake ciki…daidai saitin kunnenta yace”thank you so much baby..you really save my heart from exploding..da ummi ta dage saina sakeki baby da ban San Ina zansa kainaba..thank you so much love..I love you sosae”…wani irin dadi Layla ta sakeji ya lullubeta..kalamanshi means alot to her..tanajin dadinsu sosae ba kadan ba…yasa hannu tareda dauko ledan dake ajiye gefenshi..yasa cikin hanunta yana cewa”this is yours..idan akwai wani abun da kikeso just name it..zan fita in nemo mikishi ko menene”…Layla ta dago daga jikinshi tareda bude ledan taga tulin chocolates ciki..ta zare ido sosai tana kallonsu..batasan lokacinda ta sake hugging dinshi tace”thank you so very much Daddy”…Taheer na shafa bayanta yace”no thanks baby..yanxu ki fadamin abunda kikeso”…ta sake dago kanta tana murmushi ta girgiza Kai tareda fadin”I want nothing daddyna..wnn din ma is enough..I really appreciate”…yasa hannu ya kamo fuskanta tareda manna mata slight kiss kan both cheeks dinta.. followed by forehead dinta…ya kwantar da ita kan gadon tareda ja Mata duvet ya lullubeta snn yace”ba cewa nai ki sasu a gaba kice Zaki cinye lokaci dayaba..da kadan kadan zakina ci coz banaso ya baki matsala idan period dinki yazo”…haka nn taji kunyar mgnr daya fada..ta lumshe idanunta kawai ba tareda tace komai ba…yana jan dogon hancinta yace”alright zanje in kwanta..sai da safe”…ta bude idon da sauri tace”baka yimin addu’a ba ai”…Taheer ya Kara sakin murmushi.. actually Yana sane dama ba mantawa yai ba..kawai yanason yaji ko zatayi mgnr ne gashi Kuma tayi…a hankali ya karanto adduan tareda shafeta dashi..ya tofa both sides snn ya mike tsaye yace Mata”good night..have a wonderful sleep”…ta daga mishi Kai tana murmushi itama..shi Kuma yasa kai ya fita daga dakin ba don yaso ba…har lokacin Kuma su ummi na parlon sunata discussing mgnr bikinsu..bai sake zama ba yai musu sallama kawai ya tafi part dinshi..he have to pray ya godema Allah da yake daidaita al’amuranshi one by one.. Alhamdulillah Ala kullu Haal.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button