Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari da safe ta gama Shirin tafiya school don tanada lecture 8…shima Taheer ya gama shiri da wuri don yanaso yayi dropping dinta a school din..yana shigowa parlon ko gaisawa baiyi dasu umma ba ummi ta hau shi da fada”yanzu Taheer sbd bakada kunya..baka San Annabi ya faku ba..shine ka kira yarinyar nn jiya bangarenka koh..wani wai ta kawo maka abinci..da uban wane ya hanaka cin abincin tun a nan..shine Saida dare ya tsala ka lallaba ka kirata wurinka sbd kawai ka samu damar kebewa da ita koh”…Taheer wani irin kunya yaji ya kamashi sbd bayan umma akwai Nafisa a parlon..Allah ya sani shidai yana jin nauyinta sosae..ko don ita ta haifi Laylan oho…Saida ya Kau da kanshi gefe snn yace”ummi abinci nace ta kawomin fa kawai..mene laifi a ciki fisabilillahi don ta kawo min abinci”…ummi tace”ai bazaka ga laifi ba dama..and this should be your last..kar ka kuskura ka sake kiranta bangarenka wlh..inba hakaba ranka sai yayi mummunan baci”…Taheer da kanshi ke qasa..cikin zuciyarshi yace”kwana nawa ne zamu bar maki gidan naki ma”..a fili Kuma yace”toh”…daidai nn Layla ta fito daga dakinta don driver na jiranta a waje..tana sanyeda hijab dinta har qasa..jakanta rataye a shoulder dinta sai handouts dinta data rungume a jikinta…ta karaso parlon..ummi na kallonta tace”wai don jaraba saura kwana uku a fara bikinki amma bazaki hakura da mkrntan nn ba..daga gobe dai ba inda zaki kara sa kafa ki fita sedai ko gidan mijinki”..itadai batace komai ba..bayan ta gaisa da kowa tai musu sallama ta fita daga parlon..Taheer ya bita da kallon mamaki don shi kadai ne bata gaisar ba a parlon..ya mike da sauri zai bita umma ta maidashi zaune da sauri..ya juyo yana kallon umman yace”umma fushi takeyi dani fa”…umma na daga kai tace”kyaleta”..ummi dai ta mike ta bar musu parlon..ya rage daga shi sai umma..sai Kuma Nafee dake gefe..Taheer na duban umma da mamki yace”in kyaleta Kuma umma..fushi tayi dani fa”…umma tadan bata rai tace”ka rabuda ita tayita fushinta Mana..ai ba Kaine kayi Mata fada ba Yaya ce..sbd taga kana damuwa shiyasa take maka wnn iskancin..da girmanka da komai ka tsaya qaramar yarinya tana caja maka Kai”…kafin yai mgn Nafee ma tace”umma gsky ta fada bro..ka rabu da ita don ubanta..duk ta gaji da fushin zata sauko..kuma bari ma ta dawo zanji ko kai din sa’an tane da zatana yi maka irin wnn iskancin”… girgiza kai Taheer yai snn a hankali yace”bazaku gane bane umma..ba wai zan bata hakuri sbd tafi karfina bane..No..zan bata hakurine sbd in samu peace of mind”..sai yai shiru tareda kama hanun umma cikin nashi..snn yacigaba”indai zata cigaba da fushi dani haka umma to wlh gaba daya ku kanku bazaku gane kaina ba..bazan iya samun nutsuwa ba in har nasan tana fushi dani haka..kuyi hakuri”..ya karasa mgnr cikeda rauni..da gani zakasan ba karamin azabtuwa yakeyi da soyayya ba…umma da tausayinshi ya kamata tace”to amma Taheer haka zaa ringa biye mata baa isa ayi mata fada ba knn..kadafa ka bari soyayyan nn da kake mata ya zama silar lalacewarta Kuma”..ya rufe bakin umma da sauri yace”in Allah ya yadda bazata lalace ba umma..idan tayi laifi ko banyi Mata fadaba ai nasan yanda nake treating dinta..Kuma batajin dadin hakan..so don Allah ki dena wnn mgnr kinji..babu abunda zai faru Bi’iznillah”…umma na gyada kai tace”shknn..amma ka ringa kokarin boye wnn son Taheer..ba koyaushe zakana nuna mata u can die for her ba”..yace”an gama umma..yanxu bari inxo in wuce office”..kafin umma tai mgn Nafisa tace”kodai ka wuce wurin Laylan taka ba.. Majnoon”.. murmushi kawai ya saki kana yace”mind u..naji kina cewa zata dawo ta sameki to babu ruwanki da ita..wnn tsakaninmu ne”..dariya kawai tayi..tana binshi da kallo har ya fita snn tana duban umma tace”na rasa wnn wane irin soyayya ne umma..kmr a irin indian films din nn wlh”…umma tace”ba yanda Allah baya ikonsa ai..shi nashi jarabawan knn”

Taheer ko daya fita bai samu motan a cikin gidan ba..hakan ya tabbatar mai da cewa sun tafi..ya shiga mota shima ya tafi..ya zama dole ya bita har makarantan ya rarrashi abarshi..idan kuwa ba hakaba yau ko patients din bazai iya dubawa ba..and 10 zai shiga theatre..so dole ya lallabota kafin time din..kar yaje ya farka matar mutane yazo ya kasa dinkewa..lol????

mintina qalilan suka kaishi school din..bayan yayi parking sai ya shiga Kiran wayanta…saida ya kusa katsewa tayi picking..a takaice yace da ita”Ina jiranki a parking lot baby”…bai jira me zata fada ba ya kashe wayan..ita Kuma ta dubi Hanna dake zaune kusada ita tace”babe bari in dan je waje pls..daddy na jirana”…Hanna ta saki wani dariya tana fadin”saikin dawo yammata..ai yanxu ke amarya ce..so dole ayi miki duk abinda kike so”..Layla na murmushi ta fita daga lecture hall din…tana isa inda motarshi ta bude ta shiga ciki…kanta a qasa tace mai”Good morning Daddy”…maimakon ya amsa sai cewa yai”fushi kikeyi dani koh baby..kiyi hakuri nasan it’s my fault..da bance ki kawomin abinci jiyaba da ummi bazata yi maki fada ba”..Layla da har ta fara hawaye tace”ba laifinka bane daddy..ka dena apologizing..kawai mgnr da ummi ta fada ne banji dadinshi ba”…Taheer ya kamo hannayenta yace”duk da haka it’s my fault..tunda kina zaman zamanki na Kira nace ki kawomin abinci..kiyi hakuri kinji..and ki dena hawayen nn”…tasa hannu tana goge tears din nata snn tace”it’s ok ya wuce”…yaja kumatunta yace”to bakiyi dariya na gani ba”…ba musu ta sakin mai murmushi..shi kuma yai pecking dinta yana fadin”ko kefa..at least yanxu ina iya aikina cikin kwanciyar hankali..yanzu ki koma class abunki.. thank you”…har yanzu bata bar murmushi ba..ta bude motan ta fita..tana mai waving har ya tafi snn ta juya itama ta koma class.

Thursday..

Yau ya kama ranan kamu..tun jiya mai lalle tazo ta dandara ma amarya lalle na gani na fada..gidansu kuwa cike yake taf da mutane..’yan uwa da abokan arziki duk sun hallara.

Karfe 4 zaa fara kamun..don haka tun around 2 make up artist da zatai ma amarya tazo gidan…a nan compound din gidan zaayi kamun…so masu decorations suma na waje suna baje basirarsu na decorations…ko Ina ka waiga mutane ne abun baa cewa komai..

4:30 sharp aka gama yima amarya make up dinta..tana sanye cikin atampa super Holland fara mai zanen manyan flowers green…anyi mata irin traditional dinkin nn riga da plane zani..sai aka daura Mata zanin a kan rigan..head din dake kanta shima green.. likewise purse da kuma takalmin dake kafanta..kunneta da wuyanta kuwa..wani danqareren sarqa ne na gold..wanda ummi da kanta ta siya mata as wedding gift..haka ma Bangles da rings da suke hannunta…kallo daya zakayima Layla ka tabbatar da cewa amarya ce ko baa fada maka ba..sbd tsabar kyan da tayi..ni kaina garin kallonta saura kadan wayana ya fadi a qasa..????

Ummi da Umma kuwa..anko sukai na atampa suma super England..dinkinsu irin dogon rigan nn A shape sai aka bajeta da stones tun daga sama har qasa..mayafan da suka yafa ma iri dayane haka komai da suka Sanya irinsu daya..sunyi kyau dasu kmr ba tsofaffi ba????????

Sai Kuma Nafisa da Ramla..suma kaya iri daya sukasa..atamparsu iri daya da nasu ummi..sai dai color daya bambamta su..dinki ma iri daya akai musu..snn mayafi and everything suma iri daya sukasa..hakika duk Wanda ya kallesu dole yaji sun burgeshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button