Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bata bata lokaci wajen shiryawa ba ta sauka downstairs kmr yanda yace…yana ganinta ya mike ya fita…itama ta bishi a baya…Saida yai locking kofar snn ya nufi inda motarshi yake…yana karasawa ya bude ya shiga itama ta shiga…snn yai Mata key…mai gadi ya bude musu gate suka fita daga gidan….ko a kan hanya Layla sai Satan kallonshi take…duk ta damu da yanayin data ganshi ciki…dama shi bai iya rashin lfy ba…ba tareda ya kalleta ba yace”mu fara zuwa kici abinci ne sai mu wuce gidan?..”ta girgiza kai da sauri tace”aa idan munje can sai muci abincin”…bai sake cewa komai ba yaci gaba da driving dinshi.
Bayan sun isa gidan yayi parking ta bude mota ta fita…shima ya fita suka shiga ciki tare…ummi na zaune a parlor..sai Nafisa da itama bata komaba tana zaune kusa da ummin…da gudu Layla ta karasa ciki ta fada kan ummi tana fadin”I missed you so much Ummita”… murmushi ummi tai kafin tace”ke dawa haka da ranan nn Layla”…kafin Layla tayi mgn sai ga Taheer din shima…Saida ya samu wuri ya zauna snn ya gaisa da ummi…yana Shirin gaida Nafisa kawai yaji tace”Ina yini”…yai murmushi yana girgiza Kai shima yace”an yini lfy”…tace”lfy Lou..ya gida”….”gida lfy Lou…su Ramadhan sun koma koh”…tace”sun koma wlh..ai sbd school..nima jibi zan wuce InshaAllah”…yace”ok..Ina umma fa”…”tana kitchen”…Yana kokarin mikewa zuwa kitchen din Layla tace”yawwa umma kiyi ki gama girkin wlh yunwa nakeji”…sai ya juya yana kallonta da sauri…ummi ma kallon nata take kafin tace”ke uban me ya hanaki cin abinci kafin ki baro gidan naki”…ba tareda ta kawo komai a rai ba tace”kinsan ba iya girki nayi ba ummi..daddy yace zai siyo kafin mu tafi nace idan munxo nan sai muci”…shiru ummi tayi tana kallon Layla rai a bace…itama Laylan sai yanxu tasan tayi subutar baki…batasan lokacinda mgnr nn ya fito daga bakinta ba wlh..shknn yau mai rabata da ummi sai Allah.
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
Somebody was saying wai amarya da ango basuci kaza ba and basuyi sallah ba a last page????well you guys should relax cox bamuzo wnn wajen ba tukun…da akwai saura…so aci gaba da karatu kawai..thanks n love you all❤️????
33
Da mamaki sosae ummi ke kallonta kafin tace”me kika ce”…Layla na stammering tace”ba..ba…ba komai ummi…am sorry plss”…wani zagi ummi ta kunduma mata tana fadin”har wani abun alfahari ne rashin iya girkin da kike fada with confidence…shima Kuma tunda ba hankali ne ya ishesa ba ya biye maki kuketa sintirin siyan abinci a waje koh”…ummi ta maido kallonta ga Taheer dake sauri ya shiga kitchen wai don kar ta juyo kanshi…kawai sai yaji tace”dawo nn kaima”…jiki a sanyaye ya dawo parlon…ummi na dubanshi da kyau tace”yanxu abunda kakeyi kana ganin daidai ne knn…duk abubuwan da muka fadama yarinyar nn kasa tayi watsi dasu..don me zaka biye mata ka ringa fita siyan abinci… idan tana gwadawa ba a haka zata saba ba”…Taheer ya rausaya Kai yace”kiyi hakuri don Allah… InshaAllah zaa kiyaye”…daidai nn umma ta shigo parlon tana fadin”ah yaushe kuka zo son”…Taheer yace yanxu mukazo umma..Ina yini”…Saida ta zauna kusa dashi snn tace”lfy Lou..ya gidan”…ya sake cewa”lfy Lou”…umma na duban ummi tace”ke da qawar taki Kuma Yaya daga zuwa har anji kanku”…tsaki ummi taja snn tace”ai abun ne abun takaici wlh Aisha…har wani cemin take wani wai ita ba yin girki take ba..shima dan naki sbd shashasha ne yake biye Mata kullum yana gararin siyo musu abinci”…umma ta maida kallonta kan Taheer kafin tace”why son..ance fa ka dinga bari tana practicing watarana sai kaga tayi abunda akeso”…a takaice yace”to umma”…Saida umman ta mike snn tace”an gama abincin…sai ku tashi muje dinning”…ummi ce ta fara mikewa tai dinning din snn Nafisa..umma ma tabi bayansu…ya rage daga shi sai Layla dake matsan kwalla a parlon…ya karaso gareta da sauri ya zauna snn yace”tashi muje kici abincin toh”…tana share hawaye tace”ni na koshi”…yai shiru Yana kallonta for some secs snn ya sake cewa”to Fadi abunda kikeso inje in siyo maki yanxu kafin time din tafiyana yayi”…maimakon ta amsa sai ta riko hanunshi tace”daddy am sorry nasa ummi tayi maka fada”…yana girgiza kai yace”it’s not your fault okay..yanxu ki fadamin me kike son ci”…tana turo baki tace”ni na fasa zama a nan daddy…kaje dani clinic din kawai”…yace”bazai yiwu in tafi dake can ba baby..kiyi hakuri ki zauna a nn..zanyi mgn da ummi bazata sake yi maki fada ba”…shiru tai kawai tana kallonshi sai wasu sabbin hawaye ke fita a idonta…Taheer ya janyota jikinshi yana cewa”come on mene abun kuka Kuma..kiyi hakuri ki dena kuka naji zan tafi dake..are you happy now?..”…sai ta shiga share hawayen tana daga mishi Kai…nan suka cigaba da zama su kadai kmr marasa gsky????
Umma ce ta fara dawowa parlon snn ummi…tana dubanshi tace”wai baza kuci abincin bane”…Taheer ya Dan saci kallon ummi snn yace”Ni dama banjin yunwa”…”ita Kuma Laylan fa”…umma ta sake fada tana kallon yanda Laylan ta wani lafe a jikinshi…Saida ya sake kallon ummi ta gefen ido kafin yace”ta koshi…dama ba yunwa takeji ba”…yana gama fadan haka ya mike Yana fadin”bari muzo mu wuce..dama clinic zamuje nace mu biyo ta nan”…umma na kallon Layla data mike tsaye itama tace”ba nan zaka barta ba?..”yace”no tare zamu tafi”…ummi ta watso musu wani kallo tana cewa”to bazaka tafi da itan ba..a nan zaka barta..sbd nayi muku fada wato ku baa isa a fada maku gsky ba knn”…da sauri Taheer yace”ummi ba haka bane..dama can banyi niyyar barinta a nn din ba”… strictly ummi tace”to ni nace ka tafi ka barta a nan..idan ka dawo sai ka biyo ka dauketa”…bai sake cewa komai ba ya juya yana kallon Layla da har ta fara hawaye…ya karasa inda take tareda kamata suka zauna…cikin lallami yace daita”kiyi hakuri ki zauna kinji.. InshaAllah bazan dade ba zan dawo”…Layla sai ta fada jikinshi tana fashewa da sabon kuka…umma da ummi kallonsu kawai suke baki bude…ummi ce ta kasa hakura Saida tace”ai saidai Allah ya kyauta Kuma..dududu satinsu daya da tarewa amma dubi yanda yarinyar nn ta sake tabarbarewa sbd Allah…zuwa nan gaba ban San me zai faru ba Kuma”…su dai basu kulata ba…Taheer ya mike rikeda Layla a jikinshi suka kama hanyar dakinta…ummi na duban umma tace”kingani koh..wato ga mahaukaciya na mgn”…umma na girgiza kai tace”ki rabu dasu kawai Yaya…ki dena ma shiga harkansu suje can su karata..in yaga dama ya maidata ciki ma tsabar soyayya”..
Taheer na shiga dakin da ita..ya zauna gefen gado itama ya zaunar da ita..hannunta cikin nashi yace”kiyi hakuri ki zauna baby..tunda ummi tace ki zauna kin San ban isa in tsallake umarnin ta ba..zanyi mgn da ita InshaAllah bazata sake yi maki fadan ba..yanxu ki fada me zakici inyi sauri in kawo maki kafin na tafi”…tana share hawayenta tace”no ba sai ka siyo komai ba..zanci a nan din”… yana dubanta yace”are you sure”…ta daga mai kai…saida yai kissing dinta a forehead snn yace”to bari inzo in wuce..take care of your self kinji”…tana murmushi ta daga kai alaman toh..snn tace”daddy kaima bakaci abincin bafa”…yace”idan na fita zan nemi abinda zanci.. promise me baza ki Kara kukaba in na tafi”..tace”I promise”…”that’s my baby..Allah ya maki albarka”..Taheer ya fada yayinda yake fita daga dakin….bai sake zamaba yai sallama dasu umma snn ya tafi.