Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yana isa clinic din bayan ya shiga office dinshi sai ya shiga Kiran wayan umma…yanaso yace Mata ta bama Layla abinci kafin ya fito amma ganin ummi a wurin sai ya fasa… ringing kmr uku umma tayi picking call din…tun kafin tai mgn yace”umma don Allah ki bama baby abinci taci kinji..wlh tun safe bata karacin komai ba”… murmushi umma ta saki kafin tace”naji..bari in kirata sai ta fito taci”…cikin jin dadi yace”yawwa umma thank you…snn umma don Allah ki kulamin da ita Amana pls..ko wani abun tayi kice ma ummi a bari in na dawo sai a fadamin..ni zanyi mata fada da kaina..kinji umma”…wnn karon dariya umma tayi sosae kafin tace”saidai ka kirata da kanka ka fada Mata”…dariyan yayi shima yace”Tabb kinaso ta zageni knn umma”…”eh ni sbd ka rainani ai shiyasa ka fadamin..hadda wani cewa a riketa Amana sai kace Wanda muke gutsuran Naman jikinta munaci”…still Yana dariya yace”wlh ba raini bane umma..kawai ke kina fahimta na ne unlike ummi da slight mistake zata fara fada”…umma tace”to naji..yanxu bari in kirata taci abincin”…yace”yawwa umma i love you”… murmushi kawai take snn ta kaste wayan…Taheer dai kan Layla baida kunya Sam..
Tana shiga dakin ta samu Layla zaune waya kare kunnenta..daga yanayin yanda take mgnr umma ta gane Taheer ne…ta girgiza Kai cikin ranta tace”oh wnn yaron baida hakuri wlh..har ya kirata”…a fili Kuma tace”to ki fito kici abinci..yanxu aka gama bani amanarki”…Layla da ta gama wayan da takeyi yanxu ta mike suka fita tareda umma…ita ta zauna parlor umma Kuma ta zubo abinci ta kawo Mata…ba laifi ta danci abincin amma ba wani sosae ba…so take kawai daddy ya dawo su tafi gida abunsu…ita bai taba yi mata fada ba tun da sukaje amma yanxu ummi daga zuwanta ko 10 mins batayi cikin gidan ba ta fara Mata fada.
9 pm daidai ya shigo gidan…duk hankalinshi na kanta ko time din tashinshi bai karasa ba ya tafi…duk suna zaune parlor sai hira suke kmr ba abinda ya faru…a boye ya sauke ajiyan heart at least dai ba wanda ya sake Mata wani abun…Yana zuwa shima abinci kawai yaci snn suka tafi bayan ummi ta sake mai gargadi sosae kan lallai ya ringa Bari tana practicing girki ko yaya ne..yace Mata zaiyi ba don zai aikata din ba..ya fada ne kawai don a zauna lfy sbd ita ummi hukuma ce sai da lallashi????
Washegari…
Karfe takwas daidai yayi dropping dinta a school don 8 zata fara lectures…yana ajiyeta ya koma gida don he’s still on evening duty.
Tun da ta shiga class yau bata samu fitowa ba..sallah kadai suka fito sukayi ko abinci basu samu daman ci ba suka sake komawa for another lecture..lectures din a jere sukayi su.
Karfe uku suna zaune cafeteria itada Hanna..ita tanacin abinci Hanna Kuma tace ita tafiya gida zatayi…Layla tai sipping drink dake hanunta tana fadin”wai saurin me kikeyi ne haka..idan kinje gidan ma me zakiyi da bazaki tsaya kici abinci ba”…Hanna tace”Habibi 4 zai tashi daga office..Kuma banaso ya dawo gida ban gama abinci..I want to go back on time so that in samu in gama girki kafin ya dawo”…Layla na daga Kai tace”ohk..you can go sai gobe”…Hanna tace”wait..ke bazaki koma kiyima daddyn naki abinci da wuri ba..ko ba da wuri yake dawowa ba”…Saida ta sake sipping drink dinta tana daga kafada tace”ni bana girki ai”…Hanna ta zaro idanu waje tace”ban fahimceki ba..don’t tell me tunda kukai aure baki taba shiga kitchen da sunan girki ba”…tana rufe baki Layla tace”come on mene kikayi haka da fuskanki toh..meye a ciki..ai ni ban iya girki ba dama”…Hanna ta saki salati tareda komawa ta zauna inda ta tashi…tana kallon Layla da mamaki tace”then me kukeci a gidan all this while”…”daddy ke fita ya siyo mana”..ta fada kanta tsaye…Hanna ta sake sakin wani salatin tace”wlh Jakada ban taba sanin you insane ba sai yau…how could you…kina zaune cikin gida allowing mijinki yana fita kullum siyan abinci a eatry..mene amfaninki…to let me tell you this..namiji da kike ganinshi bashida tabbas wlh..kina nn zaune kina tunanin he can die for you wata zatazo ta kwace maki shi a banza..duk kika kuskura ya gaji da fita siyan abinci to definitely aure zai Kara..kika bari mijinki ya karo aure sbd kina lacking wani abu kuwa kinyi asara..kinaji kina gani zaa maisheki bora a cikin gidan wlh..ko kinzo kinayi daga baya bazaki taba burgeshi ba”…tunda Hanna ta ambaci wata zata kwaceshi a hanunta taji gaba daya abincin ma ya fita a kanta…like how on Earth Hanna zata kawo Mata wnn mgnr…ya zaai tace daddy zai Dena sonta ya samu wata..no..that’s no possible..idan Kuma haka ya faru to tabbas zata iya mutuwa…Saida Hanna ta buga table din dake gabansu snn ta dawo daga tunanin data Lula…cikeda rudu tace”how could you say such a thing Hanna…kawai don ban iya girki ba sai daddy yace zai karo wata”….Hanna ta kwashe da dariya kafin tace”unbelievable..ba dai har kishi ya rufeki don kinji ance he might marry a second wife in future ba..to wallahi matukar baki tashi kin gyara rayuwar aurenki ba…I assure you ko daddy bai Kara aure ba watarana duk son da yake maki sai ya Dena..sbd bakida amfani a wurinshi…bakisan girki nada matukar muhimmanci wurin ‘ya mace ba koh..to duk macen da bata iya girki ba she’s an incomplete woman..ya zama lallai ki koyi girki nor matter what don ki gujema kanki dana sani a nn gaba”…zuwa yanxu Layla kuka takeyi wiwi…harga Allah she can’t stand seeing him with another..bazata iya sharing dinshi da kowa ba..it’s better ta koyi girkin kota yaya ne amma bataso daddy yace zai Kara aure ko ya Dena sonta…tana sheshsheka tace”I know you are right Hanna…nasan gsky kike fadamin amma ban iyaba..ya zanyi in koya don Allah”…Hanna ta matso da kujeranta kusada nata..ta riko hanunta snn tace”ba Abu bane mai wahala ai…Thank God akwai social Networkings…ba abinda bazakiyi da wayanki ba..for example idan kika shiga YouTube kikai searching zasu nuno maki different kind of girki da procedures dinsu..sai ki ringa downloading kina bin yanda sukayi kema kiyi…a hankali zakiga kin saba…snn akwai recipes da nake dasu..zanyi maki sharing ta WhatsApp sai ki duba..suma Zaki iya yinsu…and akwai online classes da akeyi shima Zaki iya joining..da akwai wata sis dina a kano take..so zata fara online classes dinta cikin week din nn..zanyi maki registration sai muyi tare..and the most important thing shine kisama ranki Zaki iya..ki cire son jiki ki ware kiyita practicing tun kina samun mistake zakiga kin kware…but kina zaune a haka kina cewa baki iyaba bazai miki amfani ba…yanxu Bari in tafi kinga sauri nake..zamu cigaba da mgn gobe..akwai wasu littafai duk na koyon girki ne zan kawo maki su gobe sai kiyita practicing..bye”…Hanna na gama mgn ta wuce ta tafi don sauri takeyi…ita Kuma Layla tabita da kallo tana share hawayen idonta… maganganun Hanna ba karamin tsoro suka bata ba wlh…ashe ummi gata takeyi Mata bata saniba..aiko zatai iya bakin kokarinta taga itama ta iya girkin nn..idan ta tuna yanda Taheer ke mugun bata kulawa sai ta sakejin wani tsoro ya shigeta..bazata iya jure yana treating wata kmr yanda yake treating dinta ba..she can’t.
Haka taci gaba da zama nan wurin tana jiranshi..time time tana share hawaye don da gske mgnr Hanna ya shigeta…bata taba tunanin haka take da kishi ba sai yanxu..a da idan taga mace na damuwa idan zaa Mata kishiya ko idan taga mijinta da wata… gani takeyi kmr basuda aikinyi…like mene zai kaita wani damuwa don kawai mutum yace zai Kara aure…bata taba sanin haka feeling din yake ba sai yanxu…yanxu ta gane dalilinda yasa wasu matan ke aikata abubuwa marasa dadi kan kishi…don inhar mutum bai iya controlling kishin shi ba…babu abunda bazai iya aikatawa ba…sbd gaba daya hankalin mutum gushewa yake..bazaka Kuma taba gane yanda yanayin kishin naka yake ba sai wani abun ya faru..
(Allah ka mana tsari da kishi mara amfani????????)