Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari daya tashi bai sameta a dakin nashi ba…har ya shiga wanka ya fito..ya gama shiryawa tsaf ba ita ba alamarta…sai ya fito don zuwa dakinta ya dubata…to his suprise bai sameta a dakin ba…ya fito daga dakin ya sauka kasa wondering Ina ta shiga at this time of the day…kawai sai ya jiyo motsi a kitchen…wani smile ya saki..ashefa ta koma chef ya manta…Kai tsaye ya nufi kitchen din shima…duk ta barbaje abubuwa a kitchen tayi kicin kicin tana girki…Taheer Saida yai da gaske snn ya danne dariyan dake son kufce mai…ya karasa ciki a hankali…sai ji tayi yayi hugging dinta ta baya…ta tsayar da abunda takeyi cak…ya sunkuyo kanshi daidai wuyanta yace”good morning sweetheart…”Layla ta wani turo baki kafin a takaice ta amsa da”good morning…”ya juyo da ita tareda hade goshinsu wuri daya..hancinshi na gogan nata..idonshi kuwa kirr kan bakin da take turowan yace”idan na kama bakin nn naki bazakiji da dadi ba baby…”da sauri ta tura lips din nata cikin bakinta…Saida ya sake yin dariya snn ya zagayo kugunta da hannayenshi yace”me kike dafa mana ne…”shiru tayi da bakinta don Allah Allah take ya saketa ya kama gabanshi…ganin kiris ya rage tasa mai kuka sai ya saketa…yaja gefe ya zauna yana binta da kallo… cikin kankanin lokaci ta gama abunda takeyi..dama ta kusa gamawa ya shigo…shi ya tayata suka gyara kitchen din snn suka jera abincin a dinning…da sauri ta haura sama tana cemai she’s coming…dauriya kawai take amma maranta ya fara Mata ciwo…tunda ta tashi yau dashi ta tashi…dama tasan date dinta ya kusa…tsoronta Allah tsoronta kar ya kwantar da ita don ko kadan batason yin fashin zuwa school…a gurguje ta gama shirinta snn ta sauka kasa…ta sameshi zaune a dinning din…tana zuwa tai serving dinshi kawai itama tayi snn suka faracin abinci…yau ma dai la ba’asa..girkin nata bazaace baiyi dadi ba don tana kokartawa sosae…
Suna gama ci Kuma suka fita…tun a hanya ya lurada ita kmr batajin dadi..bai dai ce Mata kala ba Saida suka isa makarantan..kafin ta fita a motan ya zaro drugs din daya fito mata dasu…don Yana sane period dinta na iya zuwa yau…Mika Mata drugs din yai Yana cewa”take..duk kikaji maranki ya fara ciwo sai Kisha..idan Kuma kinga bazaki iya zama ba just give me a call..sai inzo in maidaki gida…”ta sakin mai murmushi snn ta amsa drugs din…bayan ta fita daga motan tace”thank you”..shi Kuma ya daga Mata kai snn ta tafi…shima ya tada motan ya tafi..cikin ranshi ko har yanxu bai bar tunanin scene dinsu na jiyaba..kawai sai ya sake sakin smile Yana shafa gemunshi…ya tabbata ba don period dinta da yake expecting ba..da ba abunda zai hanashi angoncewa yau..but zai jira har zuwa time din da zata gama period din…he really can’t wait…

A can makarantan nasu kuwa..Layla bata bama Hanna lbrin yanda sukai da Taheer ba..itama Hanna bata tambayeta ba..don bincinke is not her thing…sukaci gaba da abubuwansu as they used to.

Bayan sun gama last lecture dinsu duk kowa ya gaji so kawai yake a tashi…sai lecturer din ya tsaidasu wai zai raba musu assignment da sukayi submitting tun last week…Layla na duban Hanna tayi kasa da murya tace”kiji mutum don Allah..kowa ba class rep yake ba assignments din ba.. meye shi zai wani tsaidamu wani wai zai raba mana assignment…”itama Hanna murya a kasa tace”ki rabu da gulmamme Mana..shegen rawan Kai ne dashi”..

Yayinda suke gulmarsu…shi Kuma lecturer din nasu mai suna AY Gambo yanata Kiran sunan mutane yana raba assignment din..kmr daga sama taji yana Kiran Maryam Taheer Jakada…Layla ta mike a hankali daga seat din da take…ta fita zuwa inda yake..dukda idanunshi na boye cikin galsses saida jikinta ya bata he’s looking at her…itadai kanta kasa harta karasa inda yake ta amsa abunta…abun mamakin Kuma..yana bata nata sai ya tattare sauran papers din yacema class rep dinsu ya karba ya karasa…da hanzari kuwa class rep din yazo ya amsa..su Kuma Layla da aka basu nasu sai suka fita daga class din.

Thank you all for the prayers..na samu sauki sosa????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

35

Suna fitowa Hanna ta wuce don already Habibinta na waje yana jiranta…Layla ta rakata suka gaisa dashi snn ta samu wuri ta zauna nn parking lot din tana jiran Taheer…zuwa yanxu maranta ciwo yakeyi sosae…bata taba tunanin she is this strong ba sai yau…bata dade zaune a wurin ba ta hangoshi yazo…ta wani kauda Kai ita a dole yayi mata ba daidai ba…tun kafin ya gama parking dama ya hangota..so yana yin parking din ya nufi inda take…Yana isa ya kama hanunta ta mike tsaye..still bata kalleshi ba…shi Kuma yai murmushi snn ya shiga janta har zuwa inda motanshi yake..ya bude tareda sata ciki snn shima ya zagaya ya shiga…bayan sun fara tafiya ya dubeta har yanxu bai dena smiling ba yace”come on talk to me mana baby..sorry for keeping you waiting”…yana rufe baki ta juyo tana kallonshi da idonta daya cika da hawaye tace”bani da lfy..tun daxu nake jiranka baka zoba”…ya kamo hanunta ya rike yace”to kiyi hakuri ki yafemin kinji…wasu mutane aka kawo emergency wlh..I can’t leave ba tareda na dubasu ba”…batace komai ba sai kifa kanta da tayi kan laps dinta tana cigaba da kuka don ciwo yake Mata sosae…Taheer na rikeda hanunta har suka karasa gida…ko parking din kirki baiyi ba ya bude motan ya fita…ya zagaya side dinda take ya dauketa cak yai cikin gidan da ita…Saida ya haura sama har dakinshi snn ya ajiyeta kan gado..ya lalabo injection da zaiyi Mata da sauri ya shiga withdrawing dinshi..yana gamawa ya karasa inda take ya dagota..yana share Mata hawaye shima kmr zaiyi kukan yace mata”baby kukan ya isa haka don Allah..bari inyi maki alluran..kinci abinci dai koh”…tana hawaye ta daga kanta alamar taci..shi Kuma Taheer ya mikar da ita tsaye snn a hankali yayi Mata alluran…Yana gamawa ta sake rushewa da kuka tana kokarin durkushewa a wurin ya kamota jikinshi da sauri…ya kwantar da ita kan gadon shima ya zauna gefe…hanunta cikin nashi yace”baby dan girman Allah kibar kukan nn haka..you have no idea of what am feeling right now..da ciwon naki zanji ko da kukan da kikeyi..or do you also want me to cry?..”ta girgiza mishi kai da sauri..ta sake rike hanunshi dake rikeda nata tace”to na dena daddy..amma fa ciwo yakemun inaji kmr zan mutu ne dad…tun kafin ta karasa ya katseta ta hanyar rufe Mata baki da hanunshi…ya janyota ya dora kan laps dinshi..yana kallonta da idanunshi da sukai jaa sosae kmr zaisa kukan shima yace”ki dena cewa zaki mutu don Allah baby..bakijin tausayina koh”…Layla ta sake lafewa a jikinshi tana sauke numfashi…shima ya gyara mata kwanciyan a jikinshi yana goge Mata hawayen yace”InshaAllah Zaki samu lfy kinji koh..bazaki mutu ki barni ba Bi’iznillah”…

Daren nn dai basu samu isashshen bacci ba…sai wurin karfe 3 ciwon ya lafa Mata shine ta samu bacci…shikam ji yayi bazai ma iya baccin ba…jiki a sanyaye ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala snn ya fito ya fara sallah.

Da safe data tashi ta samu sauki sosae…ya dauketa da kanshi zuwa toilet din dakinta…ya hada mata ruwan wanka tayi..ya taimaka mata ta shirya snn yace bari ya siyo musu breakfast ya dawo..kememe Layla ta hanashi fita wai ita lallai bazai sake zuwa eatry siyan abinci ba..gashi Kuma ita bazata iya yin girkin ba..haka nn ya hakura ya dafa musu tea da kanshi snn ya soya kwai..ya dauko bread da jam..ya hada komai kan tray snn ya dauka zuwa sama..ya ajiyesu nan dinning din dake parlon snn ya shiga dakinta ya fito da ita…sai mita takeyi wai ita zata iya zuwa school ta samu sauki amma ya hanata…yace Sam bazai yadda ta bar gida ba sai ya tabbatar da she’s alright.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button