Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan sun gama Breakfast din suka cigaba da zama nn parlon..ya kunna musu wani movie a system dinshi sunata kallo..tana lafe a jikinshi bacci ya dauketa…ya maidata zuwa dakinta ganin time din sallah yayi…yana fitowa ya daura alwala snn ya tafi masallaci…bai wani jima a masallacin ba ya dawo..don hankalinshi gaba daya yana kanta..baiso ta tashi daga baccin bai dawoba..yana haurawa sama sai yaga har yanxu bata tashi a baccin ba…ya zauna knn zai cigaba da kallon da yakeyi yaji ana danna doorbell…ya ajiye system din ya sauka kasa..yana tunanin wane bako sukayi ya isa kofan ya bude…sai ya zare idanu ganin Ummi da Umma tsaye a bakin kofan…ummi tace”ko mu koma ne naga ka wani tsatstsaremu da ido”…Taheer ya saki smile snn ya matsa daga hanyar suka shigo…yace”ummi ai banyi expecting dinku bane shiyasa..sannunku da zuwa”…bata amsa mai ba suka karaso parlon suka zauna…shima ya zauna kusada umma…bayan sun gaisa ya mike zuwa kitchen tareda dauko musu drinks da ruwa ya kawo parlon..bayan ya zauna sai ya kamo hanun umma cikin nashi yace”nayi missing dinki sosae ummata”…umma tai murmushi tareda shafa kanshi tace”and I missed you more”…ummi dake zaune gefe tana dubansu tace”Ina matar gidan takene wai..ko an tafi makarantan ne”…Taheer yace”yau bata samu zuwa makarantan bama ummi..batada lfy”…ummi ta zaro idanuwa tace”batada lfy Kuma..meya sameta ni Maryama”… maimakon ya amsa mata sai ya mike yace”muje ku ganta tana sama..bacci takeyi”…gaba dayansu suka mike tareda bin bayanshi zuwa upstairs…har dakin Layla suka shiga..tana kwance kan gado tana baccinta hankali kwance…ummi ta karasa kan gadon da sauri ta zauna..har ta Kai hanu zata tashi Laylan sai ta fasa..snn ta dawo da kallonta ga Taheer tace”kai kodai ciki garta ne..inba hakaba to wnn baccin dun na meye”…Taheer ya zare idanu yana kallon ummin kmr zaisa kuka yace”haba ummi ciki Kuma ana zaune qlou”…ummi bata sakebi ta kanshi ba ta shiga tashin Layla daga baccin…a hankali ya fara bude idanunta har ta saukesu kan ummin…sai ta mike zaune da sauri tana fadin”ummi yaushe kukazo”…maimakon ummi ta amsa mata sai tace”ke me yake damunki ne haka..ciwon me kikeyi”…a hankali Layla tace”marana ke ciwo ummi..jiya ko bacci banyiba kmr zan mutu wlh”…ummi tace”tooh ciwon mara Kuma..Kai ba ance ana dainawa idan anyi aure ba”…ta karasa mgnr idonta kan Taheer da har yanxu ke tsaye…ya dan dukar da Kai snn yace”ana denawa mana..itama zata nasan zata Dena kawai lokaci ne baiyiba”…umma dake zaune gefen gadon itama tace Mata”sannu Layla..Allah dai ya rabaki da wnn wahalan”…ummi tace”Ameen”..sai Kuma ta mike ta shiga bin dakin da kallo tace”to har yanxu dai banga datti cikin gidan naku ba…Ina sane nace Aisha kar ta sanar daku zamuzo don inaso inga wainar da kuke soyawa”…babu Wanda ya tanka ta acikinsu…suna gani ta bude bayi ta leqa snn ta sake fitowa ta fita daga dakin…umma girgiza kai tace”Hajia Yaya ikon Allah”…sai Kuma ta dawo da kallonta kan Taheer tace”zafa muyi mgn son”…Taheer na dubansta shima yace”to muje dakina umma”…bata sake mgn ba ta mike..shi Kuma ya karasa inda Layla take..yai kasa da murya yana ce Mata”koma kicigaba da baccinki baby..yanxun nn zamu dawo”…ba musu kuwa ta koma ta sake kwanciya..shi kuma hadda rufeta da duvet snn yabi bayan umma da har ta riga ta fita daga dakin…suna shiga dakinshi in a serious tone umma tace”fadamin tsakaninka da Allah.. yarinyar nn ajiyeta kawai kayi kana kallonta koh..har yanxu bakayi hankali ka dena cutar kanka ba koh”…dan murmushi ya saki yana shafa Kai..yasan dama da kyar idan umma bata ganoba…a hankali yace”umma ni tausayinta nakeji wlh..she’s too young for that..ko 18 fa bata karasa b…”tun bai karasa ba umma ta katseshi da fadin”rufemin baki da Allah..da can baka San she’s too young dinba sai yanxu..haka zaka ajiyeta kana kallo knn kai bazaka tausayama kanka ba..idan Kuma da gaske bakada lfyn sai ka fada a nema maka magani”…da sauri yace”wlh lfyna qlou umma..kawai banso tasha wahala ne”…this time muryan umma a hankali tace”ka gwammace Kai kayita Shan wahalan knn…wane irin so kakema yarinyar nn ne Taheer da baka ganin komai sai ita…ko kanka baka dubawa sai ita..wane irin abune wnn fisabilillahi sai kace shanyayye”…jiki a sanyaye ya Dora kanshi kan kafadan umma…murya can kasa yace”wlh umma ni kaina ban san irin son da nake Mata ba…inajin zuciyata kmr babu komai a ciki sai ita..duk wani abu da zai dameta yana daga mun hankali fiyeda yanda zakiyi tunani..shiyasa nake hakuri sbd bazan iya jure ganin tana Shan wahala ba umma”…ajiyar zuciya mai karfi umma ta sauke kafin a hankali tace”nidai duk da haka bai kamata ka ringa cutar da kanka ba Taheer..she is your wife afterall..ba wanda zaiyi questioning dinka kan duk abunda zai faru tsakaninku”…ya dago kanshi zaiyi mgn sai ga Layla ta shigo dakin…ya mike da sauri ya rikota yana fadin”meya fito dake baby..bakijin mgn koh”…ta lagabe kai tana cewa”naji sauki fa daddy..ummi ce take nemanku”…umma najin haka ta mike suka fita daga dakin…Taheer na rikeda hanun Layla suka sauka kasa…ummi dake zaune parlor tace”Allah ya taimakeku banga wani abun da ba daidai ba a gidan..yau da naci mutuncinku wlh”…Taheer na murmushi bayan sun zauna yace”baby fa yanxu har girki takeyi ummi”…wata harara ummi ta maka mai tace”yause ka maidani kakar ka ban saniba”…Layla ma dariya tace”Allah da gske yake ummi..ko jiya ma ni nayi girki na da kaina”..dan tabe baki ummi tayi tace”da yake girkin lokaci daya ake koyanshi ba”…Taheer yace”vidoes take downloading a YouTube tana gani ummi..Kuma sunayin online classes”…cikeda fara’a ummi ta kalli Layla tace”Dan Allah da gaske”… Layla ta daga kai itama tana murmushi…umma ma murmushin tayi kafin tace”to ko ku fa..amma ace mace ta zauna bata iya girki ba Kuma bazata koyaba ai da matsala”…tana rufe baki ummi tace”gane min hanya dai Aisha..da duk tasan da wnn din ta ringa yi mana iskanci..da kin zauna baki koya dinba kanki Zaki cuta ai..Allah na tuba mazan nn na yanxu da ba shedan su akeyi ba..kina zaune zaije ya dankaro maki kishiya tazo ta kwace maki shi”…Taheer ya rausaya kai yace”Kai ummi..yanxu hadda ni cikin Wanda bazaa sheda din ba”…”hadda Kai Mana..ko kai sunanka mace ne ba namiji ba..duk mazan yanxu halinsu daya ai..sai dai wani yafi wani amma gabaki dayanku ba tabbas garesku ba”…Layla taji gabanta ya Fadi da furucin ummi…idan bata manta ba irin mgnr da Hanna ma ta fada knn…kenan da gaske ne maza basuda tabbas din..ita kuwa idan daddy ya dena sonta ko ya Kara auren wata ai ta gama yawo..tasan har ta rasu bazata samu Wanda zaiyi Mata irin son da yake Mata ba..
A takaice dai nan su ummi suka karasa yininsu a gidan…sunsha hira sosae snn an sake yi musu nasiha na zaman aure…sai after magrib suka maidasu gida..
Saida Layla ta kwana uku snn period dinta ya dauke…sai yau ne Kuma zata koma makaranta don kiri kiri yace bazata jeba sai ta warke gaba daya…suna gama breakfast suka fita don shima da wuri yake son ya isa clinic yanada theatre karfe 10.
Yana dropping dinta ya tafi…ita Kuma ta shiga ciki…tana shiga class Hanna ta taso ta rungumeta tana fadin”babe nayi missing dinki sosae ‘yan kwanakin nn…ya jikin naki”…Saida suka karasa suka zauna snn Layla tace”jiki alhamdulillah na warke..Ina Habibi”…Hanna ta wani kashe ido tana cewa”Habibi na wurin aiki wlh..har kin tunomin dashi”…dariya Layla ta saki kafin tace”Allah ya shiryeki wlh..yanxu sai kixo ki koyamun abubuwan da akai bana nn”…da sauri Hanna tace”yawwa you remind me of something..kinsan tun ranar nn kullum sai AY Gambo ya aiko a kiraki baki nn..wai meya hadaki dashi ne”…Layla na kallonta da mamaki tace”waye AY Gambo Kuma”…tsaki Hanna taja kafin tace”AY Gambon ne baki saniba Kuma yau”…Layla ta zaro idanu don sai yanxu ta ganeshi…ta bude baki zatayi mgn sukaji Class Rep dinsu yace”Jakada kije AY Gambo na nemanki…kwanakin nn da baki zoba sai da na gaji da aiken a Kira mai ke wlh..kullum sai ya kirani a waya wai in turo mai Maryam Jakada”…lokaci daya Layla taji wani irin faduwar gaba ya risketa..to laifin me tayima AY Gambo Kuma..iyaka tunaninta bata gano laifinda tai masa ba..don haka sai ta dubi Hanna tace”babe bari inje in dawo..Allah dai yasa lfy”..Hanna tace”Ameen Ameen..be careful okay”…Kai kawai Layla ta iya daga Mata snn ta dubi Class Rep din nasu tace”Yana Ina?…”muje in nuna maki office dinshi”…cewar Class Rep din knn yayinda ya juya ya fita daga class din…a hankali Layla ke binshi a baya har sukazo office din…shi ya fara shiga snn itama tayi Bismillah ta shiga…Yana zaune bisa office chair dinshi yana dan juyawa…idanuwanshi rufe ruf kmr mai yin bacci…matashi ne Wanda akalla bazai haura 31 zuwa 32 ba a shekaru…yanada haske amma ba sosae ba..snn yanada tsayi haka Kuma bai da jiki sosae…Class Rep din ne yace”Sir gata na rakota”…ya bude idanunshi da sauri snn ya saukesu kanta…ya shiga binta da wani kallo kmr Wanda keson gano wani abu tattare da ita…ya kwashi almost 6 mins yana kallon nata kafin ya zaro kudi a aljihunshi ya mikama class rep din yace”you can go”…Class Rep na amsan kudin ya juya tareda fita daga office din…ya sake maido da idanunshi kan Layla dake tsaye kanta kasa..sai wasa takeyi da fingers dinta…a hankali taji yace”ki karaso mana ki zauna Madam..ba pepper soup din mutane nakeyi Ina cinyewa ba”…jiki a sanyaye Layla ta karasa ciki ta zauna…har yanxu idanunta na kasa tace”Good morning Sir”…shiko yai relaxing kan kujeran da yake Yana kare Mata kallo at the same time yana murmushi…Saida ta sake maimaita gaisuwan snn yace”good morning princess ya jikinki”…wani irin faduwa gabanta ya sakeyi jin sunan da ya kirata dashi..Allah dai yasa ba abunda take zargi bane…har yanxu bai bar kallon taba yace”I was very worried about you..har na fara tunanin ko gida zanzo in dubaki”…mamaki ya sake kama Layla..ya akai yasan gidansu toh..ko dai kawai ya fada ne…a hankali ta dago tareda yimai one second look kafin tace”Sir you called for me”…tana rufe baki yace”I know..inaso in fanshe kwanakin da ban kalleki bane”…wnn karon dubanshi tayi da kyau snn tace”ban gane me kake nufi ba Sir”…ya saki wani smile still Yana kallonta…Saida ya kwashi kusan 3 mins snn yace”from the very first time da nayi setting idanuna kanki na rasa sukuni…what have you done to me?..”Layla tayi tsitt tana jira ya kai inda za tace mai tanada aure and leave…”am asking you princess what have you done to me dana kasa dena tunaninki even for a second”…banza ta sakeyi dashi don she don’t have answer to his stupid talks…bai damu da shirun taba yai kasa da murya yace”well tunda bazaki fadi abunda kikai min ba let me tell you abunda ke cikin raina…I think I love you…I love you much more than you could imagine”…fuska daure Layla take dubanshi…dama inda takeso yazo knn Kuma yazo…cikeda bacin rai tace”Sir am sorry..Ni matar aure ce”…ya saki wani smile shima yace”Ma am sorry..Ni mijin aure ne”…a kufule ta sake dagowa tana dubanshi..bata San Kuma me zata fada mai ba…yana kallonta shima yace”do you think wnn mgnr da kika fada zaisa ince na dena sonki ne..to ki kalleni da kyau da gaske nake sonki bada wasa ba..nasan Mata irinku dama sunada habit din cewa sunada aure in order to get rid of wadanda ke sonsu”…zuwa yanxu tsoro ne fal cikeda zuciyar Layla..ta fuskanci da gasken fa yakeyi kmr yanda ya fada..ya zama dole ta sashi ya yadda ce wa tanada aure..idan ba hakaba kuma zatasa kanta cikin matsala…a nutse tace”wlh Allah Sir ba karya nake maka ba..inada aure”…shiru yai yana kallonta..cikin ranshi ya kasa amincewa tana da aure..gani yake kmr raina mai hankali take…ita Kuma Layla ganin yayi shiru ta mike tsaye tana cewa”Sir I have to go kar a fara lecture ban koma ba”… wrist watch din hanunshi ya duba yaga time ya wuce Kam..ya mike tareda zagayowa inda take kafin yace”to muje in rakaki”…Layla ta sake zaro idanu tana girgiza kai tace”no thanks..ba sai ka rakani ba pls”… murmushi ya Kara saki kafin ya karasa bakin kofa ya bude mata..snn yace”to zo ki tafi abinki..inaso in Kara mgn dake before you leave”…bata sake cewa komai ba ta fice daga office din…gabanta har yanxu bai dena faduwa ba..ga wani tsananin tsoro daya baibayeta..idan daddy yaji wnn mgnr Allah kadai yasan abinda zai iya aikatawa…ta tuna yanda yakeda kishi a kanta…ko kallonta namiji ya fiya yi haushi yakeji inaga Kuma yaji mgnr wani na sonta..Kuma da aurenta… innalillahi wainna ilaihi rajiun…taketa maimaitawa har ta karasa class..Allah ya taimaketa tana shiga lecturer dinsu ta shigo…tai shiru kawai idanunta kan lecturer din daketa explanation amma hankalinta kaf baya wurin..tunanin abun daya faru kawai takeyi…har wani kuka kuka taji yana son taho Mata..ya zatayi da wnn masifa daya tunkarota.