Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Fitowanta daga wanka knn tana kokarin shiryawa Taheer ya shigo dakin..yayi wanka shima yayi changing zuwa kananan kaya..idanuwanshi a kanta yace”baby bari in danje gidan Yusuf in dawo yanxu..bai da lfy ne wlh tun last week yake kwance”…tace”tohm saika dawo..kace Nima Ina dubashi”…yace”zan fada mak ISA”…yayi kmr zai fita daga dakin sai Kuma ya dawo zuwa inda take kawai ya hadata da jikinshi..Layla ta lumshe idanunta tana jin yanda yai applying force sosae a hug…yayi kissing forehead dinta yana mata murmushi snn yace”sai na dawo”…Kai kawai ta iya daga mai tareda binshi da kallo…bayan fitanshi itama ta saki murmushi cikin ranta tana fadin”daddy Majnoon”
Washegari ma throughout AY Gambo bai kirata ba..snn bai aiko yana nemanta ba..taji dadin hakan sosae tana Kuma addu’a Allah sa ya manta daita gaba daya itama ta huta..
A bangaren AY Gambo kuwa..ba don komai ya kyaleta ba sai don yaga alamar tana bukatan ya bata space…ya sama ranshi cewa bazai sake kiranta ba as tun jiyan ma bai kara dialing numberta ba..saidai ya dauki niyyan daukan next step dinshi matukar bai samu hadin kanta ba..zai Kira sister dinta dake bashi duk wani updates a kanta..har address din gidansu ya sani..ya Kuma San address din clinic din dadyn nata da ma phone number dinshi..and the next step da zaiyi taking is zaije wurin Dr.Taheer din Kai tsaye ya sanar dashi cewa yana sonta..ai yasan ba matar kowa bace so bazai taba hakura ba sai idan cewa tayi bata sonshi.
Layla har ta tabar school tana murna yau AY bai aiko kiranta ba…hankalinta har ya fara kwanciya..don a tunaninta ya riga ya hakura..ita kadai ta fito daga class dinsu kasancewan Hanna bata da lfy..so bata samu zuwa school dinba…
Suna komawa gida ta shiga dakinta don yin wanka…Taheer ya shigo dakin nata don ganin meya hanata fitowa har yanxu…bai ganta cikin dakinba amma yaji motsin ruwa a bayi..so ya gane tana wanka knn..a hankali ya zauna gefen gadonta kawai sai idanunshi suka sauka kan wayanta dake haske tun shigowanshi..alaman dai ko Kira ko Kuma text message..bai kawo komai a ranshi ba ya dauki wayan nata..kasancewan babu key sai ya bude…number ne ya gani anyi Mata massage dashi har guda uku…ba bata lokaci ya shiga massages din…na farko cewa akai… “princess I love you”
Yaji kirjinshi yayi wani irin bugu don bai taba tunanin abinda zai gani ba knn…daya duba na biyu sai yaga ance
“I missed you so much..don Allah gobe ki daure kizo in ganki”
Wnn karon Taheer wani tari yaji ya taho mai..aiko ya shiga yinshi kmr wanda ya kware da wani abun…jikinshi har ya fara kadawa kmr mazari..waye wnn..waye wnn yakema matarshi messages irin haka..does this mean Layla na kula wani saurayi a waje knn..no hakan bazai taba yiwuwa ba..to amma idan ba kulashi takeba ta Yaya zai ringa sending mata love messages irin haka…at this point sai yaji kmr kar ya karanta na karshen don bai San me zai gani ba kuma..amma zuciyarshi ta kasa hakuri..dole yanada bukatar karantawan…don haka kmr Wanda kejin tsoron wayar ya sake dagota yana kallon last message din kmr haka
“Princess kiyi min reply plss..ko in kiraki?..”
Yana gama karantawa ya saki wayar ta Fadi kasa…ya Kai hannu da sauri yana dafe saitin heart dinshi da yaji ya shiga tsalle kmr zai fito waje…lokaci daya idanuwanshi suka koma jajur…kanshi har ya fara sarawa kmr zai rabe gida biyu…ya mike da kyar zai fice daga dakin Layla ta fito daga toilet…ta kalli wayanta dake kasa..sai tayi saurin karasawa inda wayan take ta dauka praying Allah yasa ba abunda take tunani bane…shiko Taheer bai sake kallon inda take ba yasa kai ya fice daga dakin…ita Kuma tana gama karanta text din ta saki wayan itama a kasa tareda Dora hannayenta a kai tana cewa”ma shiga uku na lalace..me na janyo wa kaina ni Maryam…na shiga uku”…sai ta durkushe a wurin tana fashewa da matsanancin kuka..tasan daddy ya riga ya gani..ta Kuma San duk bayanin da zatamai da kyar zai yadda da ita..sai yanxu taga amfanin shawara da Hanna ta bata…data fada mai tun farko da duk baazo nan wurin ba… innalillahi wainna ilaihi rajiun..na shiga uku”..shi taketa ma imaitawa tana zagaya dakin…ganin hakan ba maslaha bane sai kawai ta fita zuwa dakinshi…daga ita sai dan towe a jikinta…ta sameshi zaune gefen bed dinshi…ya dafe Kai da duk hannayenshi…tana iya jiyo yanda numfashinshi ke fita da sauri da sauri…cikin hawaye ta karaso inda yake tareda durkusawa gabanshi tace”daddy Dan girman Allah ka saurareni kaji..I will explain my self”…ya dago idanunshi da sukai jaa ya azasu kanta..tunda take bata taba ganin face dinshi a hade irin na yau ba…da kyar ya iya bude bakinshi da yaji ya bushe kaff yace Mata”to hell with your explanation…tashi ki bar min daki”…ta zaro idanuwa tana kokarin kama kafanshi tace”daddy pl..”bata karasa ba ya janye kafarshi a hanunta yace”ki 6ace min da gani Layla don’t let me repeat my self”…Layla na kuka sosae tace”I won’t leave daddy..don Allah ka sau..”mgnr nata ya makale sakamakon wani kyakyakyawan mari daya wanketa dashi…ya mike tsaye yana muzurai kmr bashi ba..ya kamata ya shiga janta a kasa..sai da ya isa bakin kofa ya bude tareda turata waje da karfi snn ya maida kofan ya rufe yana durkushewa a nan wurin…
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
38
Taheer ya lumshe ido wasu hawaye masu zafi suka shiga saukowa kan fuskanshi…yanxu ya gane ma’anar mgnr data fada ranar..”Allah ya kiyaye bacin rana”..kenan wnn ranan take addu’a Allah ya kiyaye bacin ta..”baby why plss..why zaki bama wani namiji fuska har yana kiranki yana miki sending love messages a wayanki..why plss…me na rageki dashi..is it because I love you..sbd kinga ina sonki Ina gudun bacin ranki”…shi kadai yaketa surutanshi…yana jujjuya kanshi from one side to another…Allah kadai yasan what is taking place a cikin heart dinshi..he’s feeling kmr ana wura mashi wuta ne a ciki..Banda zafi ba abunda yakeji.
Ita kuwa Layla yana turata waje tai saurin kamo towel dinta dake kokarin kwancewa..ta sake daureshi a chest dinta tana cigaba da rusa kuka…cikin muryanta daya fara dishewa sbd kukan da takeyi tace”daddy listen to me plss..wlh ba abunda kake tunani bane…ban taba bashi daman cigaba da kulani ba daddy wlh ban taba sonshi ba.. believe me dan Allah…wlh it’s not my fault..I have been trying to tell you amma ina gudun bata maka rai shiyasa ban fada ba…kayi hakuri don Allah ka yafemin”…Taheer dake ciki yanajin duk abinda take fada amma baiji zai iya sauraranta ba ko kadan…like how on earth zata ba namiji dama yana kulata and all this while bata taba fada mai ba sai da yaga text message snn Kuma tazo tana wani she’ll explain.. explain what…ai ko zai saurari abunda zata fada ma not now…gaba daya ji yai kukanta na damunshi sai ya mike daga bakin kofan tareda komawa ciki ya fada kan gado…har yanxu zuciyarshi bata bar mai suya ba…da wani ne yazo ya bashi wnn lbrin yasan bazai taba yadda ba..amma da idanunshi ya gani…ta yaa take tunanin zata mai wani explanation ya saurareta…sbd taga yana lallabata ne..zatasha mamakinshi this time around..
“Daddyna am sorry..don’t be mad at me don Allah…wlh idan na maka bayani ko bincike zaka iya zuwa school dinmu kayi it’s not my fault…don Allah daddy ka saurareni plss”…ya sake jiyo voice dinta da bai fita sosae tana fada daga waje…ya runtse idanunshi gam…bai son jin maganganun nn nata Sam..snn baison jin kukanta..amma he have to be strong..ya zama dole ya nuna mata ya dena damuwa da kukanta anymore..he have to teach her a lesson..