Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari Saturday baije clinic ba..itama Layla sbd akwai dan sauran fever jikinta bataje school din ba…tun da ta tashi ko parlor bata fita ba…shi dai ya shigo Mata da tea da magani kmr jiya snn ya fice daga dakin…
Karfe 11:30 yana zaune parlon kasa yana operating laptop amma hankalinshi Sam baa wurin yake ba…yau ma ya kira number nn Kuma bai sameta ba…zuwa gobe indai bai shiga ba he thinks zuwa makarantan nasu kawai zaiyi..zai nemoshi da kanshi in yaso duk abunda zai faru ya faru…yayi nisa cikin tunani kawai yaji ana danna bell…ya ajiye system din nn gefe snn ya mike zuwa kofar…Yana budewa yaga Yusuf tsaye tareda yaranshi guda biyu…Taheer ya wara ido da mamaki yace”so kaji sauki knn.. bismillah ku shigo”…ya basu hanya suka shigo ciki…Taheer yasa hannu ya riko yaran suka zauna kusa dashi.. yana kallonsu yace”big boys how far”.. babban cikin ne yace”ina kwana uncle”…Taheer ya amsada”lfy lou son..Ina mum dinku”.. yaron yace”tayi bakuwa”… Yusuf dake kallonsu yace”wlh har mun shirya zamuzo tare fa kawai sai ga kanwar mum dinta tazo..shine nace ta zauna mu muzo kawai..ita sai tazo next time”..Taheer na daga kai yace”aikam Kun kyauta…ya jikin naka”… Yusuf yace”Alhamdulillah wlh..jiki yayi kyau”…yace”Alhamdulillah”…yana kokarin mikewa don kawo musu drinks Yusuf yace”Ina amaryar take ne”..Taheer yace”to dan sa ido tana nn..batajin dadi ne”…wani dariya Yusuf yayi kafin yace”Allahu Akhbar mutumina kace abun yazo..fada mun wata nawane dn Allah”…shima Taheer dariyar ya danyi..yana girgiza Kai yace”ka canza halinka wlh..a gaban yara kake wnn mgnr”…bai jira jin me Yusuf din zaice ba ya wuce kitchen…drinks da snacks ya debo iri iri..ya dorasu kan tray snn ya dauko cups ya nufo parlon dasu…daidai lokacin da Layla ta sauko kasan da niyyar ta sake bashi hakuri ko zai saurareta…tana gama saukowa daga stairs taga Yusuf da yaranshi zaune a parlon…wani kunya taji ya rufeta kmr ta juya ta koma..don yar riga ce ajikinta da kadan ya wuce gwuiwa…gashin nn a barbaje don rabon da a tajeshi tun kafin faruwar wnn abun…dama shi ke taje mata…Taheer daya fito daukeda tray ya ganta tsaye a wurin..bai San lokacinda ya ajiye tray din hanunshi kan dinning ba…ya karasa inda take ya damki hanunta snn ya haura sama da ita… Yusuf ya bisu da kallo yana murmushi..cikin ranshi fadi yake”Shege sarkin kishi”
Suna gama haurawa saman ya saki hanun nata Yana Mata wani kallo yace”have you lost your mind…bakida hankali zakije cikin mutane a haka”…hawaye har ya fara wanke Mata fuska tace”kayi hakuri..ban san yana nn ba..I wanted to talk to you”…Taheer ya dauke kanshi da sauri…yanajin yanda zuciyarshi ke kokarin karyewa sbd kukan da takeyi yace”kije kisa hijab sai ki sauko ku gaisa”…a hankali tace”toh”..snn ta nufi dakinta…shi Kuma ya bita da kallo a fakaice snn shima ya sauka kasan.
Hijab tasa har qasa snn ta sake sauka…ta zauna suka shiga gaisawa da Yusuf da yaran..tayi iya bakin kokarinta wurin boye damuwan dake tareda ita…tace zata Shiga kitchen tayi girki yace ta barshi tunda bata da lfy..haka nn ta hakura ba don taso ba…tareda Yusuf suka fita sukayo musu takeaway din abinci..ita Kuma aka barta da yaran..
Sai gab da magrib Yusuf suka tafi…shima Taheer daga nn ya wuce masallaci…
Bai dawo ba sai da yayi sallahn Isha…yana zaune dakinshi yayi nisa cikin tunani…gobe take cika 18 years cif…he planned so many things kafin zuwan ranar nn…he have so many suprises for her…bai taba tunanin ranar nn zatazo mai a haka ba..he can’t even wish her a happy birthday…at this point sai yaji zuciyarshi ya karye sosae…Allah ya sani shi ke fushi da ita amma it’s like shi yake punishing kanshi da kanshi…duk suka samu sabani dama sai yaji a jikinshi… har bai san lokacinda ta shigo ba…tana sanyeda kayan baccinta lemon green…riga da wando iya gwuiwanta..kan nn a barbaje kmr na karamar yarinya…a hankali ta hauro kan gadon da yake kwance kawai sai ta fada jikinshi tana sakin kuka mai karfin gaske..Taheer ya runtse idanunshi da sauri yanajin yanda yanayinshi ya sauya lokaci daya..tausayinta da Kuma sonta da yaketa kokarin boyewa suka shiga kokarin bayyana kansu…idanunshi lumshe har yanxu…yanajin yanda bugun zuciyarshi ya sauya…bashi da zabin daya wuce yasa hannu yayi hugging dinta dasu gam…har yanxu idonshi lumshe yanajin yanda guraben da sukai missing dinta a jikinshi na ciccikowa…yayi missing dinta kmr zaiyi hauka amma ya danne…sun dauki almost 10 mins rungume da juna…ita tanata rusa kuka shi kuma yanajin wasu sabbin sonta da tausayinta na ratsa kowace kafa ta jikinshi…a hankali ya saketa..tareda kwantar da ita a kan gadon…ta dago tana dubanshi tace”Daddy list..”yai saurin katseta da fadin”I don’t want hear anything”…aikam lokaci daya tayi tsitt shi kuma ya mike tareda fadawa bathroom..cikin ranshi yana ayyana this is not the right time to surrender…ya zama dole ya daure ya nuna Mata abinda tayi ba daidai bane…soyayyarta shine babban jarabawa da yake experiencing a rayuwarshi…he pray Allah sa yaci wnn jarabawan.
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
39
Layla binshi da kallo tayi tana cigaba da kuka…yanxu daddy bazai tausaya Mata ba knn..does this mean daddy ya dena sonta knn.. innalillahi wainna ilaihi rajiun…sai ta sake kwanciya tana cigaba da rusa kuka…”Allah ya isa tsakanina dakai..ka cuceni ka shiga tsakanina da mijina..ban yafeba”..abunda take fada knn yayinda take rusa kukan nata.
Taheer bai fito daga bayi ba sai daya tabbatar da tayi bacci…a hankali ya karasa tareda zama nan kusa da ita…yasa hannu ya gyara mata gashinta da barbaje a face dinta..ya duba agogon wayanshi yaga 12 daidai…ya lumshe ido tareda sunkuyowa a hankali yayi kissing forehead dinta..murya can kasa yace”Happy Birthday my baby..I love you so much”…ya jima nn zaune yana kallonta kafin ya mike tareda kwanciya a extreme end of the bed…yanata kallon yanda take baccinta..gaba daya zuciyarshi ta sake dagulewa…bai so birthday dinta yazo a haka ba…yaso yayi mata abubuwa da dama a wnn ranar..amma he can’t…”my baby 18 years old”…ya fada a hankali…lokaci daya kuma murmushi ya maye gurbin bacin ran dake kan face din nashi…shi yana 40 ita Kuma 18…this means he’s 22 years older than her..Nafisa nada 20 years knn ta haifeta..shi kuma yanada 22…”Gosh what a mess!”…ya fada yayinda ya dafa goshinshi…har yanxu in yayi tunanin ya girmi mum dinta yakan danji wani iri..like wani irin kwamalaca ne wnn..love bai yimai adalci ba gsky..ya rasa inda zai sauka sai akan baby…shi kadai yaketa zancen zuci at thesame time yana murmushi…at this point sai yaji bacin ran nashi ya dan ragu unlike before…Yana sonta fiyeda komai a duniya..Yana sonta fiyeda son da yakema kanshi…he prays Allah ya sa a gano problem din nn..yanaso ya daidaita da matarshi ya zama ango shima kmr normal couple…
Da wnn tunanin bacci yayi awon gaba dashi.
Da asuba sai daya dawo daga masjid snn ya tasheta bayan ya gama kare mata kallo…Yana ganin ta tashi ya mike zuwa inda ya shimfida dadduma..ya zauna a Kai snn ya dauki Alqur’ani daya ajiye nn wurin ya shiga karantawa a hankali…ita Kuma ta wuce bayi Kai tsaye ta dauro alwala snn ta fito… already tanada dogon riga da hijab da take sallah dasu a dakin..don haka ta zirasu a jikinta snn ta tayar da sallah..