Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan ta idar itama Alqur’anin ta dauko ta shiga karantawa.. tana so tayi mgn dashi amma zata bari su gama karatun tukun..

Karfe 7 saura wayan Taheer dake ajiye kusa dashi ya shiga vibrating…ya dauki wayan yana kallon mai Kiran…Nafeesah…bai bata lokaci ba yayi picking call din…muryan Al’ameen yaji yace”daddy good morning”…ya Dan wara ido yace”morning Al’ameen..how are you”… Al’ameen yace”daddy am fine..pls ka kunna datanka munaso muyi video call da Yaa Layla”…Taheer yace”ok..bari in kunna”…yana gama fadan haka yayi hanging call din tareda kunna data dinshi…Yana shiga WhatsApp kuwa call din ya shigo…Saida yayi picking snn Mika mata…da sauri ta amsa..tana duba screen din wayan taga yaran da suka jere suna kallon wayan suma…kafin tayi mgn suka hada baki suna fadin”Happy Birthday to you… Happy Birthday to you…Happy Birthday dear sister.. Happy Birthday to you”….Layla dake murmushi at thesame time tana hawaye tace”Wow!!…ya akai na manta it’s my birthday..you guys are really Amazing…thank you so much…I love you all”…ta karasa mgnr tana satan kallon Taheer dake kallonta shima yana murmushi…ba karamin dadi yaji da suka kirata ba..at least zataji dadi sunyi wishing dinta Happy Birthday…yana ganin ta kallo inda yake ya dauke Kai da sauri..yayi kmr ba ita yake kallo ba…ita Kuma ta sake maida kanta kan screen din tana kallonsu tace”to Ina Mami take”… Al’ameen yace”Nasan yau daddy yana nn yana planning big big suprises for you”…yana rufe baki Ramadhan yace”how I wish i can fly to Abuja so that inga big party da daddy zai shirya maki”…Layla ta share hawayen idonta..tana kokarin danne kukan dake son taho mata tace”silly boys…to ba wani big party da big suprise da ake shiryawa..am grown up now..am 18..so no more parties”…ta karasa mgnr tana kokarin dora murmushi a fuskanta…kana gani kasan yake takeyi…kafin su sake mgn Nafeesa ta karaso inda suke ta amsa wayan…tana duban su Al’ameen din tace”oya aje a fara Shirin school”…ba musu yaran suka tafi suna ce mata “ba bye”…Saida suka tafi snn Nafee ta dubi screen din with a smile on her face tace”Happy Belated Birthday to you..Allah yayima rayuwa albarka..Allah ya shiryaki yasa ki dena dabi’un yara”..Layla na murmushi snn tana hawaye tace”thank you Mami..Ina Abba”…Nafeesa tace”Abba yana Lagos tun jiya..but am sure bai manta ba maybe zai kiraki zuwa anjima”…Layla na gyada Kai tace”ohk Mami..Ina Hibba”…tace”Hibba na bacci..Ina daddyn naki yake muyi mgn”…a hankali tace”gashi”..snn ta tashi daga inda take ta Mika mai wayan…ya amsa bayan sun gaisa yace”Kun wanke kanku da kuka Kira…dama Ina nn Ina zuba ido inga wa da waye zasu manta da birthday din namu”.. Nafeesa na dariya tace”to bamu manta ba..tun jiya ma yara keta damuna wai zasu Kira nace bazasu Kira da dare ba..shine yanxu daga suje suyi Shirin school suka dauki wayan suka Kira”…Taheer na gyada Kai yace”aikam sun kyauta..”Nafee tace”yanxu dai she’s 18 so sai ka dena pampering dinta like a small baby”…har ya bude baki zaice”she is.. and will always be my little baby girl”…sai Kuma kmr Wanda ya tuna da wani abu ya fasa..ya
manta fa da sirika yake mgn…lol????

Sun dan taba hira kadan snn sukai sallama…ya ajiye wayan snn yaci gaba da karatunshi ba tareda ya kalli inda take ba..

Layla bakin ciki ya isheta..Sam ta manta yau birthday dinta sbd damuwan da take ciki…tasan daddy bazai taba mantawa ba amma shine yayi kmr bai saniba…ta share tears dinta tana tuno tsawon shekarun nn duk zatai birthday dama a kan idonshi 12 yake cika daidai..snn shi yake fara wishing dinta Happy Birthday banda uban gifts da zai siyo Mata kmr hauka…snn every year sai ya shirya Mata party amma wnn ko alama bata gani ba…wnn abu ba karamin sake daga Mata hankali yayi ba.. gani take shknn ya dena sonta Kuma…
Tana cikin tunaninta wayan Taheer ya sake daukan ruri…wnn karon ummi ce…ba bata lokaci nan ma yayi picking…bayan sun gaisa ummi tace”wai meya samu wayar Layla ne..tun jiya nake Kira a kashe..ka manta yau birthday dinta ne?..”yace”ummi ban manta ba..gata sai kuyi mgn”…yana gama fadan haka ya mikama Layla wayan…Saida ta goge hawayenta snn ta amsa..a wani marairaice tace”Ummi”…a daya bangaren ummi tace”Happy birthday takwarata..Allah ya rayaki ya miki albarka..Allah ya Baku zmn lfy da zuria dayyiba”…Layla da kuka ya fara cin karfinta tace”ummi nidai Ina missing dinku..inaso inzo gida”…tana rufe baki ummi tace”to meye abun kuka keda kika fara girma kuma..you are 18 years old fa…ki dena kuka yau it’s your day so duk abunda kikeso zaayi maki..bashi wayan muyi mgn”…ba musu ta mikama Taheer wayan..yana amsa ummi tace”kana jina Taheer”…yace”inaji ummi”…ta sake cewa”inaso ka daukota ka kawota ta yini a gida..kaga it’s her birthday bai kamata a hanata abunda take so ba”…a takaice yace”to ummi zan kawota”…ummi tace”Yawwa Allah muku albarka..sai kunzo toh”…bata jira ko zaiyi mgn ba ta kashe wayan… saida ya saci kallon inda take zaune tana rizgan kuka snn ya mike daga inda yake..ya ninke dadduman ya maidashi inda yake snn ya dauke Alqur’anin ma ya ajiyeshi inda ya dace…yana Shirin zama gefen gadon wayanshi ya sake daukan suwa…ya karasa zama snn ya dauki wyan…yasan ko baa fadaba dama umma ce…Yana picking tace”Taheer”..ya amsa mata”Naam umma..ya gida”…umma tace”lfy Lou Taheer..Ina birthday girl”…Saida ya kalli inda take snn yace”gata nn umma..bari in bata wayan”…umma bata sake mgn ba har Saida Taheer ya Mika Mata wayan…tasa hannu da kyar ta amsa snn tace”umma Ina kwana”..umma tace”lfy Layla.. i wish you a very happy birthday kinji…Allah yayi Albarka ya kawo yara na gari”…Layla na kokarin murmushi tace”Ameen Umma..anjima zamuzo gidan ai”…umma tace”to Allah ya kawoku”…daga haka ta Mika mai wayan…ya amsa suka cigaba da hiransu da umma kafin suyi sallama.

10:15 daidai ya gama shirinshi snn ya fito daga dakinshi…Kai tsaye ya wuce nata dakin don ganin ko ta gama shiryawa itama…a gaban mirror ya sameta zaune…tanata kokarin daure gashinta da ribbon amma ta kasa sbd gashin ya dan jima baa taje Shiba…ya karasa inda take fuska a tamke ya amsa comb din dake hanunta…ta dago tana dubanshi da sauri..ganin yanda ya hade rai sai ta dauke kanta..tana share hawayenta…a hankali ya shiga taje Mata gashin kmr yanda ya saba…ita Kuma sai kallonshi takeyi ta mirror fuskan nn ba sarari…har ya gama taje kan bai yadda sun hada ido da itaba…ya dau ribbon yayi mata parking dinshi kmr yanda ya saba snn ya ajiye comb din tareda juyawa ya bar wurin…Saida yaje bakin kofa snn yace Mata”kiyi sauri ki fito..I don’t have time to waste”…kallon mamaki kawai ta bishi dashi kafin ta mike tareda zira hijab dinta dake kan gado a jikinta snn ta bi bayanshi…tana sauka kasa ya fita daga parlon itama ta fita…Saida yayi locking ko Ina na gidan snn ya nufi inda motarshi…ya bude ya shiga itama ta shiga…snn yai Mata key tareda yin horn..mai gadi na bude musu gate suka fita daga gidan.

Daidai wani katoton Saloon taga yayi parkingExclusive Women Saloon..shine sunan da ta gani rubuce a wall din saloon din..da Kuma sign board dinsu…kafin ya fita daga motan yace”what’s his name”..Layla ta dan kalleshi don bata gane me yake nufi ba…”I mean Wanda ke tura maki love messages..ya sunanshi”…ya sake fada Mata yanda zata gane…murya na rawa tace”AY Gambo”…don tayi alkawarin bazata sake hiding wani abu daga gareshi ba…bai sake ce mata komai ba ya bude motan ya fita..a dole itama ta bude ta fita…kai tsaye cikin saloon din suka shiga…suna shiga receptionist tazo tana tambayansu me suke bukata…yana pointing Layla da hanunshi yace”wanke Mata Kai nake so ayi snn ayi kitso”…Layla ta daga Kai tana kallonshi a razane…kmr zatace itadai batason kitso amma tayi shiru don bataga fuska ba… receptionist din na washe baki tace”an gama oga..muna pedicure da manicure ma in Kuna bukata..snn muna yin lalle kala kala”…Saida yadan tabe baki snn yace”ayi Mata lallen amma jaa”…da sauri receptionist tace”ohk sir”…shi Kuma ATM card dinshi ya zaro daga aljihu ya mikama Layla yace”idan sun gama sai ki basu su cire kudinsu”…Saida ta goge hawayen da suka zubo Mata snn ta amsa atm din..dama already tasan pin dinshi…bayan ta amsa ya dubi receptionist yace”kmr nanda wani lokaci ya kamata in dawo..I mean idan kun gama komai da komai”…yarinyan tace”nan da 3 hours zamu gama InshaAllah”…yace Mata shknn snn ya juya ya fita..Layla ta bishi da kallo har ya fice snn receptionist din taja hanunta suka shiga ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button