Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari suna idar da sallahn asuba suka fara Shirin tafiya..Taheer ma tunda ya dawo daga masjid bai koma part dinshi ba..yanata kallonsu sunata shiryawa..saidai tunda ya zauna baiga Layla ba…su Al’ameen suka fita da kayayyakinsu suka Sanya a mota snn suka dawo..daidai lokacin Kuma ummi da Nafee suka fito cikin Shirin su..can saiga umma ma ta fito daga dakinta…yanata baza ido ya hangota ta fito daga dakinta..tana kokarin gyarama Hibba hulan dake kanta so bata kula dashi ba…Taheer yai shiru yana kallonta..tayi mai kyau sosae as always…lace ne a jikinta riga da skirt..ta yafa mayafinta golden yellow daya shiga da lace din nata…lokaci daya ya lumshe idonshi ya bude..yanajin kmr ya dauketa su gudu inda ba mai takura musu..sam bai son kowa ya kalleta a yanda tayi kyau din nn..wani kishi yaji ya tokareshi daya tuna gidan biki zataje..and Allah kadai yasan adadin mutanen da zasu kalleta…at this point sai yaji kmr ya sa kuka…a hankali ya juya ya fice daga dakin ba tareda sunyi notcing dinshi ba.

Yana nn zaune cikin motanshi ya rasa inda zaisa kanshi sbd bacin Rai suka fito…bai yi yunkurin tashi ba yaci gaba da zamanshi nn ciki…su Kuma suka karasa gaban motan da zasu tafi dashi..suka fara shiga..da yake family car ne so ta daukesu gaba daya…ummi..umma da Nafee suna baya..tsakiya Kuma Layla ce da Hibba sai Ramla da zasu tsaya gidanta su dauketa.. Al’ameen da Ramadhan kuma suna gaba…Layla sai wara idanu take tanason ganin ta inda zai bullo amma bashi ba alamarshi…gaba daya ta damu so take kawai ta sashi a idonta kafin su wuce…shiko yana cikin motanshi yana kallonsu..duk zuciyarshi a jagule yake..yaji kowa da komai ma na bashi haushi…a hankali ya fito daga motan tareda nufowa inda suke…

A cikin motan kuwa umma sai tambayanshi take amma ba Wanda ya ganshi..Saida ya karaso inda suke snn ya shiga gaida su umman fuska ba walwala.. Nafeesa taji tausayinshi ya sake kamata kwarai..wnn wane irin punishment ne ummi take mai haka…a hankali ya matsa inda Layla ke zaune itada Hibba…tunda yazo wurin take satan kallonshi tana mamakin meya bata mishi rai haka…shiko Taheer kallonta yake yanaso ya dan kakalo murmushi ko na karya ne amma kmr fuskan ne yake daurewa da kanshi..tsabar kishi duk ya rufeshi ita kanta yaji yana jin haushinta kan wnn dressing da tayi..gashi bai isa yayi mgn ba ummi ta haushi da fada…a hankali Layla tace”daddy ina kwana”…daga kanshi kawai yayi da kyar yace”lfy”..sai Kuma ya juya ga su ummi yace”Allah ya saukeku lfy”…bai jira jin me zasu fada ba ya bar wurin da sauri…Layla ta bishi da kallo tanajin yanda hawaye yake kokarin zubowa a face dinta…wnn fushin nashi definitely tasan akwai abinda ya faru..haka nn bazai dauki fushi ba tareda reason ba..to ko sbd ummi ta dage sai sunje da ita ne..Ummi ce tacema driver yaja mota su tafi…maigadi na bude musu gate suka fita daga gidan..

Haka Layla tayita sake sake har suka isa gidan Ramla suka dauketa snn suka kama hanya…har yanxu bata bar tunanin sudden change din nn nashi ba..why is he upset..duk sai taji tafiyan ma ya fita kanta gaba daya..Allah ya sani tanajin tsoro yayi sabuwar budurwa kmr yanda ya fada Mata.

Gsky Taheer nada Fans da yawa..kowa Dr kowa Dr..ko Laylan ma bata da Fans kmrshi..yace yana godia snn Yana gaida Fans dinshi na ko ina
a kasar nn????One Love❤️????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

45

Taheer na ganin tafiyansu ya tada motanshi shima snn ya bar gidan…Kai tsaye gidanshi ya koma…yayi wanka ya shirya snn ya tafi clinic…har yanxu Kuma bai denajin zuciyarshi a dagule ba..aikin kirki ma kasawa yayi a clinci din tsabar bacin ran da yake ciki.

Su Ummi kuwa tafiyan almost 6 hours ne ya kaisu Kano..umma tace ko zasu tsaya a kanon su kwana zuwa gobe Thursday su kama hanyan Dutse amma ummi tace gara su hada tafiyansu lokaci guda…haka suka dauki hanyar Dutse duk ba Wanda bai gajiba a cikinsu…sallah kadai suke tsayawa suyi..abinci kuwa dama da kayansu suka taho..duk wanda yace yanajin yunwa zaa zuba a bashi yaci…Layla Kam ko abincin ma bata iya ci sosae ba..ta damu sosae akan bacin ran data gani shimfide kan fuskan Taheer..bata San meyasa ba amma ko kadan bata so taga yayi fushi da ita…gaba daya neman sukuninta takeyi ta rasa duk yake irin wnn fushin da ita.

Sai waje karfe 4 suka shiga garin Dutse sbd yanayin hanya da bata da kyau sosae…suna isa family house din su Awwal aka tarbesu sosae..aka kaisu masaukin da aka tanadar musu su kadai…cikin lokaci kankani Kuma aka cika gabansu da kayan ci da sha iri iri..gaba dayansu a gajiye suke sbd zama wuri daya..don haka kowa saida ya dan watsa ruwa snn suka zauna cin abincin dukda ba wai suna tareda yunwa bane tunda sunci abinci a mota…Saida suka gama snn suka shiga gidan aka fara gaisawa da mutane..duk inda suka shiga sai an nuna Layla ana cewa itace marigayi Usman zai aura Kuma sai Allah baiyi ba…gaba daya Layla sai suka tuno mata da Ya Usman dinta..ta tuna yanda yake sonta sosae…dukda baza tace yakai Taheer sonta ba amma shima tanada tabbacin son da yake mata mai girma ne…lokaci daya jikinta ya Kara yin sanyi.. memories dinta da Usman din suka shiga dawo Mata..ga Kuma Taheer da taketa expecting kiranshi tun dazu amma bai kiraba…abun sai ya hadu ya Mata yawa..don haka ta samu ta sulale daga cikin mutane tareda komawa masaukinsu ta kwanta ita kadai..kawai sai ta fara hawayen da bata San takamaiman dalilinsu ba…meyasa daddy zaiyi mata haka ne..?

Abuja…

Yinin yau gaba daya Taheer yayishi ne cikin damuwa da rashin walwala…ko abincin kirki ya kasa sama cikinshi har yanxu…haka yayita zama a clinic har dare snn ya tafi gida.. Yana so ya kira yaji sun sauka lfy snn yanaso itama yaji muryanta amma he’s upset with her…don me zata dauko wnn kayan ta sa hadda su mayafi snn ta kama hanya ta tafi inda yasan dole maza zasu kalleta…
Ya gama duk Shirin da yakeyi before kwanciya snn ya hau kan gadon ya kwanta..sai ya rungumi pillow yana sakejin takaicin rabashi da matarshi da akayi kawai sbd biki…the more yana tunani the more zuciyarshi ke Kara lalacewa…a karshe dai gani yai bazai iya jurewa ba sai ya dauko wayanshi ya shiga dialing number dinta..ko su ummin bazai kiraba don suma sun bata mishi rai…

Layla dake kwance daki tun dazu taji wayanta ya fara vibrating…ta daukota da sauri don tana expecting kiran nashi…tana ganin shine me Kiran kuwa tayi picking don karma ya katse bata daga ba…Taheer da yaji tayi picking call din sai ya sake tamke fuska kmr tana gabanshi ya Kuma ki yin mgn…a hankali cikin voice dinta dake nuna alamun tasha kuka tace”daddy are you upset”…Taheer banza yayi mata don yana ganin tambayan nata akwai rainin hankali a ciki…ta sake cewa”am sorry idan nayi maka wani abun”…tun bata karasa mgnr ba yace mata”don’t sorry me okay..karki kuskura ki bani hakuri”…Layla ta dafa goshi tanajin yanda yakeso ya caja mata kai tace”daddy laifin me nayi Kuma”…a fusace yace”oh tambayana ma kike..bakisan laifinda kikai ba right..wa ya baki izinin yafa mayafi ki kama hanya kije har Dutse dashi”…shiru Layla tayi a zuciyarta tana yanxu wnn fushin duk na mayafi ne..a fili Kuma tace mai”to am sorry..bazan karaba”…Taheer yai shiru kmr bazai sake mgn ba..sai Kuma yace”Ina su ummi”…tace”suna cikin gidan”…yace”ke kina Ina”…”Ni Ina daki tun dazu..na gaji ne shine nazo na kwanta”…a takaice yace Mata”to sai da safe”.. ta amsa mai da toh snn sukai hanging call din…Layla ta ajiye wayan tana mamakin wnn fushin nashi duk don tasa mayafi ne..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button