Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A can wurin dinner kuwa su ummi duk basu lura Layla bata wurin ba..don akwai mutane sosae a wajen so ko da basu ganta ba sunyi tunanin maybe tana wurin wasu family members din suna hira or something like that…

Saida aka tashi daga dinnern mutane sun fara watsewa snn hankulansu ya dawo kanta..ummi na duban Al’ameen tace”kai tashi kuje ku nemo Layla..kuce mata wucewa zamuyi zaman me takeyi Kuma”…su Al’ameen suka mike shida Ramadhan suka tafi neman Layla…suka ringa shiga lungu da saqo suna nemanta amma basu ganta ba..har premises din wurin suka fita suka duba ko Ina Amma ba Layla babu alamarta…suka dawo suka shaida musu sun duba ko Ina Amma ba Layla…”to fah”..shine mgnrda umma ta fada yayinda take duba cikin hall din kusan duk kowa ya watse su kadaine suka rage…a hankali suka mike suma suka fita daga cikin hall din..nan ma dai ba mutane sosae a wajen don da yawa sun tafi…ummi ta dubi Ramla tace”ke wai ba tare kuke bane tun dazu..ya zaayi a nemeta a rasa all of a sudden”…Ramla tace”ummi nifa tunda ta bar wurin likin nn ban sake ganinta ba..duk a tunanina wajenku tazo shiyasa ban nemeta ba”…”innalillahi ummi ta fada har karshe ta Dora da fadin”to Ina Kuma ta shiga ni Maryama”…umma tace”gsky dai abun da mamaki..ita ba karamar yarinya ba balle ace ko wani ne yai Mata wayo ya tafi da ita”..ummi tace”shine abinda na gani Aisha..ynxu idan bamu ganta ba ya zamuyi ni Maryam”..Nafeesa ta dafa kafadan ummi tace”ummi karki damu kanki dn Allah..zaa ganta InshaAllah..Bari in sake Kiran wayan nata”…tana gama mgn ta shiga dialing number Layla da taketa Kira tun dazu ana ce mata switch off..ta sauke wayan daga kunnenta a hankali..tana dubansu tace”har yanxu wayanta a kashe yake wlh”…gaba daya hankalinsu ya sake tashi…umma ce ta zaro wayanta daga jaka tareda Kiran number Taheer amma har ya gama ringing dinshi baa dauka ba…Saida ta jera mai 3 missed calls snn ta hakura..haka nn jikinta ya bata shine yazo ya tafi da ita..dukda yace sai gobe zaizo tasan halin kayanta tsaf zai iya cewa bazai iya bari sai gobn ba ya taho yau..amma gashi tanata Kiran wayanshi baya picking…Ganin mutane kalilan ya rage a wurin..umma tace su samu su karasa gidan bikin maybe tabi motan wasu ta tafi tare dasu…hakan kuwa sukayi..duk suka shiga mota suka koma zuwa gidan.

A canma dai duk binciken duniya sunyi amma ba Wanda yaga Layla…yarinyan da Taheer yasa ta kirata dazu..da taji ana nemanta tace wani mutumi ne yace ta Kira mishi ita..Kuma ta tabbata taga lokacinda ta tafi wurin mutumin…ummi ta rushe da kuka tana”innalillahi wainna ilaihi rajiun..wane mutumi ne wnn zaizo ya dauketa ni Maryam..me yake nema a wurinmu”…umma ce tayi karfin halin tambayan ta ko ya fada Mata sunanshi…yarinyan tace bai fada Mata ba Amma taji Layla ta kirashi da daddy…cak ummi ta tsaya da matsar hawayen da takeyi tareda kewayo da idanunta kan yarinyan…tana kallonta da kyau tace”me kikace ta kirashi”…yarinyan ta sake cewa”daddy”…ummi tayi wani kwafa tana fadin”aiko sai naci ubanshi wlh..mu zai rainawa hankali yazo ya sace yarinya ana cikin biki kawai sbd ya daga mana hankali”..umma da ko kadan batayi mamakin jin shi ya dauketa ba ta danyi dariya kawai..dama tasan da kyar idan bashi din bane..gashi kuwa zarginta ya zama gsky…ko Ina Kuma ya kaita yanxu sai Allah…Nafeesa ma dariya ta danyi kasa kasa cikin ranta tana ayyano rigimar da zaa sha da ummi idan ya dawo da ita…Sam ita bataga laifinshi ba tunda dama tun asali ya nuna baiso a taho mai da ita amma ummi ta dage..yanxu kuwa ko Abuja ya maida ita bazata taba ganin laifinshi ba…

A haka suka koma part din da aka saukesu..hankalinsu dai yanxu ya kwance tunda sun san tana wurinshi…ummi ce kawai taketa faman mita tun dazu..wai yaki dawo da ita ko gidan ubanwa ya kaita oho..Ramla na dariya tace”to ummi koma Ina ya kaita ba matarsa bace..ya gaji da abinda kike mai ne shiyasa kawai ya silalo yazo ya dauke kayarshi suka tafi..maybe ma zuwa yanxu sun sauka Abuja”…ummi ta maka Mata wani harara tana cewa”aiko da ya jama kanshi wlh..don sai tayi wata hudu a gida bata koma gidan nashi ba..sai inga karewan iskanci”…Ramla ta sake cewa”ummi baa shiga tsakanin ma’aurata fa..kilan yanada bukatar matarsh..”bata karasa abinda zata fada ba ummi ta buge mata bakin tana ce Mata”rufema mutane baki da Allah..kema da yake ba kunyan ne ya isheki ba zakizo ki cikani zancen banza”..gum Ramla tayi tana shafa bakinda ummi ta kaima duka…Nafeesa na zaune gefensu duk tana sauraron abinda suke fada tanata kokarin boye dariyarta amma sai daya fito…ummi ta dubeta baki bude tace”kici gaba da dariya kema..zakisha mamakina wlh..bazaku maidani tsohuwar banza ba”…

A can hotel din kuwa tana kwance a jikinshi tayi luf da idonta kmr tana bacci…a hankali ya yaye blanket da suka lullube dashi snn ya dauketa suka shiga bayi…ba tareda ta bude idanun nata ba tace”daddy ka tafi dn Allah..ni zanyi wakana da kaina”…Saida ya manna Mata kiss a Kumatu snn yace”no baby tare nakeso muyi wankan yau”…ta bude idanun nata da sauri sai Kuma ta sake maidasu still da sauri don batasan ba Kaya a jikinshi ba…ta kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”nidai dn Allah daddy kaje ka kyaleni zanyi ni kadai”…Taheer yasa hannu tareda kamo kumatunta yadan ja snn yace mata”to mu sake komawa kan gadon idan muka Kara another round sai in bari kiyi wankanki ke kadai”…fuskan ta sake kwabewa tana makale kafada tace mishi”ah ah”…ya janyota kusa dashi tareda hade bare skin dinshi da nata..ya sunkuya saitin kunnenta yace”to ya zamuyi knn..kindai san bazanyi maki alfarman abubuwa har guda biyu ba koh”…tana hawaye Kuma still idanun a kulle tace”to ka sa kayanka”… murmushi mai sauti ya saki before saying”kin taba ganin inda mutum yayi wanka da Kaya a jikinshi”…tana turo baki tace”to nidai bazan bude idona ba”…ya juyo da ita saitinshi yace”come on baby open your eyes dn Allah..am all yours so ba wani abu bane idan kin kalleni”…ta sake makale kafada tace mai”No”… shi Kuma bai sake mgn ba ya dagata sama kawai sai jinsu tayi cikin bathtub…ya cikashi taf da ruwa…a haka ya farayi Mata wankan tun tana rufe idon har Saida ta hakura ta bude..saidai taki kallon side din da yake..ita a dole bazata kalleshi ba kayaba…shi Kuma Saida ya tabbatar da ta kalla din snn ya saurara Mata…

Saida suka gama lalacewarsu a toilet din kafin suyi wankan su fito…Yana daukeda ita a hanunshi kmr jaririya…ya ajiyeta kan gadon snn shima ya zauna..tana tsuke bakinta tace”daddy dn Allah ka maidani gida…su ummi fa basu san na taho ba”…ya dauki wayanshi yana dubawa yace”ai ke da ganin su ummi sai gobe Kuma”…Layla ta wara idanu tace”hope bada gaske kake ba”.. ya dago kanshi daga kallon wayan da yakeyi yace”da gaske nake wlh..sai gobe da safe zamu koma”.. yana rufe baki tace”dn Allah daddy kar kayi haka..zasu shiga damuwa wlh dn Allah mu koma can kaji”…Taheer baiyi Mata mgn ba sai wayarshi da taga ya Kara a kunne alaman Kira zaiyi… ringing biyu umma ta daga tana fadin”sannu shugaban marasa kunya”…ya shiga shafa kanshi Yana murmushi yace”umma kinsan dai ba laifina bane koh”…tace”ba laifinka bane ai laifina ne”…yace”no umma ba haka nake nufi ba..sai da na fada maku kar ku tafimin da matata amma kuka dage Saida kuka zo..shine nima nazo kawai na dauke abata yanxu haka mun koma Abuja ma”…umma tace”ai shknn Kai da Yaya ai..zakayi Mata bayani”…Yana dariya yace”umma wasa nake wlh..Muna nn cikin Dutse bamu tafi ba”….”cikin Dutse a Ina Taheer..dama kasan wani wurin ne”… yace”aah umma..Muna hotel..amma umma dn Allah kuyi hakuri Nima ba laifina bane wlh..kawai zuwa nayi na ganta taci uban kwalliya tanata rawa shine ni Kuma na dauketa daga wurin gaba daya..am sorry kinji ummata”….umma tace”Ai shknn Taheer..yanxu sai ka dakkota ka dawo da ita tunda ka gama abinda kakeso”…Taheer ya zare idanu sosae jin abinda umma ta fada…sai kuma yai kasa da murya yace”umma ai..sai..gobe..zamu dawo”…ya fada words din a rarrabe…umma bata sake yunkurin mgn ba kawai tayi hanging call din…Layla ta matso jikinshi da sauri tana cewa”daddy dn Allah muje gida..kaga umma ma bata yadda ba..dn Allah mu koma gida kaji”…Saida ya ajiye wayanshi yace Mata”babu inda zamuje sai gobe…yanxu bari in fita samo maki abunda Zaki sa”…banza tayi dashi tana binshi da harara..ya fara shiryawa a gurguje snn yasa kayanshi…ya dau key din dakin tareda wallet dinshi snn ya fita daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button