Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Tun tana jiran su ummi su dawo har batasan time din da bacci ya dauketa ba…lokacin da suka dawo Kuma ba Wanda ya tasheta..sukayi Shirin baccinsu suma suka kwanta.
Shiko Taheer dama tun yamma ya koma hotel din da yayi lodging jiya..zai sake kwana a can amma gobe Sunday dai yake son komawa Abuja…Allah yasa suma su ummin gobe zasu tafi don baiso baby tayi missing school da yawa.
Washegari suka fara shirin tafiya kano..don daga can zasu tafi…
Basu bar cikin Dutse ba sai around 2..bayan sunyi sallama da kowa snn an cikasu da kayan biki kala kala..driver dinsu na nn dama..don haka tare dashi suka tafi…
Tun safe Layla ke zuba idon ganin Taheer amma ko mai kama dashi bata ganiba…tayita Kiran wayanshi Kuma no answer…haka har suka tafi kano bata ganshi ba..umma ma tayita Kiran wayan nashi don ta fada mishi sun wuce kano amma still no answer.
Shiko Taheer bacci ne ya daukeshi mai nauyi sosae..har bai san time ya kure haka ba…lokacinda ya tashi yayi mamaki sosae da yaga har 3 ya kusa…ya fada bathroom da sauki yayo alwala ya fito..a nn cikin dakin yai sallahn zuhr snn ya shiga bathroom din yayi wanka ya sake fitowa..a gurguje yaketa shiri don bai San ko su ummi yau zasu tafi ba…Yana daukan wayanshi ya taradda 10 missed calls from Layla..sai 4 missed calls na umma…a gaggauce ya gama shiryawa snn ya dauki kayanshi ya tafi..Saida yai clearing bill dinshi na hotel din snn ya maida musu key dinsu ya tafi…Yana zuwa can gidan aka ce mai ai sun tafi kano…wani haushi ya kamashi sosae…har zasu tafi amma ba Wanda ya nemeshi..ko da yake sun nemeshi wayan nashi ne a silent shi Kuma yanacan yana bacci..
Shatan mota ya dauka shima direct suka nufi Birnin Dabo..
Karfe 4 saura su ummi suka shiga Kano..Kai tsaye Janbulo suka wuce inda gidan umma yake…bayan sun huta sun watsa ruwa…sai suka zauna parlor suna Dan taba hira…da a yau sukaso wucewa Abuja amma ganin yamma ya riga yayi sai suka fasa sai gobe su sakeyin sammako su tafi…
Har yanxu umma bata dena Kiran wayan Taheer ba amma still baya answering…sai Kuma ta shiga tunanin ko dai ba lfy yake ba..inba hakaba ya zaayita Kiran waya Yana gani yaki dagawa.
Itama Layla a nata bangaren bata dena Kiran wayan nashi ba…duk hankalinta yaki kwanciya gani take kmr wani abu ne ya sameshi..gashi Kuma tanaso suyi mgnr AY Gambo da akace yayi test dashi..don tana tsoron taje tayi mgn dashi Kai tsaye idan Taheer din ya samu lbri tasan he’s going to be mad..ko su ummi har yanxu bata fada musu cewa anyi test a school bata nn ba.
Taheer bai sauka garin Kano ba sai after 5…direct shima ya dauki drop din napep ya kaishi gidan umma don yasan for sure zai samesu a can tunda yamma yayi so baya tunanin zasu kama hanyan Abuja..yasan ummi bata son tafiyan dare Sam.
Yana shiga duk suka bishi da kallon mamaki..don ita ummi duk a tunaninta ya riga ya koma Abuja..umma ce tace dashi”Kai meya samu wayanka ne tun safe naketa kiranka amma baka dauka”…Taheer ya karasa cikin dakin ya zauna snn yace mata”wlh umma bacci ne ya daukeni..Kuma wayan a silent yake shiyasa ban ji Kiran naki ba”…umma tace”to da kaga missed call kuma meya hanaka Kira”…Kai ya langabe snn yace”umma sauri nakeyi in taho shiyasa..am sorry”…ummi tace”Kai daya kamata ka wuce direct Abuja meya kawoka Kano Kuma”…yace”zan tafi ummi..8 jirginmu zai tashi”…daga hak ummi bata sake mgn ba…
Layla dake daki kwance taji kmr muryanshi a parlor..don haka sai ta fito parlon don ta ga ko shidin ne…aiko tana ganin shine ta karasa inda yake tana washe baki tace”daddy sannu da zuwa..yaushe kazo..daddy tun dazu nake Kiran wayanka baka dauka..what happened”…Taheer ya kama hanunta yana murmushi shima yace Mata”duk wnn tambayoyin haka baby..wayan nawa ne a silent ni kuma ina can Ina bacci”…tace”dama ancemin anyi test ne a school jiya”…Taheer na dubanta da kyau yace”test Kuma”…tana daga kai da sauri tace”eh daddy..AY Gambo..Kuma yace wai bazaima kowa mk up ba”…shiru Taheer tayi for some seconds sai kuma yace”you see..yanxu kinga dalilinda yasa na dage kan bazakiyi missing school ba..amma kika dage ke sai kinzo..yanxu ya kikeso ayi”…yana rufe baki tace”daddy Hanna tace wai idan nayi mishi mgn da kaina zai yadda..kilan ta dalilina kaga suma Wanda sukayi missing test din yayi Mana make up din tare”…Taheer ya kalleta da wani expression kan fuskanshi snn yace”ummhum Ina jinki”…a hankali tace”daddy dn Allah inyi mgn dashi?..”tana rufe baki yace mata”No…idan kika kuskura kikai mgn dashi Kuma you will see the other side of me”…Layla har ta fara hawaye..tana kokarin yin mgn ummi tace”ban gane kar tayi mgn dashi ba Taheer..ba malaminsu bane”…ranshi a bace yace”ummi malaminsu ne..amma nidai ban yadda taje tayi mgn dashi ba..ba da yawuna ba”…da mamki sosae duk suke kallonshi…banda umma da tasan dalilin da yace haka…Layla ta sake matsawa jikinshi murya a raunane tace”daddy dn Allah kayi hakuri ka barni inyi mgn dashi”…a takaice ya sake ce Mata”I said no”…tace”but daddy why”…kmr jira yake tana rufe bakinta yace”because he loves you”…tana girgiza kai tace”daddy ba mun gama da wnn mgnr ba Kuma..ya riga ya zama past tense”…”idan ke ya zama past tense a wurinki to ni a wurina bai zamaba…idan Kuma kina tunanin ya dena sonki ne you are mistaken…he loves you so much..I saw it in his eyes sbd haka ban amince kiyi mgn dashi ba…Ni zanyi mai mgn dakaina..zan rokeshi yayi maki test dinda kikai missing amma baby ko a bayan idona ban yadda kiyi mgn dashi ba..I mean it”…Taheer na gama mgn sai ta fada jikinshi tana goge hawayenta tace”na gode sosae daddy..thank you”…a hankali yasa hannunshi ya janyeta daga jikin nashi don ganin duk hankalinsu su ummi na kansu…Nafeesa da Ramla kuwa mikewa sukai suka bar parlon…ita Nafee kunyar rungumar da Layla tayi mai ne yasata barin parlon..bata San me yasa takejin nauyin hakan ba yanxu dukda ba yanxu ya fara hugging dinta a gabanta ba…ita Kuma Ramla nauyin Taheer din takeji tunda ba wani sabawa sukai dashi ba…tsakaninta dashi gaisuwa ne kawai..bai sakewa da yara sbd baya son raini…Layla ce kadai dama tun tana karama yake sakewa da ita fiyeda kowa…ashe Kuma kauna ce tsakaninsu basu saniba…
Ummi kuma na dubanshi da kyau tace”ni duk ban fahimci me kuke cewa ba..waye yake sonta Kuma”…sai yanzu umma ta fara bata lbrin duk abubuwan da suka faru…ummi tayi mamki sosae..sai Kuma tace”Amma dai wnn yarinya akwai Mara mutunci…taketa kulla makirci haka kan kankanuwan yarinya ‘yar cikinta..to Allah ya kiyaye gaba..ita Kuma Allah ya shiryeta”
Karfe 7:30 daidai Taheer yayi sallama dasu snn ya tafi airport…duk ranshi a bace yake sbd bazasu koma yau ba…knn hakan na nufin Layla zata sake missing zuwa school gobe Monday..yanayin mgn Kuma yasan ummi zata hau shi da fada..
Washegari suma karfe 7 suka kama hanya…sunaso su isa Abuja da wuri sbd Nafeesa da yara jirgin 6 zasubi zuwa porthacourt tunda yaran basu samu hutun makaranta ba.
Basu suka isa Abuja ba sai ana sallahn azhr..bayan sun karasa gida kowa ya kama dakinshi don ya dan huta… already dama mama Hauwa tayi musu girki don haka suna gamawa suka fito cin abinci…bayan sun gama sai suka koma parlor…Taheer ya Kira umma take sanar dashi sun sauka…yace zai zo gidan idan ya baro clinic.