Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Karfe 5 ya baro clinci ya nufo gidan..dama already su Nafee sun gama shiryawa daukansu kawai yayi bayan sun gama sallama da su ummi snn suka nufi airport…kafin su shiga jirgi Nafeesa ta samu ta janyo Layla gefe snn ta bude hand bag dinta tareda dauko wani leda a ciki ta mikama Laylan…ba musu Layla ta amsa tana kokarin tambayan menene Nafeesan tace Mata”ki ringa damawa da madara kullum kinasha safe da yamma..tun tuni nakeso in baki to ban samu kebewa dake bane…da akwai tsumi shima yanada kyau sosae zan aiko dashi gidan Ramla sai kije can ki amsa..Kuma ki tabbata kina amfani da ruwan zafi and ki yawaita Shan fruits don naga mijin nn naki chewing gum ne”…cikeda kunya layl tayi kasa da kanta jin abinda mamin tace…Nafeesa tasa hannu tareda dago fuskan nata tace”ke ba kunya tsakanina dake wnn shine kadai gatan da zan iya yi maki..kuma dn Allah Layla kiyi kokari ki ringa amfani da shawarwarin da Muka baki kinji…Ina Kara jaddada maki banda raki banda gudun miji Layla sai kin dage sosae inba hakaba duk wnn soyayyan da ake maki zaa dena..duk magungunan dana aiko maki dasu Kuma ki tabbata kina amfani dasu yanda ya kamata..Allah ya karo zmn lfy ya kawo zuri’a dayyiba”…tana rufe baki sai kawai taji Layla tayi hugging dinta tana hawayen farin ciki tace”thank you so much Mami..I love you”…Nafeesa ta dagota tana murmushi itama tace Mata”I love you more sarkin kuka..yanzubari mu tafi sai munyi waya”…Layla ta daga Mata kai har yanxu bata dena murmushi ba…ganin su Al’ameen na nufo inda suke Nafee tace”yi maza kisa wnn abun a jaka..Kuma ba cewa nai kije kiyita sha a gabanshi ba..karma ki kuskura yasan kinashan wani mgni kina nija”…Layla tasa maganin a hand bag dinta tareda daga Mata Kai…daidai su Al’ameen suka karaso nn ta akam hannun hibba suka nufi jrigin da zasu shiga..dama sun riga sunyi sallama da Taheer din…ita Kuma Layla juyawa tayi zuwa inda yake jiranta..ta bude mota ta shiga shima ya shiga snn suka dauki hanyan gidansu don sun riga sunyi sallama dasu ummi…
A kan hanya yake fada Mata yayi mgn da AY Gambo ya Kuma amince zaiyi Mata make up din..bama ita kadaiba duk Wanda sukai missing test din zaiyi musu…gobe idan sunje school zai fada musu date da Kuma time da zasuyi…Layla taji dadi sosae har batasan time din da ta matsa jikinshi tareda manna mai kiss a kumatunshi ba…Taheer na murmushi yace Mata”Allah baby idan kikasa mukai accident ba ruwana..bakisan effect din wnn kiss din naki ba koh”..Layla na smiling har yanxu ta juya idanunta tana cewa”Kai daddy..yanxu dan wnn peck din ne zaisa muyi accident”…tana rufe baki Taheer yace”bazaki gane bane baby..komai naki is special..komai naki is different..shiyasa dan abu kadan zakiyi ya kaimin karo..sbd haka a taimaka a dena juyamin idanun nn ki bari idan muka isa gida sai ayi duk abinda zaayi..har kiss dinma yau sai kin koya mn”…ya karasa mgnr tareda kashe mata ido…ita Kuma ta saki murmushi mai sauti snn ta maida hankalinta kan titi..har cikin ranta taji dadin mgnr daya fada..wai Abu kadan zatayi yake kaimai karo…hmmm gsky daddy sai a barshi…
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
48
Haka kwanaki sukai ta gangarawa suna zama satika..satika Kuma suna komawa watanni…yayinda tuni Layla sun gama exams sunyi hutun 3 weeks har sun sake juyawa second Semester wanda itama tana gab da karewa.. karatu sukeyi ka’in da na’in don Layla gani takeyi da kmr ma ba karatun sukayi ba…
Friendship dinsu da Hanna kuwa kullum Kara karfi yakeyi…cikin hutun da sukayi Hanna tazo gidanta..itama Kuma taje nata gidan don basu taba zuwa gidan juna ba.
Tsakaninta da Taheer kam zaace Alhamdulillah don soyayyane mai karfi ya sake shiga tsakaninsu..yana kulawa da ita sosae itama Kuma tana tattalin kayanta..duk abinda yakeso tana iya bakin kokarinta taga tayi mai shi…snn ta dena kin amincewa dashi..zuwa yanxu tasan dadin harkan sosae saidai shagwaban ne dai har yanxu ana nn ana tabawa…suna concentrating kan junansu sosae wanda hakan ke sake karfafa kaunar dake tsakaninsu..
A bangaren girki sai Hamdala don zuwa yanxu zaa iya kiranta very good cook sbd yanda ta maida hankali sosae da sosae..Kuma Alhamdulillah yanxu ba kalan abincin da bazata iya yiba..dama komai na duniya saidai mutum baisa kanshi zai koya ba.
Yau ya Sunday gaba dayansu suna gida..shi Taheer yana parlon sama yana aiki cikin laptop dinshi ita kuma daga shiga daki ta dauko wayanta kawai ta bigire a wurin tana bacci…Taheer ya ajiye system dinshi ya nufi dakin nata don gani abinda ya hanata fitowa tun daxu…da mamaki sosae yayi tsaye yana kallon yanda take baccin hani’an…rabin kafanta na kan gado sauran rabin Kuma na kasa…ya karasa kusa da ita a hankali tareda zaunawa kusa da ita…a hankali ya kamo hanunta daya ya rike cikin nashi…idanunshi Kuma nata aikin zagaye face dinta da kallo…hannunta dake cikin nashi ya saki snn yasa hannun ya dagota daga kwancen da take tareda dorata kan laps dinshi…ta bude idanun a hankali tana kallonshi sai Kuma ta turo baki tana fadin”bacci nakeji plss”…yana girgiza mata kai yace”bazan bari kiyi bacci ba da yamman nn baby..tashi muje parlor in kunna maki movie ki kalla”…a hankali ta sake turo bakin tace”nidai aah pls..I want to sleep”…Taheer yayi shiru yana kare Mata kallo kawai…lokaci daya Kuma sai ya saki murmushi snn ya mike zuwa closet dinta ya dauko Mata zumbulelen hijab ya dawo inda take ya shiga sa Mata hijab din…Saida ya gama sa Mata snn ya dagata cak yayi waje da ita…ya sauka downstairs snn ya fita waje…ya bude mota ya sanyata ciki snn ya sake komawa ya kulle gidan snn ya koma wurin motan shima ya shiga…har yanxu kuma Layla bacci take…shiko yana driving yana juyowa yana kallonta..har yanxu murmushi yakasa barin face dinshi…addu’a yake Allah sa abinda yake zato ya zama gsky…
Saida ya isa clinic dinshi snn yayi parking…ya juyo yana kallonta tareda kamo hanunta guda daya ya manna mai kiss..sai ta shiga bude idonta a hankali…sai Kuma ta mike zaune tana kalle kallen wurin tace”daddy inane nan?..”a nutse yace daita”Clinic”…ta sake turo baki tace mishi”daddy ni ka kaini mu siyo ice cream din da kace zaka siya mn..yunwa nakeji”…Taheer ya lumshe ido tareda dora dayan hannunshi kan flat tummy dinta yace”no more Shan ice cream baby..I can’t risk loosing my child”…ta sake turo bakin tace”I promise you won’t loose me daddy..kawai inaso insha ne”…dariya sosae Taheer ya saki jin abinda ta fada..wato ita batama fuskanci abinda yake nufi ba knn…Saida yayi me isarshi snn yace mata”kiyi hakuri baby Shan ice cream ya Kare”…kmr zatasa kuka tace”why daddy”…yace”na fada maki bazan iya bari wani abu ya samu child dina ba”…tace”to daddy tun da can da nakesha wani abu bai sameni ba sai yanxu”…Taheer ya lumshe ido ya bude yace Mata”wacece ke a wurina”….a hankali tace”your baby”…yana shafa cheeks dinta yana murmushi ya Kai bakinshi daidai kunnenta snn yace”yes you are my baby and not my child..am talking about my very own flesh and blood”…lokaci daya Layla ta zare idanu tana kallonshi tace”ban gane ba daddy”….Taheer ya kai both hands dinshi ya dora kan cikinta..idonshi cikin nata yace” I think you are pregnant”…sake zare idanun tayi tana girgiza kai tace”kmr ya pregnant daddy..ni wlh ban gane ba”…Saida ya saki murmushi mai sauti kafin yace Mata”I mean you are carrying my child..my own blood”…yana rufe baki Layla ta fashe da wani irin kuka hadda dora hanu a kai tana fadin”na shiga uku na lalace..shknn yanxu bazan samu daman cigaba da karatuna ba..wayyo Allah na wayyo Mami wayyo ummi wayyo umma wayyo dan Allah ku taimakeni”…Taheer yayi azaman sanyata jikinshi gamida toshe mata baki..yana dariya kasa kasa gamida bubbuga bayanta da daya hanunshi yace mata”menene abun kuka Kuma baby..what’s the meaning of wnn ihun da kikeyi”…yana gama mgn tace”daddy ciki hana karatu yakeyi wlh”… yace”how do you know?..”tace”friend dita Hanna tunda ta samu ciki har yanxu bata iya yin karatu sosae..kullum cikin rashin lfy take nasan nima shknn nawa karatun yazo karshe”…Taheer na murmushi yace”come on baby ya kike mgn kmr ba medical personnel ba..laulayi ai kowa da irin nashi..maybe ma ke bazakiyi laulayin ba..kuma ana fita daga first Trimester ake samun sauki ai”…tace”dukda haka daddy nidai am scared”…ya dagota daga jikinshi tareda cupping fuskanta yace mata”don’t be scared..abin da ma bamu tabbatar da cikin ba..shiyasa na kawoki clinic sbd ayi test mu gani”…ya fada mata kawai don hankalinta ya kwanta amma for sure yasan ya hango karamin ciki a tattare da ita(kunji sai kace maye????da gaske doctors nada wnn talent din..akwai wani doc da na taba aiki dashi a wani asibiti..irin yana duba out patient sai wata Mata ta shigo itama mara lfy ce amma ko complaint dinta bai gama saurara ba yace a rakata ward a bata gado..idan yazo yin ward round da safe zai dubata..matar tana fita doc din yace min”she will die”nidai bance komai ba sbd inaga kmr he’s lying..wlh the next day Ina shigowa ward din naga ana fitar da gawa..nace wace ta mutu akace patient din Dr.Ishaq yayi admitting jiya????nayi mamaki sosae..so da gaske doctors are amazing????suna iya gane Abu without conducting any test)