Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A haka ya bude mota ya fita snn itama ya bude mata ta fito..ya kama hanunta cikin nashi suka shiga clinic din…mutanen dake cikin asibitin sukaita kallonsu suna ‘yan kuskus dinsu..wasu sun san ya aureta wasu Kuma basu sani ba…har suka shiga elevator hanunta na cikin nashi…suna fita daga ciki Kuma suka shiga office dinshi…ya zaunar da ita kan 3 seater snn yayi using landline dake office din ya kira Central Lab kan su aiko mai da Sample bottle akwai test da yakeso ayi mashi emergency…ba bata lokaci kuwa daya daga cikin ma’aikatan lab din nashi yazo da sample bottle hadda su tourniquet da 5cc syringe Wanda zaiyi amfani dasu wajen daukan sample din…Taheer da kanshi ya karba snn ya dauki blood sample din nata da kanshi…tanata rusa kuka kmr wanda akaima operation…shi Kuma Taheer ya bada sample din yace PT yakeso ayi yanxu yanxun nn…ba musu guy din ya karba snn ya fita tareda komawa lab din..
Shi Kuma Taheer ya karasa kusa daita ya zauna tareda sanyata jikinshi..yana shafa bayanta yace”am sorry kukan ya isa haka”…yana rufe baki tace”daddy wlh akwai zafi”…yana dariya gamida girgiza kai yace”wnn idan akazo labour ban San ya zaayi ba”…aiko ta sake rushewa da kuka hadda su bubbuga kafafu…ya kama kafan nata da sauri shima kmr zaisa kukan yace mata”baby mana..don’t harm our baby da wnn buga kafafun da kikeyi”…itadai tana cigaba da kukanta..sai ya rungumeta gam ya shiga hura Mata iska cikin kunnenta kafin yace”to am sorry kiyi hakuri kinji..am so sorry bar kukan”

After like one hour aka kawo mai result din..ya karba snn ya shiga bude papern a hankali..idanunshi suka sauka kan inda aka rubuta Positive sai daga kasa Kuma aka rubuta 2/12 Amenorrhea…rungume takardan yayi sosae lokaci daya Kuma hawayen farin ciki suka wanke mai fuska..yanxu shine zaiyi Dan kanshi..baby zata Haifa mai ‘da…”Alhamdulillah ya Allah.. Astagfirulla…Subhnallah… MashaAllah…La’ilaha illallah”…abubuwan da yaketa maimatawa knn kmr zautacce..duk addu’an dayazo bakinshi yi yake Kuma har yanxu yana rungume da papern yana hawaye…Layla dai na zaune gefe tana kallon ikon Allah..sam batayi tunanin kukan farin ciki bane ita a tunaninta cikin ne babu shiyasa yake wnn kukan…shi kuma Taheer mikewa yayi da sauri tareda zagayowa tsakiyan office din ya fuskanci Qibla kawai sai ya durkusa ya fara sujoodushshukhoor…yi yake yana karawa har yanxu Kuma bakinshi bai bar furta Hamdala da salati ba…Saida ya gama snn ya mike tareda karasowa inda take ya mikar da ita tsaye kawai sai taji yayi hugging dinta so tight kmr zai maidata cikinshi..hawayenshi na sauka kan kafadanta yake cewa”baby it’s positive..it’s positive baby you are two months pregnant..you are carrying my own child baby thank you so much.. thank you so much baby I love you very much”…sai Kuma ya saketa da sauri tareda durkusawa nan kasa..a hankali yakai hannu tareda daga riganta sama…ya shiga mannawa cikin nata kisses all over har yanxu Kuma bai bar hawayeba..he just can’t believe shine zaiyi ‘dan kanshi from this loving soul..wato a duniya samun ‘da ko ‘ya from the woman da kake mugun so a rayuwanka is blessing..he can’t thank Allah enough for all these..He’s forever grateful…Saida ya gama kisses din nashi snn ya kama cikin da duka hannayenshi..fuska daukeda tsantsan farin ciki yace”your Papa loves you so much..I can’t wait to hold you…inaso ki zama good girl okay.. this mummy of yours is somehow stubborn..I want you to be a good girl kar ki ringa hanata yin karatu kinji”..sai Kuma ya sake kissing cikin nata yana”I love you so much”…Layla dai tsuru tayi tareda zubawa sarautan Allah ido…zuwa yanxu ko baa fada ba tasan the result was positive…ganin yanda yake mgn da cikin da Kuma hawayen da yake yatabbatar Mata he’s very Happy…at this point itama sai taji she’s happy..duk abinda zai sanyashi farin ciki haka ba karamin Abu bane..kuma tana son duk abinda yakeso don haka itama sai taji tana kaunar cikin..she just can’t wait ta haihu taga dawa babyn zaiyi kama…ta daga ido tana kallonshi with a smile tace”wane yace maka it’s a girl..ni baby boy nakeso wanda zaiyi kama dakai”…tana rufe baki Taheer ya sake hugging nata yana cewa”no baby InshaAllah it’s a girl..I want a baby girl just like you..I want to pamper and spoil her kmr yanda nayi maki”…dariya kawai ta saki without saying a thing…shi Kuma ya mike tareda kama hanunta yace let’s go dama abinda ya kawo mu knn…ba musu ba bishi a baya..Saida yayi locking office din snn suka shiga elevator da zai maidasu 1st floor…suna fita ya sake kama hanunta har cikin mota…ya bude motan ya shiga bayan itama ya sanyata a ciki…har zai tada motan Kuma yaji bazai iya tafiya without telling umma wnn good news ba…don haka ya zaro phone dinshi tareda dialing number dinta…tana picking yace Mata”Ummata Albishirinki”…a daya bangaren umma tace”goro”..yace”am going to become a father soon”…umma ta dan wara ido sai Kuma tace”ban fahimceka bafa”…yace”Umma baby is pregnant.. two months pregnant..we are going to become parets umma ki tayamu farin ciki”…Umma da lokaci daya farin ciki da jin dadi suka lullubeta tace”Taheer are you serious..banason wasa fa”…yace”wlh umma da gaske nake…ai bazan taba maki irin wnn wasan ba”…umma tace”Alhamdulillah Alhamdulillah..Allah ya raba lfy Taheer ubangiji Allah yayi mai albarka ita kuma Laylan Allah ya bata lfy”… yace”Ameen Umma”…kafin ya sakeyin mgn tace mai”Kai kyaleni inje in bama Yaya good news..I will get back to you”.. daga haka ta kaste Kiran..shima Taheer ya ajiye wayan nashi har yanxu yana murmushi snn ya tada mota suka tafi…
Saida suka hau kan titi snn yace Mata”baby me kikeso kici..name it..ko menene dole ma in nemo maki shi”…Layla ta rausaya Kai snn tace mai”ni ice cream nakeso”…ya shiga girgiza kai yace”banda ice cream plss..ki fada wani abun dai”…tayi raurau da ido alaman zata sa kuka tace”nidai shi nakeso”…kai ya sake girgizawa yace”dn Allah baby ki fadi wani abun..banda ice cream plss..I don’t want my baby to catch cold tun bata zo duniya ba”…yana rufe baki sai ta rufe face dinta da hannayenta ta shiga rera mai kuka…da sauri ya gangara gefen titi yayi parking tareda kamota jikinshi…a tausashe yace mata”baby dan Allah stop..why zaki fara kuka kan such a minor issue”…tana cigaba da kukan tace”it’s not minor..ni ice cream kadai nakeso kuma idan baka siya min ba bazanci abinci ba wal”..tun kafin ta karasa ya rufe mata baki da hannunshi…kmr zaisa mata kukan shima yace”baby na shiga uku..why zakice baza kici abinci ba..do you want to sterve my child”…ta dan dakatar da kukan da takeyi tana turo bakinta kmr zai bar muhallinshi tace”nidai ka siya min ice cream dina”…tana rufe baki yace”zan siya maki baby amma karami..Kuma daga yau karma ki sake cemin zakisha ice cream don bazaki sha ba..bazan bari kiyita dirkama yarinyata sanyi tun tana cikin ciki ba”…tace”to nidai muje a siyo min”…Saida ya maidata seat dinta snn shima ya koma nashi yaci gaba da driving..yanayi yana kallonta…

A Cold Stone suka fara tsayawa don siyan ice cream din..bayan sun shiga ciki ya juya yana kallonta yace”which flavour kikeso?..”da sauri tace”inason chocolate da vanilla..snn inason strawberry and daddy dn Allah ko 5 Scoops ne banason Dan kadan plss”…baice mata komai ba kawai ya zaro atm dinshi…shi Kuma mutumin dake wurin ya shiga hada mata flavours din da tace tanaso…bayan an gama hada mata anyi packaging Taheer ya amsa..snn suka fita daga wurin bayan sun cire kudinsu through his card…tun a mota ta bude ice cream din ta fara sha kmr Wanda ta dade basa komai a bakinta ba…Taheer dake driving sai juyowa yake yana kallonta..Sam baa son ranshi take Shan wnn ice cream dinba..gani yake kmr sanyin zaiyi affecting babynshi..baison komai ya samu babynshi..he wants her to stay strong and healthy in her mother’s womb..Sam bai son abinda zaisa yayi risking life din child dinshi amma baby is trying to be stubborn..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button