Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A bangaren Ummi da Umma kuwa farin ciki baa mgn..tun a jiya ummi ta kira Nafee da kanta take sanar da ita lbrin cikin…ita kanta tayi farin ciki fiyeda tunanin mai karatu..Allah ya sani tana masifar son union din Layla da Taheer..kuma samun karuwa daga garesu ba karamin karfafa zumunchi dake tsakaninsu zaiyi ba…bayan Nafee ummi duk Saida ta kira duk Wanda take ganin sun Dace su San da mgnr cikin ta fada musu..she’s over excited zata samu jika from her only son..da kuma grand child dinta data raineta tamkar ‘yarta.
Wajen karfe 10 ta shiga kiran wayan Taheer..lokacin yana office dinshi yana duba outpatients Kiran nata ya shigo…baiyi picking ba Saida ya sallami patient dake gabanshi snn ya kirata back..Yana shiga unmi tayi picking..Taheer yace mata”Ina kwana ummi”..tace”lfy qlou Taheer ya aikin”…yace”Alhamdulillah ummi”..tace”Congratulations naji good news a wajen Aisha..Allah ya raya manashi Allah ya kawo manashi lfy”…cikeda farin ciki yace”Ameen Ameen Ummi”…ummi Kuma tace”yanxu Ina Laylan take”…yace”tana school”…tace”to idan ka daukota daga school din ka kawota nan gida Ina son ganinta”…yace”ba matsala InshaAllah zan kawota”..daga nn sukayi sallama..
Ita Kam Hajia Layla tana shiga class dinsu taji ana announcing Lecturer din da zai shigo musu yanxu yace suyi hakuri bazai samu zuwaba..amma zaiyi fixing wani time din…ana fadan haka mutane suka fara fita daga class din..kowa Yana tafiya sabgar gabanshi…ita kuwa Layla karasawa tayi inda Hanna ke zaune itama ta zauna..tana dubanta cikeda tsokana tace”sannu mai ciki”.. Hanna ta galla Mata harara itama tace”masu ciki dai..ko kina tunanin duk boye boyenki ban gane kinada ciki bane”…Layla tace”gsky kinada sa ido..to ni kaina ban San da cikin ba sai jiya..haka kawai daddy ya daukeni mukaje clinic akayi test sai gashi har two months”…Hanna na dariya tace”Ni dama wlh naga alama..kinga yanxu sai ki denamin iskanchi kema gashi nn kin gamu..gara ma ni yanxu wata na 6 nake ke kuwa yanxu ma zaki fara”…Layla ta girgiza kai kawai kafin tace”amma nifa bana rashin lfy..ko zazzabi ban tabayi ba wlh..saidai kwadayi da Kuma bacci shima ba sosae ba”…Hanna tace”aikam Allah ya taimakeki don laulayi bashida dadi kwata kwata..yanxu zuwa next session duk mun zama mommies..oh I can’t wait”…dariya Layla tayi sosae kafin tace”gsky Hanna bakida kunya..wato har wani lissafi ma kike”…tana rufe baki Hanna tace”Kai kinsan dadin ‘da kuwa..Tabb ai wlh ni na matsu ma in haihu ko don in ringa kallon ‘dana ko ‘yata inajin dadi..ai haihuwa tayi a rayuwa..in inada ‘da ko miji ne ya batamin rai banjin haushi..ina kallon ‘dana zanji duk damuwana ta yaye..Allah kada ka jarabcemu da rashin haihuwa alfarmar Annabi da Alqur’ani”…Layla na murmushi tace”Ameen Ya Allah”…sai Kuma ta fara tunanin farin cikin data gani tattareda Taheer jiya..ta tuna yanda ya ringa hawaye yana maganganu kmr mara hankali..mgnr Hanna gsky ne..haihuwa tayi..Hakika duk Wanda Allah ya jarabceshi da rashin haihuwa Yana ganin babban jarabawa a rayuwarshi..Allah kayi mana tsari da jarabtar rashin haihuwa..ubangiji ka azurtamu da ‘ya’yaye na gari ba don halayen mu ba..”
Shiko Taheer yana clinic amma daidai da second daya hankalinshi bai bar kanta ba..bini bini ya kirata a waya”baby are you alright..kina bukatan wani abu..ba inda ke maki ciwo..ki kulamin da kanki da my little one plss”…Layla har Saida ta gaji da bashi amsoshin wdan nn tambayoyin..daga safe zuwa yanxu ya kirata kusan sau 20 Kuma duk mgn dayace yaketa nanata Mata har ta gaji da daukan wayan nashi ma..
Tana gama lectures ta kirashi don ta fada mai ta gama sai kawai yace mata ai yana cikin school dinma tun dazu yana jiranta…haka ta nufi inda tasan zata sameshi tana mamaki..ko wa ya barowa aikin nashi oho.
Tana karasaw inda yake dama already ya fito ya bude mota..yana tsaye wurin ta karaso tana kokarin shiga motan kawai taji ya sanyata a jikinshi…ta zame jikinta da sauri tana kalle kalle tace”haba daddy..yanxu idan wani ya ganmu fa”…Saida ya sata cikin mota snn yace”I don’t care..koma wane zai gani ya gani..you are my wife afterall..so inada right din inyi hugging dinki ko a inane”..ya rufe motan snn shima ya zaga ya shiga..maimakon ya tada motan su tafi sai ya sake matsowa jikinta a hankali ya dage hijab dinta da Kuma rigar jikinta..cikinta dake nn a shafe ya bayyana…ya lumshe idanu snn ya dora hannayenshi kan cikin..Saida ya manna kiss a wurin snn yace”your Papa missed you alot”…Layla dai binshi kawai takeyi da ido..har yanzu bata dena mamakin wnn kauna da yakema cikin nn ba…shi kuwa yana gamawa sai ya koma seat dinshi snn ya tada motan suka tafi…tadan daure fuska tana kallonshi tace”shine ni bakace kayi missing dina ba sai cikinka koh”…yace”shiyasa na farayi maki naki tun a waje sbd nasan zakice nayi son kai amma duk da haka ban tsira ba”…ta murguda baki tace”ai ni bakace kayi missing dinaba sai ita..I mean sai shi”…Saida yadan juyo ya kalleta fuska daukeda murmushi yace”ai na fada maki InshaAllah it’s a girl..so kima dena alakanta min ita da namiji”…yana rufe baki tace”aiko in Allah ya yadda namiji zan Haifa..sai muga ta tsiya”…Taheer ya fashe da dariya yana cewa”ko namijin nema ai ba kinshi zanyiba baby..I will love them equally..kawai dai nafiso in fara da mace ne sbd tana fara girma inyi mata aure in samu jikoki..and I want to spoil her kmr yanda nayi spoiling dinki..shknn”…murguda bakin nata ta sakeyi tareda juyar da kanta tana kallon titi…shi kuma yayi murmushi Yana cigaba da driving dinshi.
Suna isa kofar gidan yayi horn aka bude mashi gate snn ya shiga ciki…ya samu wuri yayi parking snn ya fito..ya zaga ya fitoda ita itama snn suka nufi cikin gidan…suna shiga parlor ummi ta taso da sauri ta rungume Layla a jikinta tanata sambada mata albarka…Taheer ya karasa ciki ta zauna kusa da umma yana murmushi…itama ummi ta kama hanun Laylan suka zauna snn Taheer ya gaishesu..itama Laylan ta gaishesu for the very first time taji kunyansu takeji duka..yanxu shknn da ance tanada ciki kowa yasan yanda akayi aka samu cikin..Gosh wnn abun kunya da yawa yake..ummi na duban Taheer tace”sai ka biyota da kayanta ko zuwa gobe ne”…Taheer ya buda ido sosae kafin yace”ban gane in biyota da kayanta ba ummi..me zatayi da Kaya a nn gidan kuma”?..”ummi tace”ai ba komawa zatayi ba Taheer..zata zauna a nan don mu ringa kulawa da ita da abin dake cikinta sosae..idanma an barka da ita ba wani iya kula dasu zakayi sosae ba”…tana rufe baki Taheer ya shiga girgiza kai yana cewa”ummi kar kimin haka dn Allah..ya zakice bazan iya kula dasu ba..ni likita nefa ummi nasan duk abinda ya kamaceta da Wanda bai kamaceta ba..dn girman Allah ummi kar kice zaki rabani da matata nidai zan iya kula dasu wlh”…shiru ummi tayi tana kallon wnn magiya da yake Mata haka..kafin tayi mgn umma tace”don Allah Yaya kiyi hakuri ki kyaleshi kawai ya kulada matarsa..nasan zai iya wlh..ai shi ba yaro bane snn yanada ilimin da zai iya kulawa dasu sosae..ki barsu suje inyaso idan cikin ya tsufa sosae a ta dawo nn din sbd haihuwa koh”…ummi dai har yanxu shiru tana tunani cikin ranta..gani tayi mgnr da umma ta fada gsky ne..sai tace”shknn..amma duk take bukatan wani abu sai ka Kira ka fada..shi sha’anin mai ciki bada wasa ake daukansa ba”…Taheer ya sauke ajiyan zuciya a boye before yace”yawwa ummina ko kefa.. thank you so much”…harara ummi ta watsa mai tana cewa”bakada kunya wlh..Ni ban san time din da ka lalace haka ba”..dukkaninsu suka sa dariya.