Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Basu suka bar gidan ba sai around 10..suna komawa gida Kuma kowa yayi shirin bacci snn suka kwanta tunda already sunci abinci a can kafin su taho…suna kwanciyan Kuma bacci yayi gaba da Layla..shi kuwa Saida ya dade yana nn zaune yana kallonta yana Kuma mgn da cikinta kmr tababbe kafin shima baccin ya silola yazo yayi gaba dashi.
Alhamdulillah am back sweethearts..nagode sosae da add’u’o’iku gareni..Allah bar love????
Mum Ashraf ✨
????Dr.TAHEER????
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
50
Haka rayuwa yacigaba da tafiya Layla na samun kulawa sosae..ba bangaren su Ummi ba..ba kuma ga bangaren daddyn nata ba..wasu lokutan har tausayi yake bata yanda taga Yana kaunar cikin nn..sai yasa cikin a gaba yaita surutunshi shi kadai yana murmushi shi bai yadda ba yana mgn da babynshi…kullum zai kaita school snn zai maidata gida…duk take sha’awan cin wani abu kuwa tana kiranshi duk inda yake Kuma duk abinda yake haka zai bari yazo ya kawo Mata…suna rainon cikinsu sosae Kuma bai hanata karatunta tunda ba wani laulayi takeyi sosae ba..
Kayan babies Kam Taheer na siyansu tamkar bai San zafin neman kudi ba…duk abun da ya gani yai mishi kyau sai yayi order indai abindaya danganci yara ne…banda Wanda kusan kullum sai ya dauketa sunje shopping Kuma duk siyayyan na kayan babies ne…duk abinda zai siya kuma na Mata yake dauka…Layla tayi tayi dashi akan su ringa daukan unisex yanda ko ba mace ta Haifa ba zasuyi amfani dashi amma inaa…kullum cewa yake shi jikinshi na bashi mace zata Haifa dukda scanning din da sukai guda biyu duk namiji yake nunawa..
Lokacin da cikin nata ya isa antenal kuwa da kanshi yakeyi Mata komai…duk wasu tests da akeyi yana Mata…har su urinalysis Yana zuwa da Combi9 dinshi har gida yayi Mata…sauran tests din Kuma irinsu PCV..VDRL da bazasu yiwu a gida ba sai ya dauketa suje clinic dinshi ayi Mata…Layla dai na ganin tsabar soyayya da kulawa a wurin Taheer..at times har tunani take kilan tana haihuwa zai dena sonta ya dena kulawa da ita..sbd yanda taga yake bala’in son cikin nn abin har mamaki yake bata..
A bangaren su Ummi ma Kam baa barsu a baya wajen kulawa da ita ba…time to time ummi zatayi Mata girki irin na gargajiya Wanda tasan mai ciki zataso snn suje har gidan su Kai Mata..watarana Kuma su aika driver yakai ko Kuma Taheer din yaje ya amsan Mata…babu abinda zatace ma Allah daya wuce Alhamdulillah.. kullum cikin godiyan Allah take for such a blessing…fatanta Allah ya sauketa lfy itama taga me zata Haifa..tanaso taga babyn da ita zaiyi kama koda babanshi..
Lokacinda Hanna ta haihu cikin Layla nada watanni 5 ciff a duniya…zuwa lokacin Kuma cikin nata ya fito sosae…haka sukasha suna da katoton cikinta abunta…yarinya taci sunan mum din mahaifinta Aisha..zasuna kiranta da Hanan…
Bayan haihuwan nata da kadan Kuma sukayi exams na second semester…wnn karon zasuyi hutun 4 weeks kafin su juya another session…haka rayuwa yacigaba da tafiya musu har zuwa yanxu da cikinta ke wata takwas…yana shiga na takwas din dama ummi ta dage kan lallai sai Taheer ya maidota gida don ba iya kulawa da ita zaiyi ba..haka ya hada kayanta da nashi snn suka tattara suka koma gidan…shima hankalinshi zaifi kwanciya idan tana tare dasu don sau tari idan zaije clinic hankalinshi bai kwanciya ya barta ita kadai a gida..yanxu kuwa ko bai nan yasan zasu kula mai da ita sosae.
Dukda suna gidan kuma bai fasa kulawa da itan ba..duk abubuwan da yake Mata a baya ba Wanda ya bari..ko abinci indai yana gida saidai ya bata a baki..wasu lokutan har kin zuwa aiki yakeyi sbd ita..daidai da wanka saiya taimaka mata tun ummi na fada har ta hakura ta zuba musu idanu kawai…yanda yake rawan jiki kan cikin nn har mamaki yake bata..sai kace a kanshi zaa fara haihuwa..ita kuwa umma sam bata mamaki don ta riga tasan irin kaunar da Taheer din kema Layla..dn haka dolene tasan yaso cikin nn fiyeda komai…
Nafeesa kam har yanxu bata samu zuwa Abuja ba sbd karatun yara..tanata so tazo ko kwana biyu ne suyi sbd ta samu taga Layla amma umma tace suyi zamansu kawai..idan Allah ya sauketa lfy sai suzo..saidai suna wayan kusan kullum da ita…haka su Al’ameen ma duk sun kagu ta haihu suzo suga babynsu…
Yau Saturday da wuri Taheer ya baro clinic zuwa gida..tun da ta fita bai samu yin waya da itaba as yanata Kiran wayan nata bata answering..gaba daya sai hankalinshi ya tashi don yana tunanin ko wani abun ne ya sameta amma daya Kira umma sai ta tabbatar mai da cewa lfy Lou take saidai tun dazu tana daki tanata bacci…dukda haka shidai baiji hankalinshi ya kwanta ba don haka ya dawo gidan don yaga hakinda take ciki.
Su ummi suna parlor suna duba uban kayan babies da sukai order tun last two weeks shine yanxu akayi delivering dinsu…ya gaisa dasu a gurguje snn ya wuce zuwa dakinta don gaba daya hankalinshi na kanta…tana zaune tsakiyar gado ta dora kanta a kan kafafunta tana rere kuka a hankali…da sauri ya karasa gareta hankali a matukar tashe yace”baby what is it?..bakida lfy ne?..”Layla banza tayi dashi tana ci gaba da kukanta…yasa hannunshi ya dagata cak snn ya zauna gefen gadon tareda dorata a kan cinyanshi…ya riko face dinta da hannayenshi yace mata”baby please..what is wrong with you”…a hankali ta dora tiny hands dinta kan nashi tace”daddy am tired plss..ka cire mn cikin nn don Allah..wlh na gaji daddy kullum bana samu inyi bacci..bana iya yima kaina komai dubi fa ko zip din rigana kasa zugewa nayi..nidai na gaji wlh”…Taheer lumshe ido yayi tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya..duk a tunaninshi ko batajin dadi ne…ya dora kanta a chest dinshi yana shafa gashinta har yanxu Kuma idanunshi na rufe yace mata”baby ba mun gama da mgnr nn ba..na fada maki saura kadan ki Kara hakuri kinji..nasan kina kokari amma dn Allah ki kara akan Wanda kike dashi..edd dinki na cika zanyi maki Cs in ciro abuna da kaina so ki dan kara hakuri kinji koh”…ta sake yin luf da kanta dake kirjinshi tace”daddy kullum sai yaita kicking dina yana hanani yin bacci..ko juyawa yayi sai naji zafi wlh”…ta karasa mgnr hadda su guntun hawaye a idonta…Taheer ya bude idanunshi dake rufe ya dago kan nata yana kallonta a hankali yace mata”kiyi hakuri kinji..lfy zaku rabu InshaAllah”…yana gama mgnr ya kama zip din maternity gown dake jikinta ya zuge Mata shi snn ya sake dago face dinta yana kallo yace”kinci abinci”…a hankali ta girgiza kanta…ya dora hannu kan cikinta a hankali yace”to me zakici”?…”ta wani kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”Fish”…Taheer ya dan wara idanu yana kallonta kafin yace”kifi dai baby?..”still fuskanta a kwabe ta daga mishi Kai…Taheer ya sauke numfashi before yace”alright bari in fita yanxun nn in samo maki shi”…da sauri tace mai”daddy ni zan bika”…yai shiru yana kallonta kmr bazai ce komai ba sai Kuma yace Mata”to tashi muje”…ba musu ta mike tsaye shima ya mike..ya dauko hijab dinta ya sa mata snn ya kama hanunta suka fita daga dakin..
Su ummi sun gama dudduba kayansu har sun maidasu daki…ummi na ganin Layla da hijabi a jiki tace”Kai badai wani wajen zaka kaita ba koh”…yace”kifi zamuje siyowa ummi”…ummi tace”wane irin kifi kuma ni Maryama..da tsohon cikin zaka wani kwasheta kuje siyan kifi”…Layla na turo baki tace”ummi nifa so nake in bishi..na gaji da zaman wuri daya”…daga haka ummi bata sake mgn ba…umma ce tace”to yanxu ta Ina zaku fara neman wani kifi Taheer”..yace”to umma tace shi takeso..dole haka zamu fita mu nema nasan InshaAllah bazamu rasa ba”…umma tace”Ay shknn sai Kun dawo”…yace”Ameen”snn suka fita suka tafi.