Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Saida sukai yawo sosae don Saida suka fara fita outskirt din Abuja snn Allah ya taimakesu suka samo kifin…tun a hanya ta faraci…
Suna isa wani super market yayi parking snn ya fita daga motan yace mata he’s coming…taci gaba da cin kifinta shi Kuma ya shiga ciki da sauri…sharp sharp ya dauko abinda yake bukata snn yazo ya biya kudin…Yana Shirin fita suka kusa cin karo da Sameera…yaja baya da sauri yana dauke kanshi daga gareta…ita Kuma sai ta saki dan smile tana cewa”doctor dama ana ganinku”…Taheer yayi mata banza yana kakarin fita daga wurin ta sake Shan gabanshi tace”dn Allah doctor duk abinda ya faru kayi hakuri..Sharrin shaidan ne wlh amma InshaAllah hakan bazai sake faruwa ba…ka yafemin”…Taheer ya matsu ta gama surutunta ta bashi hanya ya wuce yace”naji..now bani hanya in wuce”…da sauri tace”ai bakace ka yafemin ba doctor”…Taheer ya dafa goshi ganin tana neman bata mai lokaci yace”dn Allah ki bani hanya in wuce..da ban yafe maki ba kinsan baki isa in tsaya ma Ina sauraranki ba..so ki bani hanya in wuce before I loose my temper”

A cikin mota Kam Layla dake cin kifinta taga har yanxu bai fitoba sai ta bude motan ta fita…ita batama san abinda ya tsayar dashi a nn wurin ba…tana sa kai tun ma kafin ta shiga ciki idanunta suka hango Mata shi yana tsaye da Sameera..zuciyarta taji yayi wani irin bugawa da karfi..batasan lokacinda ta saki wayanta dake hannunta ba…lokaci daya Sameera da Taheer suka juyo jin karan faduwan abu a bayansu…daidai lokacin Kuma Layla ta juya tareda barin wurin da sauri kmr zata tashi sama…shima Taheer da saurin yabi bayanta yana kiranta amma batada alaman slowing down…Saida ya dauki wayanta da tayi wurgi dashi nn wurin sai yasa gudu snn ya iya kamo inda take…ya kamo hannunta ya rikeshi da karfi..idanunshi har sunyi jajawur yace mata”baby are you mad..kina haukane zaki fara irin wnn saurin bayan kinsan condition dinki..do you want to harm my child?..”a hankali Layla ta lumshe idanu wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska..wato shi baima ga girman laifinda ya aikata ba…ta danshi kawai yakeyi..bai damu da ko ita wani abun zai iya samunta ba…kawai sai ta kwace hannunta dake cikin nashi da karfi…kafin yayi yunkurin sake rike hanun nata ta sake juyawa da sauri wnn karon har tana hadawa da dan gudu ta doshi gate din wurin…ya sake binta da gudu yanajin yanda duk taku daya idan tayi jinshi yake har cikin ranshi don baison abinda zaiyi affecting ita ko cikin da yake jikinta…yana karasawa inda take kawai sai yayi hugging dinta gam..bai damu da yanda mutanen wurin keta kallonsu ba…idanunshi har sun ciko da kwalla yace”baby please…ki taimaka min ki dena gudun nn don Allah..mutuwa zanyi idan kika bari wani abu ya samu cikin nn..ki tausaya mn dn Allah..wlh ba abinda kike tunani bane”…ita dai idanunta na rufe ruf tanajin abinda yake fada sai zuciyarta ya sake dagulewa…ta shiga kokawa dashi tanason freeing kanta a hanunshi amma ta kasa…shi Kuma Taheer kawai sai ya dagata ya koma wurin motarshi da ita…duk yanda taketa dukan chest dinshi tana ya ajiyeta bai ajiyetan ba har sai daya karasa inda motar shi take ya sanyata a ciki snn ya zagaya da sauri shima ya shiga snn ya tada motar suka bar wurin.

Ko a hanya Banda kuka ba abinda takeyi Kuma mgnr da yake Mata har yanzu bata bashi amsan ko guda daya ba…a hankali ya gangara gefen titi yayi parking yana kallonta da idanuwanshi dake dab da fitar da kwalla yace mata”baby please..dn Allah kiyi hakuri ki tsaya ki saurareni..wlh ba abinda kike tunani bane..roko na takeyi in yafe mata ni Kuma nace na riga na yafe Mata..dn Allah ki dena kukan nn kinsan condition dinki…banason wani abin ya sameki ko ya samu unborn dina ki dena plsss”..idan ke da kike karatu kin tanka to Layla ma ta tanka…Taheer ya hada kanshi da starring motan yanajin yanda wani mashahurin zafi ke baibaye ko wace kafa ta heart dinshi…a hankali hawayen dake makale a idanunshi tun dazu suka samu damar zubowa a kan fuskanshi…Allah ya sani duk wnn kukan da take..da guje gujen da takeyi gani yake kmr zai iya affecting cikinta…shi kuma baison abinda zai sameta ko ya samu cikin nn kwata kwata..a hankali yasa hannu tareda goge tears din da suka zubo mai snn ya dago fuskan nashi yana kallonta…ya bude baki zaiyi mgn tace mai”na gaji..ka kaini gida in huta”…ba musu ya tada motan suka cigaba da tafiya…saidai gaba daya hankalinshi yana kanta…jin kukan nn nata yakeyi har tsakiyar kwakwawarshi…bai San me zai fada Mata ta yadda dashi ba Kuma..

Suna isa gida ko parking din kirki baiyi ba ta bude motan ta fita da saurinta…Taheer ya bita da kallo har ta shiga ciki…da kyar ya bude motan shima ya fita ya nufi entrance din gidan.

Umma ce kadai a parlor itama tana kokarin shiga kitchen sai ga Layla ta shigo a sukwane ta wuce dakinta tana sharan hawaye…umma ta bita da kallon mamaki ganin yanda take uban sauri ko nauyin jikinta bataji..sai kace ba mai ciki ba…ta sake juyawa zata shiga kitchen din sai Kuma ga Taheer ma ya shigo..sai ta dawo cikin parlon tana kallonshi da kyau tace mishi”Kai lfy..meyake faruwa?..”a hankali Taheer ya zauna kan kujera yana sauke numfashi..itama umma ta zauna kusa dashi snn tace”Ina tambayanka kayimin shiru Taheer..baa samu kifin bane ko Yaya?..”ya dago weak and tired eyes dinshi ya dorasu kan umma…murya a raunane yace Mata”Umma fushi takeyi dani..kawai sbd ta ganni da Sameera..Kuma taki tsayawa ta saurari bayanin da nakeso inyi Mata”…umma ta daure fuska snn tace”shine Kai Kuma ka sata a gaba kana Mata kuka ko mene..wai ace yarinya karama kmr Layla ta ringa juyaka Taheer..da girmanka da komai kanaso ka zama solo6iyon namiji wanda kejin tsoron matarshi koh”…tana rufe baki Taheer yace”umma ba haka bane wlh..ni banyi kuka a gabanta ba..Kuma umma ni ba tsoronta nakeji ba kawai ni damuwana kar wani abu ya samesu..kinsan condition din da take ciki baa son tana bacin rai haka..yanda take saurin nn Allah umma sai naji kmr akan zuciyata take tafiya”…baki umma ta tabe kafin tace”ai sai ka bata sarari duk ta gama iskancin nata ta sauko sai kayi mata bayanin tunda yanxu bata sonji”…Taheer na girgiza kai yace”wlh bazan iyaba umma..bazan iya barinta a wnn halin da take ciki ba..idan wani abu ya sameta ko unborn dina fa”…umma bata sake mgn ba Saida ta mike ta kama hanyar kitchen snn tace”ai sai kai tayi..haka kawai ka zauna yarinya karama tana maka iskanci iri iri kuma kana biye mata”..daga haka ta shiga kitchen abinta…shi Kuma Taheer mikewa yayi a hankali ya nufi dakin nata…a zaune ya sameta a gefen gado..tayi tagumi da duk hannayenta tana ta sharar kuka…ya karasa ciki da sauri tareda zaunawa kusa da ita…yasa hannunshi ya cire nata hannayen da tayi tagumi dasu…ya shiga girgiza mata kai murya a raunane yace”baby dn Allah..dn Annabi..kiyi hakuri ki tsaya kiji bayanin da zan miki”..Yana rufe baki Layla tace”ai dama kana sane ka shiga wajen..maybe dama Kun gama hada appointment dinku zaku hadu a wurin..shine ka tafi ka barni inata zaman jiranka a cikin mota”…ta karasa mgnr wasu sabbin hawaye na sake zubowa kan face dinta… Taheer ya kamo face dinta da duk hannayenshi…a hankali ya matsa da nashi fuskan ya hade da nata…yana kallon idanunta dake lumshe yace”yanxu baby zargin da kikemn knn..baki yadda dani ba dama”…a fusace ta bude idanunta tana zabga mai harara…ta daddage ta mike daga kusa dashi tana kokarin fita daga dakin ya dawo da ita jikin nashi da sauri…ta shiga dukan chest dinshi tana jujjuya Kanta tana cewa”ni ka sakeni..let go of me right now”…ai bata karasa mgnr ba Taheer ya hade bakinshi da nata…taci gaba da dukanshi tana kokarin kwace bakinta amma Taheer ya kamashi gam kmr magnet…a hankali yasa hannayenshi tareda rungumeta ga jikinshi sosae har yanajin tudun cikinta a jikin nashi…ya makaleta tsaf yanda ko motsin kirki ta kasayi..har yanxu kuma bai cire bakinshi a nata ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button