Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Mintina 20 ne suka kaisu clinic dinshi…da kanshi ya fito ya sake daukanta..ko su umman bai jira su fito ba yayi cikin asibitin da ita…staff dinshi sai kallonshi suke suna mamakin wnn rudewa da yayi..wasu Kuma basu mamaki as sun ringa sun wacece baby a wurinshi..sun Kuma San irin kaunar da yakeyi mata tun ba yanxu ba…Yana karasa shiga ciki wasu nurses suka shiga kokarin amsanta a hannunshi amma yaki bada ita…Kai tsaye ya nufi maternity da ita…sai da ya shiga har cikin labour room snn ya kwantar da ita kan bed shima ya zauna kusa da ita…ya dubi nurse din da ta shigo yanxu yace mata”is doctor Fatima around?..”da sauri nurse din tace”yanxun nn ta tafi sir..saidai doc Afiya itace zatayi night”…tana rufe baki yace”go go go..jeki karamin ita yanxun nn plss”…da sauri nurse din ta fita zuwa office na doc Afiya…bata jima da fitaba suka dawo cikin labour room din tare…su Kuma su ummi suna waiting area duk hankalinsu a tashe…doc Afiya na shiga cikin labour room din tace”yau Dr.Taheer da kanshi a labour room”…tana rufe baki yace”zo ki dubamin ita plss..yi mata VE muga ko haihuwan ne”…ba musu doc Afiya ta dauko hand glove dake cikin wani drawer tasa a hannayenta..tana gamawa ta matso inda Layla ke kwance tana murkususu don ciwon kara gaba yakeyi ba bayaba…Saida ta fara dage dogon rigan dake jikinta zuwa cikinta snn ta sunkuya zata zira hannun nata ciki…Taheer dake kallonta ya runtse idonshi da sauri.. bai son gani kwata kwata..dukda shi ba mace bane amma yasan yanda mata kejin zafin VE din n da akeyi musu..Yana ganin yanda suke yatsina wasu har ihu ma sukeyi idan zaayi musu…so sai ya lumshe idonshi don baison gani..ba don dole ba da babu Wanda ya isa yasa mishi hannu a gaban matarshi wlh…dukda doc Afiya mace ce ba karamin kishinta yaji ba…yasan idan yace zaiyi da kanshi ma ba iyawa zaiyi ba…gaba daya yayi loosing nutsuwarshi and ba patient din da zai iya dubawa right now bare kuma ace baby da kanta…bai bude idanun nashi ba sai da yaji doc Afiya na fadin”she’s 2 CM doctor”…a rikice Taheer ya bude idanun nashi tareda zuba Mata su…2 CM fa ko labour ma bai kankama ba… innalillahi yanxu a 2 CM take Shan wnn wahalan…gashi yasan cervix dinta dole zaiyi taking time before fully dialation tunda she’s primip…Ya Ilahi ya zanyi..kodai inducing dinta zasuyi ne…sai Kuma ya Kau da tunanin da sauri…sai zufa ke keto mishi sai kace shine ke labour din…doc Afiya ta shiga kwantar mai da hankali tareda alkawarin she will help..zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin Layla ta sauka lfy…dukda haka shidai gashi nn ne kawai..bashida burin da ya wuce a haihu da wuri don baiso ta galabaita…yace ma doc Afiya ta kula mai da ita zaije yama su ummi bayani ya dawo…

Yana fitowa su ummi da sukai cirko cirko a waiting area ko zama sun kasayi suka nufoshi da sauri…nan yayi musu bayanin komai tareda fadin haihuwan nata zai Dan sauki lokaci amma ba wani matsala bane InshaAllah…yace zai kaisu office dinshi su zauna Amma Sam sukaki yadda..dole haka ya sake komawa cikin labour room din ya barsu a wurin…yana komawa ciki ya samu har yanxu tanata fama…ya rike hannunta gam cikin nashi hawaye na wanke mishi fuska yake fadin”baby am sorry kinji..am right here with you InshaAllah ba abinda zai sameki..zaki haihu lfy Bi’iznillah”…Layla da zufa ke zubo mata da kyar ta iya bude baki tace”daddy..dadddy zan mutu..mutuwa zanyi daddy…the pain is unbearable..I can’t bear this pain daddy mutuwa zanyi”…da sauri Taheer ya toshe mata baki yana girgiza kanshi yace”InshaAllah bazaki mutu ba baby..I don’t want to loose anyone of you..I want to live with both of you so ki dena cewa zaki mutu InshaAllah ba inda zakije ki barni..I love so much..bazan iya rayuwa babu ke ba”…da kyar ta sake”nima I love you sosae daddy…I love like crazy but dd”…tun kafin ta karasa Taheer ya sake rufe Mata bakin…ya goge hawayen dake zubo mishi yana cewa” na fada maki ba inda zakije ki barni..stop saying Zaki mutu indai ba so kike ni in rigaki mutuwa ba..am right here with you and I know we can make it together..I love the both of you”..daga nn Layla bata sake cewa komai ba..sai nishi da taketa faman yi tana hada gumi…doc Afiya kuma nata kokarin assisting dinta..tana bata duk wani taimako daya kamaceta.

Wata ta kirani jiya saying ta tura min kudi Kuma banyi adding dinta a Dr.Taheer group na WhatsApp ba…for your kind information littafin Dr.Taheer is free sbd shine very first novel dana fara rubutawa..ban taba saidama kowa shi ba and ban ce wani ya Saida min dashi ba.. duk wanda yace ka tura mashi kudi yayi adding naka to group gsky 419 zai maka..sbd haka baiwar Allah kije ki nemo duk inda Wanda kika turama kudi take ta biyaki kudinki wlh..Ummu Ashraf bata taba karban kudin kowa ba sbd littafin is free…so sweethearts ku kiyaye plss☺️I love you all❤️????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

52

A takaice dai Saida Layla ta kwashi tsawon awanni tana labour amma haihuwa yaqi zuwa…zuwa yanxu karfinta ya gama karewa kaff don tun tana samu tana pushing har ta kasa yi Kuma…Taheer da har yanxu ke tareda ita duk yayi zuru zuru shima sai kace shi yake nakudan…doc Afiya har yanxu na tareda ita…su ummi ma suna waje tun suna sa rai zaa fito ace musu ta haihu har suka fara tunanin Allah yasa lfy…Saida Taheer ya fito da kyar ya samu ya lallabasu ya kaisu office dinshi don dare yayi sosae…har zuwa yanxu Kuma ko Nafeesa basu Kira sun fada Mata ba…ummi tace gara idan an sauka lfy sai a Kira duk Wanda ya kamata…shi Kuma Taheer bayan ya gama dasu ya sake komawa labour room…aikam kmr jira ake ya shigo ciwo ya sake dawowa gadan gadan…ya kama hannunta ya rikeshi cikin nashi…doc Afiya Kuma ta shiga kokarin taimaka mata…a takaice dai sai asuba snn suka samu Kai ya fito..shima Saida doc Afiya ta Mata episiotomy(‘Kari)snn aka samu ya fito…Layla ta saki wani wawan ajiyan zuciya don relieve sosae taji ta samu just by fitowan kan…doc Afiya ta taimaka tareda karasa ciro babyn…Saida ta yanke cord snn ta nade babyn a zani ta mikawa nurse dake tareda su…tayi withdrawing oxytocin tayi mata snn ta fara yi dinke mata wurin data Kara din..sai yanxu Layla ta samu bakin kuka..ta ringa kwalla musu ihu kmr ba itane take cewa zata mutu ba jiya..shiko Taheer idanunshi na rufe ruf don ba son ganin dinkin yakeba..yana kuma rikeda hanunta har yanxu..har aka gama dinkin nn Layla bata dena kuka tana kurma masu uban ihu ba…daga nn Saida ta tabbata ta fitar Mata da jinim da yayi saura a jikinta snn tayi Mata parking tareda hada mata ruwa ta shiga wanka…ita Kuma ta shiga gyara wurin…Taheer kam tunda yaga an fito da baby lfy ya lumshe ido yana maimaita”Alhamdulillah”cikin zuciyarshi…yana rikeda Layla dukda yanda yakejin zuciyarshi na fisgarshi kan yaje yaga babynshi amma baije inda takeba Saida ta shiga wanka…ya karasa inda nurse din dake rikeda babyn nashi take…ya Mika hannunshi kawai tareda amsan babyn da har an gama shiryawa an Sanya mai Kaya…ya lumshe ido tareda hugging babyn a kirjinshi…cikin ranshi yanayin duk addu’a dayazo bakinshi…yanajin yanda son babyn ke ratsa ko wace kafa ta jikinshi…wato haka iyaye keji a kan ‘ya’yansu…ya dago face din babyn yayi addu’a tareda tofa mai snn ya dubi nurse daketa kallonshi tana smiling yace Mata”me aka Haifa”…tana fara’a tace dashi”it’s a girl”…Taheer ya sake lumshe ido yana Kara godia ga Allah daya cika mashi burinshi…ya bashi ‘ya macen da yake matukar so…a hankali ya sake maida idonshi kan babyn sai ya kasa gane dawa take kama…tanadai da haske sosae Wanda ko baa fada mai ba yasan wnn hasken Layla ne tunda tafishi fari nesa ba kusa ba…a hankali yayi kissing goshinta murya can kasa yace”I love you”…
Inshort dai Saida Taheer ya bata lokaci sosae yana kallon babaynshi yana Kuma surutu shi kadai snn ya tuna dasu ummi…ya mikama nurse babyn da sauri snn ya fita zuwa office dinshi…su ummi na ganin ya shigo suka shiga tambaya ko ta haihu…Saida ya sakar musu kayataccen murmushi kafin yace”ta sauka lfy Ummus..an samu baby girl”…lokaci daya suka shiga fadin”Alhamdulillah”a tare kowacce face dinta daukeda tsantsar murna..shi sai ya kasa gane ma Wanda yafi wani murna a cikinsu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button