Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Da dare Taheer ya maida Awwal airport ya tafi bayan ya cika Layla da baby da Kaya kala kala..banda uban kudi daya basu…a Daren Kuma Taheer keta kokarin yaga sun kebe da Layla don yaji ra’ayinta akan sunan daya sama baby Amma ko keyarta bai ganiba…ganin ba ganin nata zaiyi ba sai ya hakura tareda komawa part dinshi ya kiranta a waya…tana zaune tana feeding Nawal Kiran nashi ya shigo…Saida ta kalli Su ummi dake gefe suna duba uban kayan da Awwal da Nafee suka kawo ma baby da Layla..Kaya ne masu yawan gaske…Saida taga hankalinsu bai kanta snn tayi picking Kiran…a hankali Taheer dake kwance kan gadonshi yace”babyna”…Layla ta lumshe idanu ta bude itama a hankali tace mishi”yes daddyna”…Taheer ya saki dariya before yace”baby ya kikaji sunan dana sama babynmu..sorry banyi shawara dakeba..I hope you like it”…yana rufe baki Layla tace”of course I like it daddy..sunane mai daraja da Kuma Ma’ana…sunan Amaryar fiyayyen halitta Muhammad SWA…itace mafi soyuwa a cikin matan Manzon Allah SWA…ita kadaice matar da ya aura a matsayin budurwa..itace akema lakabi da ummul mu’uminoom…itace ubangiji ya saukar da wasu ayoyi akanta don ya wanketa daga zargin da ake Mata..itace aka tambayi manzo SAW duk duniya wa yafi so..a Mata yace Aisha..a maza Kuma yace Mahaifinta wato Sayyadina Abubakar RA…daddy duk duniya nasan babu sunan daya dace da babynmu idan ba Aisha ba…snn sunan Umma ne..Wanda ba don umma ba da bazan taba auranka ba daddy…Ina alfahari da kasancewarka mijina Kuma uban ‘yata..inason sunan da kasa Mata har cikin zuciyata..infact ko Maryam da yake sunana banjin ina sonshi kmr yanda nakeson Aisha..Allah ya raya mana Aysha Nawal”…tunda ta fara mgn Taheer ya lumshe ido yanajin wani farin ciki na sake mamaye shi…Saida ta gama mgn snn yace mata”Thank you..thank you so much my baby…I love you..Allah ya maki Albarka kinji”…a hankali tace”Ameen”…shi Kuma yaci gaba da fadin”baby am missing you so much..tun dazu nakeson ganinki amma ban ganki ba..where is my sweetheart”…Layla da har yanxu ke smiling ta kalli Nawal dake bacci kan cinyanta tace mishi”she’s sleeping”…yace”ke yaushe zakiyi baccin”…a hankali ta sake cewa”Nima yanxu xan kwanta”…ya rausayar da kai kmr tana ganinshi snn yace mata”shi knn baby Saida safe..kiyi bacci mai dadi kinji…ki shafa min kan sweetheart snn kice mata Papa yana sonta sosae sosae…am missing you two like crazy”…kmr zai fashe da kuka ya karasa mgnr…Layla Kuma dake ta aikin dariya tace”to Saida safe daddy..we are missing you too”…daga haka sukayi sallama…ita kanta Layla sai taji duk ba dadi don ba karamin missing dinshi takeyi ba…tayi nisa cikin tunani kawai sai ji tayi Nafee ta dauke Nawal daga kan cinyanta tana cewa”so kike ki yar da itane Layla..wane irin iskanci ne wnn”…da sauri hankalinta ya dawo jikinta sai taga Nafee ta kwantar da ita…Ashe tayi nisa cikin tunani har Nawal din ta kusa faduwa kasa bata sani ba…

Washegari saiga Hanna tazo barka…da yarinyarta Hanan tayi girma sosae…baya ta gaisa dasu ummi a parlor ummin tace ta shiga daki Laylan ma ciki…haka kuwa ta nufi dakinda ummin ta nuna Mata…Layla na zaune suna waya da Taheer sai ga Hanna ta shigo…tayi mishi sallama snn ta mike da sauri tareda hugging din Hanna…itama hugging nata back tayi tana dariya…Saida suka gama cacime cacimensu snn suka karasa gefen gado suka zauna…Hanna na kallon Layla tace”oh wai Jakada kece kika haihu…ikon Allah knn kinganmu yanxu duk mun xama mamas”…Layla na dariya tace”bakida kirki wlh…ni sauko min Hanan din in ganta”…ba musu Hanna ta sauko Hanan dake gobe bayanta…Layla ta dauketa tana dariya tace”Tubarakallah Hanan din badai girma ba Hanna”…Hanna tace”umh wlh shegen girma gareta..ga fitina”…sai ta matsa inda Nawal ke kwance tana bacci…tana kallonta yace”wow mashaAllah…gata nn mai kamada babanta futuk..Allah ya raya mana”…a hankali Layla tace”Ameen”…ita kuma komawa tayi ta zauna snn tace”tafiya mukayi fa shiyasa kikaga shiru ban zoba…Muna Kano sai jiya muka dawo”…Layla tace”ba komai wlh..ai nasan dama kinada reason”…Hanna na gyada Kai tace”to ya sunan babyn tamu..ko baa da suna ba”…Layla tace”an sa Mata sunan Umma…Aisha amma zaana kiranta Nawal”…Hanna na zare idanu tace”Kai jama’a kin ga mun zama iyayen Aishoshi dagani har ke.. MashaAllah to Allah ya raya mana baby Nawal”..Layla ta amsa Mata da Ameen…ranar dai yini sukai suna hira da Hanna…har hiran makaranta Saida sukayi…Layla tace itama so take bayan suna ta lallaba ummi ta barta ta koma makaranta…Hanna bata bar gidan ba sai dare Habibinta yazo ya dauketa…tayi ma su ummi sallama tareda alkawarin zata dawo ranar suna..

Naga sunayen wanda sukeso suzo Mana suna????????karku damu kowa ya shirya nan da kwana biyu zamuzo mu saukeku har gida muje musha suna a Abuja snn mu dawo????????

Wnn page din sadaukarwa ne ga duk wata mai suna Aisha…Allah ya Kara Mana kaunar sunanmu????????????Allah Kuma ya raya mana Aysha Nawal ‘yar gidan baby da daddy????????????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

54

Ana gobe suna su Al’ameen suka iso Abuja…murna a wurinsu baa mgn da sukaga baby..har rigima akeyi wnn yana shi zai dauka wnn Yana shi zai dauka…a ranar Kuma da yawa daga cikin family dinsu na kano sun iso…mutanen Dutse ma mota kusan biyar sukayi suka taho suna…Ta ko Ina Yan iwa da abokan arziki sai zuwa sukeyi..

Shirye shirye sukeyi sosae sai kace taron biki ne ba na suna ba…umma ce ta dauki nauyin komai na suna hatta hall da zaayi taron a ciki ita ta kama..babu yanda ummi dashi kanshi Taheer din basuyi da ita kan ta bari ba amma Sam tace wnn taron nata ne tunda ita akayima takwara…har mawaki ta gayyato all the way from Kano..ga kuma cards da aketa bi ana rabawa mutane sai kace biki…

Washegari…

Tun safe dama aka yanka raguna kmr yanda al’ada ta tanadar…duk inda ka kalla a gidan zakaga cike yake da jama’a…tun safen Kuma masu kidan kwarya sukazo suketa faman kidi suna wakokinsu..sai wake Aysha Nawal suke mutane nata musu liki…umma Kam har rawa Saida ta taka itada Ramla..su ummi ma sun fito sunata likin kudi…mai jego kuwa tana ciki itada babyn da sauran mates dinta…taci kwalliya har ta gaji da haduwa itada baby Nawal.

Karfe biyu daidai make up artist ta iso gidan don yima mai jego kwalliya…a part din mahaifin Taheer aka sauketa don nan ne ba jama’a..basu bata lokaci na Kuma suna fara..suna tareda Hanna dake gidan itama tun safe…

Acan cikin gidan kuwa su ummi ankon lace sukayi Sea green..gaba daya sunyi dinkin bou bou iri daya…Ummi..Umma..Ramla..Nafee da Kuma Hibba..sunyi kyau MashaAllah har baa mgn…bayan sallahn asr aka fara diban mutane ana kaiwa hall din da zaayi sunan…Su ummi sune kusan na karshe a tafiya..

5:30 daidai aka gama ma Layla make up dinta…tana sanye cikin Lace dinta Blue Black..mayafi da Kuma head dinta suma blue black…sai diamond necklace dinta silver..purse da takalminta ma duk silver ne…Ni kaina dana kalleta sai dana furta Tubarakallah MashaAllah sbd tsabar kyan da tayi…Aysha Nawal kuwa tana sanye cikin dan gown dinta blue black da fari…ansa mata dan band dinta mai kyau a Kai shima white..sai showel da aka nadeta ciki shima white…kallo daya zakayi musu kaji sun shiga ranka matuka sbd tsabar haduwan da sukayi…Saida aka gama ma Hanna light make up dinta snn suka fito don tafiya wurin taron…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button