Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Angon karni kuwa tun safe ya wuce gidan Yusuf…Yusuf din nata tsokanarshi wai baban baby da baby amma kobi ta kanshi baiyi ba…sai karfe hudu snn shima ya shirya cikin Shadda sky blue snn suka nufi hall din shida Yusuf da some of friends dinshi…Allah ya sani da anbi ta nashi ba wani party da zaayi organising..shi ba son wnn harkan yakeba kwata kwata..don dai babu yanda zaiyi da Umma ne shiyasa zaije amma shi baa son ranshi zaa sa matarshi taci uban kwalliya ta shiga cikin Arrijaalu kowa ya kalle mai itaba…

Isowansu wurin yayi daidai da isowan su Layla ma…tunda ya dora idanunshi a kansu yaji tamkar ya Dora hannu bisa kai yace wayyo Allah sbd tsabar kyawun da yaga sunyi..they look absolutely breathtaking…wani irin so da kaunar su na sake mamaye ilahirin jinin jikinshi…kawai sai ya lumshe ido tareda jingina jikin mota yana dafe saitin heart dinshi da hannu…shi kadai yasan abinda yakeji cikin zuciyarshi…shi har yanxu bai yadda da ake cewa wai idan anyi aure soyayya na raguwa ba..coz kullum son baby karuwa yake cikin zuciyarshi bai tabajin ya ragu ba..ga kuma little Umma da yakejin sonta itama har cikin jininshi…yana sonta fiyeda komai…Yusuf ne ya jashi suka karasa inda suke…umma ta fito daga cikin hall din ta amsa Nawal dake hanun Layla snn suka jera tareda few mutanen da aka jera zasu shiga dasu ciki..

DJ najin zasu shigo ya sakar musu waqar Gimbiya Aisha ta Ali Jita…wai ya sadaukar da ita ga hajia Aisha uwar taro..da Kuma takawararta Aisha Nawal..

????????Gimbiya Aisha…Sarauniya ce Aisha…Aisha kixo ki dauki kidan girma…Aisha kinada babbar alfarma…Indo Indo da Aisha…gata abokin mu Aisha… Sarauniya ce Aisha…gamai kwalliya Ina Aisha…ga mace ta gari taho Aisha…yi sarauta Aisha…ke kwanta cikin kilishi huta…Aisha zauna a miki fifita…Aisha zana so ganin angon ta… Sarauniya ce Gimbiya… kyakykyawa ku tambaya…mai hakuri ce farar diya…mai nutsuwace ‘yar hajiya…an kirata zinariya…Aisha Aisha…Aisha Aisha…Aisha dole ne na danyi miki take…masu sarewa kui tayi gobeda safe…ai hakuri baa fita ba… kwalliya baa fita ba…ilimi baa fita ba…nutsuwa baa fitaba…Yar babban gidace Aisha…Yar manyan mutane Aisha????????????????(Bari in bar ku haka kar kuce na cika son kai????)

Tunda suka shigo wurin sai kallo ya koma kansu…sunyi kyaune na bugawa a jarida…duk Wanda ya kallesu sai yace mashaAllah…bayan sun karasa sun zauna akayi opening prayer tareda yima Aysha Nawal addu’an Allah yayi Mata albarka..sai Kuma taro ya cigaba kafin karasowar babban mawaki Ado Isa Gwanja…(kunsan tsakaninmu da gwanja akwai Amana????)

Su Ramla sai raba suveniers suke…kowanne na daukeda picture din babyn an rubuta welcome to the world Aisha Taheer Jakada(Nawal)…kusan duk mutanen dake wurin ba Wanda bai samu ba…
Anci ansha an kumayi rawa sosae snn anyi barin kudi kmr baa san ciwonsu ba…Layla dai lallaba jikinta take don ko rawan ma kasawa tayi…dukda dinkin jikinta ya warke amma gani take motsi kadan zai iya warwareshi…shiko Taheer dama haka yakeso..bai son tace zatayi rawa at all…and he’s happy yau da mayafi a jikinta unlike lokacin bikinsu da ko mayafin babu…dukda hakan kuma tayi mishi kyau sosae kmr ya rungumeta yakeji…baby Nawal kuwa duk wnn hidiman da ake tana hanun Namesake dinta wato umma..suk Wanda zai ganta saidai ya ganta a hanunta..dukda hidiman dake gabanta bata yadda ta bama kowa itaba wai don kar a jagwalgwalata????

Bayan anyi sallahn magrib an dawo mawaki Ado Gwanja na Mata ya iso cikin hall din…Saida yaranshi suka gama kafa kayan kidinsu snn suka fara kida..shi Kuma ya sakar mana wakarshi mai taken Mamar Mamar…lokaci daya nida jama’ata da mukazo suna tare muka shiga filin rawa????

????????????Ayye lube…Ahayye lube gumbar Dutse…naga gidanka ya cike ya batse…dan wnn kidan na mai kayane duk wcce babu sai ta koma gefe..Mamar Mamar…ai wnn kidan kidan Mata ne..Mamar Mamar…Naga Kuna rawa Kuna wani juyi..Mamar Mamar…wnn kidan kidan matane..maar Mamar…Dan kuji wnn kidan kidan matane..Mamar Mamar…Naga Mata kunyi dumur dumur Kuna wani jumping..Mamar mamar…sai na biyoku baya zam mini baitin..Mamar Mamar…sai ku tayani inji dadin sautin..Mamar Mamar…Mata a kiraku ran gida daidai ne..Mamar Mamar…dn matar wane tafi matar wane..Mamar Mamar…Mata kune na bara kune na bana..Kuma kune na shekarar basasa..Mamar Mamar…ai kowa ya ganku ya San kune..Mamar Mamar…saidai tambayar rashin albarka????????????

Ado gwanja na fara wakar nn Mata suka fara tashi..masu rawa nayi masu yi mishi liki ma nayi…Ni kaina da naji waqar nn Saida nadan taka rawana snn naci gaba da dauko muku bayani…shima bai gama performance din nashi ba sai after ishaa…daga nn Kuma mutane suka fara raguwa a hankali a hankali…su ummi Kam basu bar wurin nn ba sai around 9..lokacin kowa ya watse..Kuma taro yayi tsari yayi kyau saidai ace Alhamdulillah..Allah ya raya Aysha Nawal…

Layla kuwa dama tun dazu Taheer da kanshi ya dauketa suka tafi..bayan sun karbi Nawal da har yanxu ke hannun umma..

Yarinya tayi goshi sosae don sun samu Kaya fiyeda ma yanda sukayi tunani…ba na Nawal dinba…ba Kuma na Layla ba…Ummi kanta saida tayi musu Kaya masu yawa Banda nasu Nafee ga Kuma umma da akaima takwara…ga sauran family da friends dinsu suma sunyi kokari sosae…ga Kuma uban Wanda Taheer yayi musu kmr Wanda ke hada lefe..Layla har mamakin inda zasu Kai wnn uban kayan takeyi…sai takega kmr sunyi musu yawa..
Wanna kenan

Bayan kwana biyu da suna Taheer ya shigo gidan da dare…tun jiya yake son a bari yaga matarshi Amma ummi ta Hana…daya tambayi Layla zatasa a kawo mishi Nawal shi Kuma ba ita kadai yakeson ganiba…he wants to see his wife too…direct ya wuce dakin ummi don baiga kowa a parlor ba…su Al’ameen da zasu koma gobe suna zaune Kan gado shida Ramadhan…sunsa Nawal dake bacci a tsakiya sai musu suke wnn yace tana kamada Layla wnn yace no da Taheer take kama…ita Kuma Layla na zaune gefe tana kallonsu…Taheer ya rungume hannayenshi a kirji Yana kallonsu with a smile kan face dinshi yace”Hey musun me kukeyi haka”…da sauri Al’ameen yace”daddy dn Allah Nawal ba dakai take kamaba”…shima Ramadhan yace”daddy ai da Ya Layla take kama koh”…Taheer yasa dariya kafin ya sunkuyo tareda daukan yarinyar dake kwance…ya Kura mata ido shima kmr yanason gano dawa take kaman snn yace”yeah duk kunada gsky…eyes dinta da nose dinta da Kuma lips dinta duk irin nawa ne…skin dinta Kuma irin na mamanta ne”… Al’ameen ya mike yana dariya yace”dama na fada maka yaro..da daddy take kama”…shima Ramadhan ya mike yace shi bada daddy take kama ba..a haka suka fice daga dakin…Taheer ya rakasu da ido kafin ya dawo da dubanshi kan Layla da itama ke binshi da kallo…ya saki murmushi tareda karasawa ya zauna kusada ita..a hankali ta matsa jikinshi sosae tareda rungume hannunshi a chest dinta..ta dora kanta akan shoulder dinshi suna kallon Nawal dake baccinta peacefully…a hankali shika Taheer din ya kwanto da kanshi kan nata..muryanshi can kasa yace”my cute babies”…Layla ta dan turo baki tace”ai na fada maka bazaka na kiranta baby ba wlh..itama Kuma bazata na ce maka daddy ba”…Taheer na dariya yace”ki kwantar da hankalinki dama ba sunanku daya ba..ita kinsan mene sunanta?..”banza tayi dashi tana cigaba da turo baki..Saida yayi kissing goshin Nawal din snn yace”sweetheart..she is my sweetheart..my blood and she is my mom”..da sauri Layla ta matsa daga jikinshi tareda juyawa mishi baya…shi Kuma ya ajiye Nawal a gefe snn ya dagata cak ya dora akan laps dinshi…tana hararanshi tace”idan ummi ta shigo nidai ba ruwana”..yaja kumatunta Yana kokarin yin mgn aka bude kofar dakin…a razane suka daga kawunansu suna kallon kofan…umma ce tsaye..ta kama kugu tana kallonsu da mamaki sosae a fuskarta…da sauri Layla ta mike daga jikinshi tana marairaicewa tace”Allah umma bani na kirashi ba..kuma ni bance ya dorani a cinyanshi ba Allah”…umma batabi takan abun da Laylan ke fada ba..tana duban Taheer tace mishi”tashi ka fita”..ba musu ya mike inda yake Yana sosa Kai..shi sai yaji sauki daba ummi ce ta shigo ba..yasan da yanxu tana nn ta inda take bata nn take fita ba…maimakon ya fitan saiya tsaya kusada umman yace”umma shigowana knn wlh..ki tambayeta k”bai karasa mgnr ba umma ta sake cewa”nace ka fita kabar dakin nn Taheer..idan Kuma so kake Yaya ta shigo ta sameka Bismillahi”..bai sake mgn ba ya kama hanya kmr zai fita daga dakin sai Kuma ya dawo da sauri zuwa inda Nawal ke kwance tayi kissing goshinta yace”I love you sweetheart”…yayima Layla ma kiss din yace”I love you baby”..sai ya karasa inda umma take itama yayi kissing forehead dinta snn yace”I love you umma”…daga haka ya fice daga dakin…umma ta bishi da kallo tana girgiza Kai..wato ko kunyarta baiji yake wnn iskancin hadda wani kissing dinta..ko dayake batayi mamaki ba..indai Taheer ne akan Layla ba abinda bazai iyayi ba..ga Kuma ‘yarshi itama da ba kunyan me dashi a kanta ba…haka ta juya ta bar dakin tana murmusawa ita kadai…alamrin Dan nata dariya yake bata wlh..”Allah ya shirya mana”
A gurguje plss..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button