NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

“Me too.” Ta fad’a tana raba hannunshi da nata, rufe motar akayi inda yace mata “Mu shiga ciki ko.”

D’an karkace tayi tace “Sorry, i’m going to late but Abhi she’s inside, go to meet him.”

Gtara tsayuwa yayi yace “Amma na d’auka ke na zo gani dan iyayenmu na son had’amu aure.”

Wani sororo ta kalleshi tace “Whit u? In this level? I have no idea.”

Murmushi yayi yace “To yanzu kin sani, mu shiga ciki.”

Rumgume hannaye tayi tace “Sorry, amma gaskiya baka cikin irin mazan da nake so, sorry.”

Zata koma ciki ya daka mata tsawa da cewa “Ke.”

Cak ta tsaya tana kallonshi yanda ya nuna mata tsaya, d’orawa yayi da “Wacece ke fa har zaki kalleni ki ce bana cikin irin mazan da kike so? Ke d’in kin d’auka wata sarauniyar kyau ce? Me ke gareki? Dubeki da kyau ki gani mana mummuna da ke, mtsss.”

Tsaki yayi tare da bud’e motar ya shiga ranshi a b’ace, ita ma juyawa tayi ranta b’ace kamar zatayi kuka, Abhi na gani ta gilashin k’ofar, zuciyarshi ta karaya daya ga ya nunata da yatsa, ya d’aga murya kanta wanda bai tab’a yi ba shi, ko da ta shigo a hassale ta d’auki jakarta ta fita ko kula shi ba tayi ba.

Wayarshi dake hannunshi ya shiga tura dogon sak’o wa wanda zai cika mishi aiki, dole ya ladabtar dashi ya gane ba’a ma Sarah haka, kuma ko waye yayi zai shiga taitaiyinshi. Ba zai ji wuyar d’aukarwa Salah shatar jirgin da zai kaishi har Abidjan dan ya tsoratar da yaron ba.

Da yamma ya isa wurin a birgin daya tanadar masa kawai dan yaje ya kirta rashin mutumci ya dawo, da sauri secr茅taire d’in tace “Pardon monsieur, tu ne peut pas entr茅 sans permission (Ba zaka iya shiga ba babu izini.”

Tsaye yayi a hankali ya kalleta, saida gabanta ya fad’i ganin fuskarshi, tsoratarwarta tayi yawa, idonshi kamar na damisa gasu da matuk’ar sakin charme (sharme), a hankali cikin nutsuwa da bawa kowace kalma hakk’inta ya bud’a bakinshi mai d’auke da kakkauran labb’a yace “J’ai une rendez vous avec Malik, 01:30.”

Da sauri ta shiga danna ordinateur (laptop) d’in dake gabanta dan ganin yaushe haka ta faru? Abun mamaki da ita dai bata san dashi ba shine wani sabon rendez vous (appointemen) ta gani a daidai lokacin daya fad’a, kallonshi tayi tace ” Ubaid Umar?”

A hankali ya lumshe ido alamar eh, agogon dake fuskantarta ta kalla ta ga minti d’aya ne babu a lokacin shigarshi, nuna mishi k’ofar tayi tace “Tu peux.”

Bai ko kalleta ba ya wuce, yana bud’a k’ofar ya shiga ya mayar ya rufe, wanda ya samu zaune a gaban makeken tebur d’in yayi sauri k’ura masa ido, bai san shi ba ko kad’an, hasalima bai tab’a ganinshi ba sai yau, da mamaki yace “Waye kai? Waya baka izinin shigowa?”

Mutumin dake cikin bak’ak’en kaya costume (cot) da kuma wata babbar riga ta sanyi bak’a a saman kayan, k’ala baice ba har ya zagaya ta kukeran da mutumin ke zaune, shirin mik’ewa yayi tsaye yana fad’in “Malam wai waye kai? Me kak…”

Maganarsa ce ta tsaya sakamakon had’a kanshi da mutumin yayi da tuburin gabanshi ya danne, kafin yayi wani k’ok’ari ya fito da mouchoirs (hankceip) a aljihunshi ta tusa mishi a baki, hannunshi ya kama ta baya ya murd’e sosai tare da kama yatsarshi manuniya, bai b’ata lokaci ba wajen karya yatsar.

Ihu yake daga kwance amma baya fita da kyau, sakinshi yayi ya ciro mouchoirs d’in ya jefar, har ya sakankance da mutumin ya rabu dashi ne sai yaji gwiwar hannunshi a bakinshi, ba shiri ya rufe baki jini na zuba a ciki, gabanshi ya dawo ya tsaya ya cire bak’in gilashinshi, saida ya fito da sigari a aljihun rigarshi tare da mak’yasta ya kunna, kallonshi yayi ido ciki ido.

Da sigarin hannunshi ya nuna shi yace “Wannan gargad’i da jan kunne, ba’a d’aga mata yatsa, ba’a d’aga murya sama da ta ta, kayi sa’a baka harare ta ba, da zuwa yanzu idonka ne a hannunka ba hak’ori ba.”

Ko da ya gama fad’a ya juya yana saka gilashinshi ya fice, tana ganinshi tace “Sai anjima yallab’ai.”

Ko kallonta baiyi ba sai ma k’ok’arin kiran wata lamba daya shiga yi. Ana d’auka daga b’angaren aka ce “Ya akayi?”

Cikin isa da k’asaita ya amsa da “An gama, gobe ba zai sake kallonta ba ma bare ya nuna ta da yatsa.”

Dariya akayi tare da cewa “Da kyau Salah, aikinka na kyau, ka duba counte d’inka zaka ga kud’inka.”

Ko da ya fita ya bud’a hannayenshi daya rufe baki dasu, jini da yawu har da haure biyu sun fita, da gudu ya shiga douche (ban d’aki) ya shiga wanke baki, kallon kanshi yayi ta madubi ya bud’a baki, kam bala’i kenan shine da wawulo haka, ko da ya fito yana rik’e da yatsanshi ya shiga tunanin abinfa ya fad’a masa, ya sani ita ce dan da ita kad’ai ya had’u da ita yau har ya nuna mata yatsa, takowa yayi da sauri ya d’auki wayarshi ya kira mahaifinshi.

Yana d’auka yace “Abba ka gani ko? Ka ga abinda ka ja min?”

Cikin nutsuwa Alhaji Kabeer ya amsa shi da “Lafiya Malik? Me ya faru?”

Cike da takaici yace “Abba yarinyar nan mana, saida na fad’a maka ni bata gaba na amma ka tilasta ni zuwa na had’u da ita, yanzu gashi har bureau (office) d’ina an shigo an ci zarafi na akan ta.”

Cikin kulawa yace “Subhanallahi Malik, waya ci zarafinka? Ya kuka yi daka je ka same ta?”

Shi haushi ma tambayar ta bashi, cikin b’acin rai sosai ya buga wayar a k’asa tayi d’aid’ai, huci ya shiga yi da tunanin uban waye ma ya zo ya masa wannan wulak’ancin?

Dama ya tashi ne dan amsa wayar da aka kira shi yanzu, ko da ya dawo kan babban tuburin cin abincin ya same ta har yanzu kumbura fuska take, murmushi ya saki yana komawa kukerarshi ya zauna yace “Kinfi kowa sanin bana son ganin fuskar shanun nan ko?”

Kallonshi tayi cike da sangarta da shagwab’a tace “Na daina to.”

Wani murmushi yayi yace “Na fad’a miki ko ganinki yayi yanzu saiya rufe idonshi bare yayi gigin fad’a miki maganar banza.”

Da dare ya je k’ungiyarsu ta matsafa kamar yanda suka saba, amma yau da aje sai shugabansu yace “Shakoor, jibi zaka gabatar mana da ‘yarka Sarah, Nga da sauran yan k’ungiya muna buk’atar jininta.”

Dammmm ya samu wani mummunan fad’uwar gaba, Sarah? Lokacin har ya zo? Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, abinda ya dinga maimaitawa kenan har saida yaji sun kwashi gaisuwa irin ta zasu koma gidajensu, da sauri ya dawo hayyacinshi yana kallon kowa a tsorace da mamaki, da k’yar shima ya b’ace ya bar wurin, ko da ya samu kanshi d’akin baccinshi saiya duk’ufa tunanin yanda akayi suka rabu da mahaifiyarta…

SADAUKARWARKI CE

Yagana surukata, Allah ya saka miki da alkairi馃グ

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:56 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button