NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯8锔忊儯

Kamar cikin mafarki taji Dr. na fad’in “Alhamdulillah, kai amma fa an auna arzik’i, kiga wani ikon Allah kisan da lallai Allah ne mai juya al’amura yanda ya so, kina ga duk jinin data zubar da wahalar da tasha cikin hukuncin ubangiji Allah ya bamu damar cetota da abinda ke cikinta, lallai Allah kaine Allah.”

Malamar asibitin ce tace “Gaskiya kam, dan abune dake wuyar samu gaskiya cikin dubbanin mutane.”

Kamar wacce tasha k’waya cikin magagi da zafin ciwo ta shiga juya kai tana fad’in “Dan Allah Dr. ka taimake ni, ku taimake ni karku fad’a musu ina da ciki, zasu kasheni ne su kashe abinda ke cikina, karku bari su sani dan Allah na rok’eku.”

Kallon juna sukayi a hankali malamar ta dafa kafad’arta tana kallon fuskarta tace “Madame, ba kya so su sani? Ba mijinki bane?”

Shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta bud’a ido ta kallesu tana hawaye tace “Mijina ne, amma bana so ya sani shima saboda matarsa bata da kirki, zata kasheni da abinda ke cikina idan tasan yana nan.”

Kallon juna suka sake yi sai kawai malamar tace “Ba komai karki damu, insha Allahu ba zamu fad’a masa ba kinji.”

Lumshe ido ta sake yi tana ta jujjuya kanta tana cije leb’e, saida suka samu ta d’an nutsu kamar tana son yin bacci amma su kansu suna mamakin yanda baccin ya k’i d’aukarta har yanzu suka samu suka keb’e, tattaunawa sukayi inda yake nuna mata anya kuwa ya dace su b’oyema mijinta, amma saita fahimtar da shi abinda ita ma ta fahimta, da haka ya gamsu harya sanar da Salahadeen cewa cikinta ya zube.

Kallonta yayi ganin kallon da take masa yasa shi cewa “Lafiya malama?”

Da sauri kamar wacce ya ganota ta girgiza kai alamar ba komai, sama da k’asa ya harareta yace “To kalli gabanki.”

Sai kuma ta samu kanta da d’auke idonta daga kanshi d’in cikin sanyin jiki, d’an gyara zamanta tayi ta jingina sosai ta rufe ido, k’afarta take d’an d’agawa amma ta kasa motsata. Yanda yale lura da kowane motsi nata ne yasa shi fahimtar komai a tsanake, kallonta kawai ya ci gaba da yi ba tare da wani d’auke kai ba.

Basu shafe wasu awanni ba saboda gudu sukayi sakamakon cewa da akayi suna tare da marar lafiya, suna sauka airport d’in k’asar Tha茂lande saukar jirginsu daidai da zuwan ambulance da matsiyacin gudu wanda aka sanar dasu lokacin saukar marar lafiyar, ba wai dan tana wata mai kud’i ko matsayi ba sai dan yar k’asar ce hakk’i ne kula da lafiyarta akansu, da gudu gudu suka fito aka turo gado aka nufi jirgin, da kansu suka shiga ciki suka d’aukota akan wani gadon mai kama da makara na k’arfe wanda tsakiyarshi kamar wata leda ce mai k’warin gaske, suna saukowa daga matakalar aka d’ora kan gadon mai k’afafu aka turata da sauri, cikin motar aka saka inda suka bawa Salahadeen damar shiga tare da ita suka figi motar ana jiniya.

A cikin motar aka fara mata gwajin k’wak’wafi musamman k’afarta data fi d’aukar hankalinsu kan kumburin data fara, wani pommade ya shafa mata a k’afar, kafin wani lokaci su isa asibitin kam har zugin k’afar ya d’an rage a yanda take jinshi a farko, suna zuwa aka shiga da ita ciki da sauri sai Salahadeen daya tsaya a k’ofar d’akin.

Ka rantse da Allah bata samu kulawar likitoci ba saboda yanda suka duk’ufa dubata, binciken k’wak’waf kamar na son gano yaushe zata mutu, a haka har suka gano cikin dake jikinta da kuma karayar dake k’afarta, sanda suka tambayeta garin yaya tayi sakaci haka alhalin tana da ciki? Suma rok’onsu tayi kan karsu bari a sani dan Allah, bata fad’a musu dalili ba sai dai tace zata sanar dasu a lokacin daya dace da kanta, basu damu da hakan ba su lafiyarta ce a gabansu yanzu, dan danan suka bata wasu k’wayoyin magani tasha aka ce za’a mata aiki a k’afar, Salahadeen dake tsaye yana ganin wani likita ya fito zai shiga d’akin da take yaji gabanshi ya fad’i, dan daga inda likitan ya fito ya tabbatar mishi da likitan k’ashi ne, hakan na nufin ta karye ko kuma k’ashinta ya tsage kenan? Kamar wanda aka tura d’akin kawai ya tura k’ofar ya shiga, duk juyowa sukayi suka zuba masa ido sai wata ma’aikaciyar dake fad’in “Malam ka jira a waje, ba’a shigowa nan.”

Bai ko kula da abinda take fad’a ba sai ma nufa wajen Sarah da zaune tana kallonshi da mamaki, suna kallon ikon Allah ya k’arasa kusa da ita ya kamo hannunta yana kallon idonta yace “Sannu ko.”

Wani likitan ne yace “Mr. ka jira mu a waje ko? Zamu kula da ita yanda ya dace.”

Kallonshi yayi kamar baisan me yace ba, karon farko sai yaji daga bakinta ma yake son jin sunan mr. d’in dan yafi dad’i, kallonta yayi yana sake k’amk’ame hannunta yace “Karki damu, ina nan tare dake, alk’awari na d’aukarwa Mama kan zan kula dake.”

D’auke idonta tayi daga kanshi ta kalli likotocin, likitan k’ashin ne ya kalli sauran yace “Shikenan kawai, zai iya zama anan ba wani abu.”

Matsawa yayi kusa da k’afar mai ciwo ya sunkuya yana kallonta, hoton k’afar da akayi ya d’auka yana sake nazartat komai a ilmance, kallon Sarah yayi ya mata murmushi saboda ya tabbatar yanzu k’wayoyin sun fara mata aikin da suke buk’ata. Salahadeen kuma wata muguwar harara ya kwad’a masa da jin haushinshi, dalilinshi kuwa bai wuce akan me zai kalli matarshi ya mata murmushi ba? Iskanci yake nufi da hakan ko kuma duk cikin salon kulawar ne?

Kama k’afar yayi ya d’an matsa wanfa hakan yasa ka Sarah sakin ihu a lokaci d’aya ta janye k’afar tare da matse hannun Salahadeen dake cikin nata, da sauri ya zauna gefenta ya danna kanta a k’irjinshi ya d’ora bakinshi saman kanta yana fad’in “Shiiiii, is ok, sorry princess, is ok uhmm.”

D’ago kanta tayi ta kalleshi, idonta har sun canza launi sunyi jawur, cije leb’enta na k’asa tayi da taji kamar zai mara rawa, sanda ta shagala da kallon fuskarshi ne likitan ya kalli ma’aikaciyar jinyar yace “Ba kun bata magani ba?”

Da girmamawa ta amsa mishi da “Eh an bata Dr.”

Hannu ya mik’a mata yace “Naga rahoton gwaje gwajenta, ina son ganin rukunin jininta.”

Da sauri ta ciro rahoton dake mak’ale a gadon ta mik’a mishi, dubawa ya shiga yi kafin ya kalleta yace “Kin tabbatar maganin nan kuka bata?”

Cike da tabbaci tace “Yes sir.”

Kallon Sarah yayi yana nazarin yanda zasu mata, ba zai yiwu su sake bata wani maganin ba ko allurar kashe zafi saboda tana da k’aramin ciki, hakan zai shafi lafiyar abinda ke cikinta ko kuma ita suyi drogu茅nta, kallon Salahadeen yayi da ido ya shiga mishi nuni daya rik’e musu ita sosai.

A hankali ya sake kwantar da kanta a k’irjinshi yana ta ci gaba da fad’in “Shiiiiii.”

Bata ankara ba taji an sake damk’o k’afarta, a hankali a hankali taji ana shafa ta ana d’an juyawa, duk in aka mitsitsika d’in nan saita k’ara matso Salahadeen a jikinta, an jima ana haka har ta sakankance ta fara sabawa da wannan rad’ad’in sai kawai taji wata azaba sanda ya juya k’afar da k’arfi har tayi k’ara, zunbur ya mik’e tsaye idonshi lik’e gam ya kasa kallo sai mimi yake da baki yana addua’r da duk ta zo bakinshi, k’ara danne kanta yayi a k’irjinshi da hannu d’aya kuma yana rik’e da bayanta yana shafawa, yana jin yanda take rizgar kuka rigarshi har ta jik’e da yanda take ta cumimiyo shi ta baya tana matsarshi kamar mai wankin kaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button