NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Yya juya zai fita da sauri zuwa station d’in da Richard ya fad’a masa kawai wani abun al’ajabi ya faru, wani jijjiga suka ji gaba d’aya gidan yayi kamar yar k’aramar girgizar k’asa, Salahadeen dake zaune d’aga kai yayi ya kalli sama, inda Richard da Malik sukayi saurin dafe duk abinda ke kusa dasu saboda tangal tangal d’in da sukayi zasu kifa, kai tsaye kuma komai ya tsaya cak kamar ba ayi ba, sanda suka shiga waige waigen abinda ke faruwa ne kuma suka lura da wani d’aki a saman wanda ke shi kad’ai a kusurwar, duk mamaki ne ya sake bayyana a fuskokinsu suna k’ara kallon d’akin, duk da dai basu ma gidan wani kallon tsanake ba, amma sun tabbatar babu wannan d’akin a d’azu sai yanzu. Malik ma daya san gidan duk da ba nan yake rayuwa ba yasan babu shi, cike da mamaki yana kallon d’akin yace “Kai! Yaushe kuma Abba yayi wannan d’akin? Sai naga kamar babu shi dana shigo ko?”

Ya fad’a yana kallon Richard da tambayar, shima da mamakin ya kalli Salahadeen dake ta kallon d’akin yana ta ci gaba da addu’a hannayenshi sama, mik’ewa yayi ya tunkari saman matakalar, Richard ne yace “Salahadeen ina zaka je? Ina ga fa akwai had’ari a wurin nan, ka bari na kira Insp ya dawo.”

Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace “Ba buk’ata ka barshi, Allah yana tare dani.”

Malik ma bayanshi yabi yana fad’in “Malam kai waye? Me zaka je yi ne a saman?”

Komai bai ce masa ba har ya haye samaya nufi kusurwar, Richard ma bayansu yabi dan duk tsoro ya kama shi, suna zuwa bakin k’ofar ya murd’a, amma sai yaji k’ofar gam a lik’e, sake murd’awa yayi tare da turawa amma babu alamar zata bud’e, k’arfi yasa sosai tare da turawa da iya k’arfi yana fad’in “Bismillah.”

Bud’ewa k’ofar tayi amma k’arfin guguwar data fito daga ciki ta saka su fad’uwa a wurin duk suna rufe da idonsu, koma menene ya fita sautinsa kad’ai zai tsorata ka saboda kamar k’arar sahara ce a tsakiyar dokar daji, hakan zaka ji tana fitar da wani sauti mai ban tsoro “Wuuuihhhhhui, wuuuuhhhhui!”

Bai daina ambaton sunan Allah ba har saida yaji komai yayi shiru, mik’ewa sukayi tsaye suna kakkab’e jikinsu saboda sosai sukayi k’ura, kallon k’ofar d’akin sukayi wanda daga nan basa iya ganin komai dake ciki, lumshe ido yayi tare da sauke ajiyar zuciya a ranshi ya raya tabbas zai shiga komai zai faru ya faru, bud’a ido yayi ya sake k’udurta wata addu’a a abakinshi sannan ya d’aga k’afar dama ya shigar da ita. Dauuuuu! Wani haske mai d’aukar ido ya gifta ta gabanshi tare da gauraye d’akin gaba d’aya, ba komai a d’akin banda wannan jan k’yale da kokon kai da kuma kwarya sai Sarah a gefe d’aure, da wani irin gudu ya k’arasa gabanta ya zube yana rumgumeta jikinshi da fad’in sunan “Mom Waleed, Sarah, weke-up.”

Jin bata motsa ba yasa shi rik’e igiyar da aka d’aureta da ita, kallon igiyar yayi har zuwa can saman yar tagar dake d’akin wacce ba’a ganinta sosai, tallabo fuskarta yayi ashe idonta a bud’e suke tsabar galabaita ce kawai da wahala, jinin daya bushe a hancinta zuwa bakinta yabi da kallo, bakinta ya bushe sosai sai k’ok’arin tattaro yawu take, shafa fuskarta yayi kamar zai fashe da kuka ya sake rumgumeta sosai a jikinshi yace “Sarah ba kya jin magana, dubi yanda suka miki da gatanki da komai.”

Cikin sa’a ta samu kunnenshi a daidai saitin bakinta ta furta mishi “Ru..wa, ru…wa m..r.”

Da sauri ya juya ya kalli Richard dake tsaye yace “Bani ruwa Richard.”

Da gudu ya fita dan kawo masa ruwan, sake k’amk’ameta yake a jikinshi cikin kunne yake rad’a mata “Ban so haka ta faru ba Sarah, nayi iya k’ok’arina wajen ganin basu samu damar cutar dake ba, kiyi hak’uri kinji ki yafe min, na gaza wajen zama miki garkuwa, ki gafarce ni.”

D’an gaba yake da ita yana baya suna d’an lilawa, a haka Richard ya shigo ya bashi ruwan, da kanshi ya bud’e ya kafa mata a baki, da niyyar zuba mata kad’an kad’an ya tafi, amma sai tayi wuf ta rik’e bakin robar da bakinta ta shiga kwankwad’ar ruwan har wasu na fitowa tana neman k’warewa amma bata tsaya ba, saida ta kusa shanye robar yana kallonta cike da tausayi sannan ta janye kanta alamar sun isheta, aje robar yayi yana ci gaba da kallon fuskarta, a hankali ta fara dawowa hayyacinta ta fara jin wani kuzari kuzari yana d’an shigarta, yunwa ce yanzu ta rage mata kawai, amma bata jin tana da lokacin tsayawa cin abinci a garin nan, kallonshi tayi da idonta da suka k’ara yin fayau dasu sai kumburin da sukayi na kuka da ja, a hankali cikin muryar da bata fita sosai tace “Ina so na bar garin nan bari har abada, dan Allah mr. ka d’auke ni daga nan, ina so naje wajen dangin mahaifina.”

Hakan data fad’a ne ya tuna mishi da wayarta dake hannunshi har yanzu, da sauri ya shiga lalubarta a aljihu ya cirota, bud’a data yayi ya shiga manhajar WhatsApp, kamar an sanar dasu kam an bud’a wayar kawai kiran Sajida ya shigo wacce ke ta hada hadar shan ruwa a lokacin, kamar taji a jikinta kawai ta d’auki wayar ta sake aika kira.

Da sauri ta rarumi wayar ta d’auki kiran ta d’ora a kunne, daga b’angaren Sajida tace “Yer uwa ina kika shiga duk kin d’aga mana hankali? Na d’auka zan same ki anan amma baki zo ba.”

Wani murmushi Sarah taji ya taho mata dan yanda taji tana maganar da shagwab’a, da alama zata samu abokiyar gwagwarmaya, cikin danannan muryarta tace “Sorry sister, wani abu ya faru dani ne, amma na miki alk’awari yau zan shigo k’asar nan, ki tanadar min abincin da yafi kowane dad’i kinji.”

Da sauri tace “Da gaske? Amma me ya faru dake? Hankalinmu duk ya tashi wallahi.”

A hankali tace “Karki damu idan na zo zaku ji.”

Cikin sanyin jiki tace “Shikenan sai kin zo, amma tare da ogan zaku taho?”

A hanjali ta kalli Salahadeen da ka rantse muninta yake son hangowa tsabar yanda ya kafeta da ido, d’auke idonta tayi daga kanshi tace “A’a, zai wuce Maradi ne tare da matarshi, ni kuma zan zauna cikin yan uwana.”

Daga b’angarenta tace “Kinji sai kace wani lusari, haka kawai sai yayi nesa dake?”

Gimtse fuska tayi tace “Zamuyi magana anjima sis.”

Ko da ta fad’a ta kashe wayar, ta wutsiyar ido ya harareta ya mik’e daga gurfanan da yayi, kwance mata k’ullin k’afarta yayi da hannayenta, taimaka mata yayi ta mik’e tsaye, sai lokacin ma ta kalli Malik da shi dai ya kasa gane komai, rik’eta yayi ya rumgumata a jikinshi suka shiga takawa a hankali saboda bata da kwarin tafiya, haka har suka fita a daidai k’ofar fita kuma suka sake had’uwa da motar asibiti data Insp d’in sun dawo saboda kiran da Richard ya musu.

Sun so tafiya da ita asibiti dan duba lafiyarta amma tace sam ba zata je ba, dan haka anan cikin motar aka d’an dubata, babu wani abu kawai k’arfin jiki ne sakamakon rashin abinci da ruwa, wasu k’wayoyi suka bata tasha tare da bata Apple guda ta ci, tana zaune kan motar ta sake kallonshi, mamakin halinshi take mutumin nan, da fari daya ganta alamu sun nuna tsananin farin cikinshi da kuma damuwar daya shiga na rashinta, amma ji yanzu sai wani had’e rai yake yana cin magani, ko idonta baya son kallo yanzu kamar wata dodo.

Yar ajiyar zuciya ta sauke ta d’auke idonta daga kanshi tace “Daga nan nake so na wuce, ka taimaka ka kira min captain zamu tashi.”

Shima ba tare daya kalleta ba yace “Na ji.”

Matsawa yayi nesa da ita tare da Richard tana kallo yana ta mishi magana kamar dai yana bashi umarni, kafin daga bisani Richard d’in ya karb’i makullin mota a hannunshi yana jinjina kai alamar to. Sun d’auki minti talatin anan kafin motar asibiti data police d’in ta bar wurin bayan ta basu rahoton abinda ta gani kuma ta ji ta sani, tayi mamaki sanda suka shiga taxi taji ya ambaci a茅roport, ta d’auka saiya mata billi da isa kafin ya amince, ai kam sai gasu filin jirgi cikin mintuna da basu kai ashirin ba, amma kuma da zuwansu saita samu Richard acan da kuma Farhanatu da jakunkunan kaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button